Connect with us

LABARAI

Da Dimi-diminsa: Majalisar Dokokin Ondo Ta Fara Zaman Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar

Published

on

Majalisar dokokin jihar Ondo, ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mr Agboola Ajayi.

 

A halin yanzu ‘yan majalisar na muhawara a zauren majalisar a kan zargin saba dokokin aiki da ake yi wa mataimakin gwamnan. Jami’an ‘yan sanda da na hukumar tsaro ta NSCDC sun mamaye harabar majalisar domin tabbatar da doka da oda.

 

An hana manema labarai shiga harabar majalisar. An bukaci su kira Gbenga Omole, shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar ya basu izini kafin a bari su shiga kamar yadda aka ruwaito.
Advertisement

labarai