Connect with us

Da dimi-diminsa

Da Dimi-diminsa: Gwamna Akeredolu Ya Kamu Da Korona

Published

on

Gwamnan Jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, Ya kamu da Cutar Korona.

Gwamnan Ya fitar da sanarwar kamuwarshi da cutar ne ta hanyar sadarwar zamaninshi ta Facebook ayau Talata

Gwamnan yace yanzu haka yana killace, akan bin dokar hukuma mai kiyaye yaduwar cututtuka wato NCDC.

Gwamnan yace ya samu tabbacin kamuwa da cutar ne sakamakon gwaji da yafuto yau, amma inanan cikin koshin lafiya.

Ina nan akillace, kuma hukumar NCDC zata bada kwararrun ma’aikatanta don kula da lafiya ta. Sannan ina rokon kowa da yazauna cikin koshin lafiya.

Akeredu ya shiga cikin jerin manya wadanda suka kamu da cutar ta Korona. Wadanda sun hada da marigayi Abba Kyari; Nasir El-Rufa’I, Gwamnan Jihar Kaduna; Bala Muhammad, Gwamnan Jihar Bauchi; Seyi Makinde, Gwamnan Jihar Oyo.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: