Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Da Dimi-diminsa: Mambobin APC Sun Tsige Uba Nana A Matsayin Shugabansu Na Jihar Bauchi

by
2 years ago
in Da dimi-diminsa
2 min read
Da Dimi-diminsa: Mambobin APC Sun Tsige Uba Nana A Matsayin Shugabansu Na Jihar Bauchi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Wata sabuwar rigima ta kunno kai a cikin jam’iyyar reshe jihar Bauchi, inda wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka shelanta tsige shugaban jam’iyyar a matakin jihar Uba Ahmad Nana tare da maye gurbinsa da shugaban riko har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin taron manema labaru da wasu ‘ya’yan APC din suka kira a ofishin jam’iyyar APC da ke Turum yau Laraba, suna masu shaida cewar tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar shine ya jagoranci aiwatar da haramtacen zaben shugabanin jam’iyyar a matakin jihar da ya kai ga kawo baraka da rashin amincewar wasu bangaren, don haka ne a yanzu suka sanar da dakatar da Uba Nana a matsayin shugaban jam’iyyar.

Da yake magana da ‘yan jarida a madadin mambobin jam’iyyar APC gaba daya, wani jigo a jam’iyyar a matakin jihar da ma kasa, Alhaji Ibrahim Ago, ya shaida cewar sun dauki matakin ne domin dawo da bartaba da kimar jam’iyyar, yana mai cewa zaben da ya kai ga ayyana Uba Nana a matsayin shugaban jam’iyyar haramtacce ne.

Labarai Masu Nasaba

Zanga-Zanga Ta ɓarke A Asibitin Kwararru Na Gwamnatin Adamawa

Jirgin Kasan Injiniyoyi Ya Halaka Dabbobi 700 A Hanyar Kaduna-Abuja

Ya ce, zaben da aka yi a 2018 har Uba Nana ya zarce a matsayin shugaban APC haramtacce ne, “Ba wanda zai sake kiran kansa shugaban jam’iyya har san an zo an sake yin zabe. Muna son jama’a su sani shugaban da yake kiran kansa shugaban APC (Uba Ahmad Nana) ba shugaba bane,”

Ya ce sun sanya shugaban riko da zai jagoranci jam’iyyar har zuwa a sake yin zabe, “Shugaban APC na riko yanzu a jihar Bauchi shine Malam Aminu Na-Borno, shugaban APC na karamar hukumar Shira shine sabon shugaban APC na riko,” A fadin Ago.

Shi ma Alhaji Rabi’u Shehu Dan-Baba, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a matakin karamar hukumar Bauchi, ya shaida cewar jam’iyyar APC ta kasa ci gaba a kullum matsaloli suke samu a sakamakon gazawar Uba Nana, ya kuma ce rashin adalci da rashin iya shugabanci sun mamaye jam’iyyar don haka sun dakatar da shi har zuwa lokacin da za a sake zabe.

Daga nan sun zargi Uba Nana da hada kai da gwamnati mai ci a lokacin zaben 2019 da har hakan ya kai ga shan kayen APC a jihar, ya kuma sake zarginshi da cewar har yanzu yana da alaka da gwamantin PDP mai ci a jihar.

Da yake mai martani kan wadannan batutuwan, shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana, ya shaida cewar jam’iyyar APC jam’iyyace da take tafiya bisa tsari da dokokinta, don haka ya shaida cewar duk abin da wadannan fusatattun mambobin jam’iyyar suke yi bai bisa ka’ida.

Da yake ganawa da manema labaru Uba Nan ya ce, an zabeshi a matsayin shugaba kuma yana kan kujerarsa ta shugaba, ya shaida cewar dukkanin matakan da suka dace jam’iyya ta tafiya a kai, APC ma tana tafiya a kai.

Ya ce, mambobin da suke wannan ikirarin an sake zabe basu samu nasarar kaiwa ga zarcewa a a matsayin shugabannin jam’iyyar ba, “Wannan dalilin ya sanya suka fusata,” sai dai ya shaida cewar abun da suke yi bai ma kai jam’iyya da kanta ta tsaya biye musu ba.

“Kungiyoyi irinsu za su basu amsa daidai da abubuwan da suka yi,” A cewar Uba Ahmad Nana.

Cikakken wannan labarin zai biyo baya:

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

NPA Za Ta Tabbatar Da Kafa Tashar Jiragen Ruwa Na Cikin Teku

Next Post

Mike Pompeo Na Tafiyar Da Harkokin Jakadanci A Matsayin Makaryaci

Labarai Masu Nasaba

Zanga-Zanga Ta ɓarke A Asibitin Kwararru Na Gwamnatin Adamawa

Zanga-Zanga Ta ɓarke A Asibitin Kwararru Na Gwamnatin Adamawa

by Muh'd Shafi'u Sale
1 week ago
0

...

Jirgin Kasan Injiniyoyi Ya Halaka Dabbobi 700 A Hanyar Kaduna-Abuja

Jirgin Kasan Injiniyoyi Ya Halaka Dabbobi 700 A Hanyar Kaduna-Abuja

by Abdulrazaq Yahuza Jere
1 week ago
0

...

Da ɗimi-diminsa: Gobara Ta Sake Tashi A Babbar Kasuwar Sokoto

Da ɗimi-diminsa: Gobara Ta Sake Tashi A Babbar Kasuwar Sokoto

by Abdulrazaq Yahuza Jere
2 weeks ago
0

...

Wani Abu Da Ake Zargin Bom Ne Ya Jikkata Mutane A Gashuwa

Wani Abu Da Ake Zargin Bom Ne Ya Jikkata Mutane A Gashuwa

by Muhammad Maitela, Damaturu
3 weeks ago
0

...

Next Post
Mike Pompeo Na Tafiyar Da Harkokin Jakadanci A Matsayin Makaryaci

Mike Pompeo Na Tafiyar Da Harkokin Jakadanci A Matsayin Makaryaci

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: