Daga Muhammad Maitela, Maiduguri
Rahotanni daga kauyen Kawuri a jihar Borno sun bayyana cewa motar jami’an tsaron yan sa-kai ta taka bam, wanda ake zargin mayaqan Boko Haram ne su ka binne shi a kasa, a safiyar yau Laraba, al’amarin da ya jawo asarar rayukan yan sintiri bakwai.
Wadannan jami’an sa-kai sun gamu da ajalin su ne kusa da wannan qauye na Kawuri a lokacin da dureban motar ya bi ta kan biznannanen bam din a lokacin da su ke aikin sintiri a yankin.
Bugu da kari kuma, yanzu haka an kawo gawawakin yan-sintirin babbar asibitin jami’ar Maiduguri.
A hannu guda kuma, wani daga cikin manyan jami’an gwamnatin jihar Borno ya tabbatar da faruwar al’amarin- duk da ya buqaci a sakaya sunan shi.