Da Dimi-diminsa: Fadar Shugaban Kasa Ta Dakatar Da Magu

Fadar Shugaban Kasa ta sanar da dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar EFCC mai yaki da almundahana da rashawa ta Nijeriya.

A jiya Litinin ne Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba.

Kwamitin – karkashin jagorancin tsohon mai shari’a Ayo Salami – ya gayyaci Magu ne domin jin ta bakinsa kan abubuwan da suka shafi ayyukan sa a hukumar ta EFCC.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Magu ya kwana a tsare a hannun jami’an tsaro saboda ba a kammala binciken da aka soma ba a jiya Litinin.

Exit mobile version