Da Dimi-Diminsa: Dan Atiku Abubakar Na Daga Cikin Jerin Sunayen Kwamishinoni A Adamawa

Atiku

Yanzun nan majalisar dokokin jihar Adamawa ta amshi sunayen jerin sunayen kwamishinonin da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ya aike musu, domin tabbatar da su.

Wasu daga cikin jerin sunayen sun hada da dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Adamu Atiku daga karamar hukumar Jada, Abdullahi Adamu Prambe daga Song.

Sai kuma Wulbina Jackson, Guyuk da Shuaibu Audu Mayo Belwa, Aloysius Babadoke Jada, Justina Nkom Lamurde, Mustapha Musa Jika Yola ta kudu.

Bayanai dai na nuni da sunayen Kwamishinoni 23, gwamnan ya aikewa majalisar.

Cikakken rahoto na tafe.

Exit mobile version