Da Dimi-diminsa: Boko Haram Sun Sake Mamaye Damask A Borno

Kudin Fansa

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Wasu maharan da ake kyautata Boko Haram ne, da yammacin ranar Talata, sun sake mamaye garin Damask, shalkwatar karamar hukumar Mobbar a jihar Borno, yayin da bayanai sun kara da cewa yan ta’addan sun farmaki garin ba tare da fuskantar turjiya ba.

Har wala yau, a wannan karon, maharan sun kona ofishin yan-sanda, makarantu, shaguna da gidajen jama’a, wanda daga bisani kuma suka sanya tuta a matsayin alamar iko da garin.

Ko a ranar Asabar din da ta gabata sai da mayakan Boko Haram sun kai wani mummunan farmaki a Damasak inda suka kashe sojojin Nijeriya uku da karin wasu mutum 6 a sa’ilin da wani makamin roka ya fada tsakiyar mutane a lokacin bikin suna a garin.

A harin Asabar din, yan ta’addan sun kona ofisoshi tare da kayayyakin kungiyoyin ayyukan jinkai a garin, kana da wawushe magunguna a babbar asibitin Damasak.

Bugu da kari kuma, garin Damasak ya na kan iyaka da jamhuriyar Nijar a arewacin jihar; mai tazarar kilomita 180 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Da yake tabbatar da faruwar sake kai wannan sabon farmakin a Damasak, shugaban karamar hukumar Mobbar, Hon. Mustapha Bunu Kolo ya shaida wa wakilinmu cewa sabon harin ya yi muni sosai, saboda yadda maharan suka karasa cinna wuta ga sauran ofisoshin da suka rage na kungiyoyin jinkai, ofishin yan-sanda, kasuwa, shaguna tare da gidajen jama’a a garin.

“Eh haka ne, Boko Haram ne suka sake kawo mana hari a garin Damasak a yanzu haka zancen da muke yi da kai.”

“Duk da bana cikin garin Damasak yanzu haka, saboda tafiya da nayi ta aiki, amma bisa bayanan da na samu kan lamarin, maharan sun shiga garin tun kimanin karfe 5 na yamma, wanda suka ci gaba da cin karensu babu babbaka har kusan karfe 10:40 na dare.”

”Wanda hakan ya basu damar kona sauran da ya rage na ofisoshin kungiyoyin jinkai, kasuwa da shaguna, tare da wasu gudajen jama’a wadanda ba a san adadin su ba, kuma sun yi amfani da abubuwa masu fashewa a wannan aika-aika ba tare da samun turjiyar jami’an tsaro ba.”

“Har wala yau kuma, na samu labarin an kashe mutane da dama a wannan harin, amma bani da adadin yawan wadanda suka mutu saboda yadda har yanzu yan ta’addan suna ci gaba da kaddamar da wannan farmaki ga jama’ar da basu ji ba basu gani ba a garin.” In ji Hon. Kolo.

Amma duk kokarin samun tabbacin kai harin tare da mamaye Damasak daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan-sandan jihar Borno, DSP Edet Okon ya ci tura a lokacin hada wannan rahoton.

Exit mobile version