Umar Faruk Birnin-kebbi">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Da dimi-diminsa

Da Dimi-diminsa: ‘Yan Sanda Sun Cafke Dillalan Makamai A Kebbi

by Umar Faruk Birnin-kebbi
February 9, 2021
in Da dimi-diminsa
1 min read
Da Dimi-diminsa: ‘Yan Sanda Sun Cafke Dillalan Makamai A Kebbi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kebbi ta cafke wasu mutane uku da ake zargin dillalan makamai ne.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DSP Nafi’u Abubakar, shi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na gaggaawa da aka gudanar yau a ofishin rundunar da ke Birnin Kebbi.

DSP Abubakar ya bayyana cewa, rundunar ta kuma kama wani shahararren mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Mulki ta Arewa.

“Mun kama bindigogin ganga biyu da kuma bindiga guda daya a cikin jakarsa.

“Inda ya bayyana mana cewa wasu mutane biyu ne suka bashi kwangilar sayo musu bindigogin da aka cafke shi da su, kan hakan ne jami’an rundunar yan sandan suka cafko wadannan mutanen biyu da ya bayyana.

“Lokacin da aka tambaye shi, bai iya ba da gamsassun bayanai game da bindigogin ba, don haka aka kama shi,” in ji jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan.

Daga karshe ya ce: “Da zarar rundunar yan sanda ta kammala bincike za a gurfanar da su a kotu.”

Wakilinmu ya zanta da daya daga cikin wadanda ake zargi, wato Ibrahim Bulus. Inda ya bayyana cewa: “Na sayo wadannan bindigogin ne a Kasuwar Dirin Daji, a karamar hukumar Sakaba da ke jihar kebbi, a cikin kasuwa ake kasa bindigogin na sayar wa, a nan ne na sayo wadannan.”

SendShareTweetShare
Previous Post

Kiran Sarki Sanusi Ga Malaman Kano: Ku Mara Wa Ganduje Baya Kan Sheikh Abduljabbar

Next Post

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sauya BVN Da NIN – Pantami

RelatedPosts

Masarautar Gwandu Ta Bada Sanarwar Dakatar Da Wazirin Gwandu

Masarautar Gwandu Ta Bada Sanarwar Dakatar Da Wazirin Gwandu

by Umar Faruk Birnin-kebbi
2 weeks ago
0

Daga: Umar Faruk Birnin-Kebbi Masarautar Gwandu a karkashin jagorancin Mai...

Gwamna Bagudu Da Minista Malami Sun Sabunta Rajistarsu Ta Jam’iyyar APC

Gwamna Bagudu Da Minista Malami Sun Sabunta Rajistarsu Ta Jam’iyyar APC

by Umar Faruk Birnin-kebbi
4 weeks ago
0

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi A yau ne Gwamnan Jihar Kebbi,...

Da Dumidumin-sa : Kungiyar Lauyoyi Zata Kaurace Wa Zaman Kotutuka A Kebbi

Da Dumidumin-sa : Kungiyar Lauyoyi Zata Kaurace Wa Zaman Kotutuka A Kebbi

by Umar Faruk Birnin-kebbi
1 month ago
0

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Kebbi, ta bayyana cewa"...

Next Post
Gwamnatin Tarayya Za Ta Sauya BVN Da NIN – Pantami

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sauya BVN Da NIN - Pantami

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version