Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Kebbi, ta bayyana cewa” zata kaurace wa zaman kotutuka na duk fadin jihar ta Kebbi har tsawon makonni uku kan matsalar tsaro da yawan kashe-kashe jama’a da yin barazana ga rayuwar al’ummar musamman ga Alkalai da Lauyoyi da ‘Yan Sa kai ke gudanar a yankin Masarautar Zuru da ke a cikin jihar ta kebbi.
” Bayanin haka ya biyo bayan wani taron tattauna wa na gaggawa da kungiyar ta NBA ta gudanar a yau a Birnin-Kebbi, Inda takardar na dauke da sa hannun Shugaban kungiyar na Jihar Kebbi, Barista Kabiru Aliyu da Sakatare, Barista Aminu Hassan suka sanyawa hannu, kuma aka fitar da ita ga manema labarai bayan kammala taron tattauna na gaggawa da suka gudanar a ofishinsu da ke a Birnin Kebbi Ayau.
Takardar ta ci gaba da bayyana cewa” kungiyar ta NBA ta kosa da kuma damuwa ga irin yadda ‘Yan Sa kai’ na Masarautar Zuru ke hana jama’a bin umurnin kotutuka da kuma hana yin hukunci a kotutukan yankin ko shigar da kara kai har da masu bada sheda a gaban kotu .
“Bugu da kari ma’aikatar kotu su ma rayawarsu na cikin hadarin gaske, bisa ga wannnan matsalar rashin tsaro ga yanki ne ya sanya kungiyar NBA ta jihar Kebbi daukar wa mataki har sai gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Kebbi da Masarautar Zuru da sauran masu ruwa da tsaki ga harakokin tsaro sun dauki mataki kare rayukan al’umma, inji takardar NBA Kebbi” . Cikaken rahoton za a karan tashi a jaridar mu ta jumaa.