Tsohon gwamnan jihar Oyo, Alhaji Abiola Ajimobi ya rasu, Ajimobin shine sirrikin Gwamna Jihar Kano, kuma tsohon Sanata.
Ajimobin yana kwance a wani asibiti a Jihar Legas, inda ake bashi kulawa sakamakon kamuwa da ya yi da cutar Korona.
A makon da ya gabata an yi rade-radin rasuwar tsohon gwamnan, inda hadiman shi suka karyata.