Connect with us

Da dimi-diminsa

Da Dimi-diminsa: Umar Sa’idu Ya Lashe Zaben Shugaban ‘Yan Jarida Na Bauchi

Published

on

Yanzu-Yanzu: Umar Sa’idu Ya Lashe Zaben Shugaban ‘Yan Jarida Na Bauchi

Daga Khalid Idris Doya

Malam Umar Sa’idu shine ya samu nasarar lashe zaben shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi (NUJ) da aka gudanar a yau Asabar din nan.

A daidai karfe 3:300 na ranar yau ne Shugaban kwamitin shiryawa da gudanar da zaben Malam Umar Shira shine ya sanar tare da ayyana Umar Sa’idu a matsayin zabon shugaban bayan samun kuri’u mafi rinjaye a kan abokin karawarsa wato Bashir Idris da suka nema shugabancin kungiyar tare.

Umar Sa’idu wanda dan jarida ne da ke aiki a ma’aikatar yada labaru ta jihar Bauchi ya samu zama shugaban ne da kuri’u 150 a inda ya kada Bashir Idris mai kuri’u 76.

Har-ila-yau kwamitin zaben sun kuma sanar da Abbas Maikano (NTA) a matsayin wanda ya lashe kujerar mataimakin shugaban kungiyar da kuri’u 114 inda ya kada abokin karawarsa Hashimu Bulkachuwa daga ma’aikatar sadarwa mai samun kuri’u 112.

Sai kuma a kujerar sakatare Alhaji Garba Gadau ne ya samu nasarar zama sabon sakataren kungiyar ne da kuri’u 120 a inda ya kayar da abokin hamayyarsa Kabiru Garba (BRC) mai samun kuri’u 107.

A yayin da Adama Ibrahim daga ma’aikatar sadarwa ta jihar Bauchi ta samu nasarar zama sabon mataimakiyar sakataren kungiyar NUJ a jihar da kuri’u 105 inda ta kayar da abokin takararta Sani Mu’azu ya samu kuri’u 84 sai kuma Bature Malumbashi (NTA) ya samu kuri’u 45.

Sai kuma kujerar ma’ajin kudi Abubakar Musa Waziri (Globe FM) ne ya samu nasarar kayar da abokin nemarsa da kuri’u 162, sai kuma Zurkarnaini Inuwa (Globe FM) ya samu kuri’u 62.

Sai kuma wadanda suka zarce a kan kujerarunsu Najib Sani (Correspondent chapel) sakataren kudi da kuma Danjuma Sarki Sale (Globe fm) mai bin dindigi (Auditor).

Khalid Idris wakilinmu ya shaido mana cewar tunin aka rantsar da sabbin shugabannin nan take bayan samun nasarar wadanda suka lashe kujerar.

Cikakken labarin na tafe.




Advertisement

labarai

%d bloggers like this: