Da Dimi-diminsa: Shugaba Buhari Ya Umarci A Bude Twitter

Shugaban kasa Buhari ya umarci a dage haramcin da aka sanya wa shafin Twitter, daga karfe 12 na daren yau, wato daga gobe shafin zai fara aiki bayan shafe watanni da aka rufe shi.

Daraktan Hukumar NITDA, Mallam Kashifu Inuwa ne ya sanar da haka da yammacin yau Laraba.

A watannin baya ne Gwamnatin Tarayya ta rufe shafin sakamakon goge wani sako da shugaban kasa Buhari ya sanya a shafin, inda hakan ya haifar da cece-kucen da ya jawo gwamnatin ta rufe shafin.

Exit mobile version