Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da murabus din shugabannin rundunonin tsaro, da kuma ritayar da suka yi daga aiki.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Abayomi Olonisakin; Shugaban hafsan soji, Lt-Gen. Tukur Buratai; Shugaban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar.
Shugaba Buhari ya gode wa Shugabannin masu barin gado saboda abin da ya kira “gagarumar nasarar da suka samu a kokarinmu na samar da dawwamammen zaman lafiya a kasarmu,” yana mai yi musu fatan alheri a ayyukan da za su yi nan gaba.
Sabbin shugabannin hafsoshin sun hada da: Manjo-Janar Leo Irabor, Babban hafsan hafsoshin tsaro; Manjo-Janar I. Attahiru, Shugaban hafsin soji; Rear Admiral A.Z Gambo, Shugaban hafsan sojojin ruwa; da Air-Vice Marshal I.O Amao, Babban hafsan sojojin sama.