Connect with us

Da dimi-diminsa

Da Dumi-duminsa: Gali Na’abba Bai Rasu Ba

Published

on

Sabanin labaran boge da aka rika yadawa a kafafen soshiyal Midiya tun daren jiya cewa, tsohon Kakakin majalisar Tarayya, Ghali Na’abba ya rasu, ta tabbata yana nan da ransa kamar yadda LEADERSHIP A YAU ta binciko.

Jita-jitar mutuwarsa ta fara yaduwa ne tun daren jiya a kafafen sada zumunta ciki harda wadansu kafafen yada labarai (banda LEADERSHIP A YAU).

Honorabul Na’abba ya rike Kakakin majalisar tarayya a lokacin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Advertisement

labarai