Kwamitin Koli na jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) reshen jihar Bauchi ya amince da gaggauta dakatar da dan majalisar Dokokin Tarayya mai wakiltar mazabar Bauchi, Alhaji Yakubu Shehu Abdullahi da aka fi sani da Wakilin Birnin Bauchi nan take ba tare da bata lokaci ba.
Jam’iyyar da dakatar da shi na tsawon watanni 12 bisa samunsa da laifin zagon kasa (Anti-Party) wa harkokin jam’iyyar, da laifin kin biyayya wa jagorancin jam’iyyar, tare da kasa gudanar da kyakkyawar wakilcin da jama’a suke son ya je majalisa musu daidai da manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar.
Bayan wannan, jam’iyyar ta kuma rushe kwamitin riko na jam’iyyar a karamar hukumar Bauchi nan take.
A sanarwar manema labarai da jam’iyyar ta fitar a yau Alhamis, dauke da sanya hannun sakataren watsa labaranta Usman Muhammed, PRP ta lura kan cewa tun lokacin da dan majalisar ya taka kafarsa zuwa cikin majalisar har zuwa yanzu babu wani kuduri ko guda daya da ta tashi ya gabatar domin al’umman da ke wakilta, suna kiran jama’an mazabarsa da su dauki matakin da ya dace a kansa.
Har-ila-yau, majalisar koli na jam’iyyar ta PRP (SEC) reshen jihar Bauchi a zaman da suka gudanar a ranar 23 ga watan Disanban 2020, sun cimma matsayar amincewa da rushe kwamitin riko na karamar hukumar Bauchi.
Sanarwar ta shaida cewar an kuma kafa kwamitin riko da zai jagoranci ragamar jam’iyyar a karamar hukumar Bauchi har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe.
Kakakin jam’iyyar ya bada sunayen sabbin shugabannin riko a karamar hukumar Bauchi na jam’iyyar da aka kafa da cewa Malam Abdulmalik M. Aliyu shine shugaba, Salmanu Muhammad Luti kuma sakatare tare da sauran.
Daga nan sanarwar ya nemi mambobin jam’iyyar da su cigaba da gudanar da harkokinsu bisa mutuntawa da sanin ya kamata tare da yin aiki tare domin cimma nasara.
Wakilinmu ya kira Wakilin Birnin Bauchi, dan majalisar da jam’iyyar ta dakatar ta wayar tangaraho domin jin ta bakinsa kan wannan matakin amma bai kai ga daukar kiran da muka masa ba kawo buga wannan labarin.