Hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da dage zabukkan da za a gudanar a yau Asabar, shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya sanar da dage zaben, indaya bayyana cewa sai ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu za a gudanar da zabukkan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa.
Zaben gwamnoni da na majalisun tarayya kuma sai ranar Asabar 9 ga watan Maris a maimakon ranar 3 ga watan Maris da ka tsara za a gudanar a farko.