Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home NAZARI

Da Gaske Akwai Zinare A Kan Masu Sanko?

by Tayo Adelaja
September 13, 2017
in NAZARI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Daga Wakilinmu

Allah daya gari bamban, a yayin da al’ummarmu ta Nijeriya musamman hausawa ke alakanta sanko da arziki ko tarin ilimi. Su kuwa a kasar Mozambikue abin ba haka bane. Matukar ma kana da sanko a kanka, sai dai ka shiga taitaiyinka tare da taka-tsantsan din wuraren da zaka rika zuwa.

samndaads

A wata sabuwa, ‘Yan sanda a kasar Mozambikue sun gargadi masu sanko cewa matsafa ‘yan yankan kai na iya far musu, bayan kisan mutum biyar a baya-bayan nan don cire sassan jikinsu.

An kama mutum biyu da ake zargi a tsakiyar lardin Milange, inda kashe-kashen suka faru.

Haka kuma a wani rahoton makamancin wannan, an kakkashe zabiya ma a yankin don yin tsafi da sassan jikinsu. A cikin makon jiya kadai, an kashe mutum uku.

Sai dai hukumar ‘yan sanda ta yi watsi da batun wai akwai zinare a cikin kan masu sanko. Hukumar ta ce wata yaudara ce ta bokaye don samun mutanen da za su yanko musu kan irin wadannan mutane.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mutanen da ake zargi matasa ne guda biyu ‘yan kimanin shekara 20.  Wani mai magana da yawun jami’an tsaron yankin, Miguel Caetano, ya fada wa AFP cewa an yanke kan wani mutum kuma aka datse masa al’aura.

Ya ce wadanda ake zargin sun ce ana amfani da sassan jikin ne wajen yin asiri don samun karuwar arziki ga masu kudin da ke zuwa neman magani daga Tanzania da Malawi.

A shekarun baya-bayan nan an samu kashe-kashen zabiya a yankin Afirka Ta Gabas, inda bokaye suke amfani da sassan jikinsu don yin asiri.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamna Masari Yayi Kira Ga Masu Cutar Kanjamau

Next Post

Za A Binciki Kayayyakin Da Hukumar UNICEF Ta Kawo A Kebbi

RelatedPosts

Yaki Korona

Yaki Da Korona: Hannu Daya Baya Daukar Jinka

by Muhammad
4 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Tun a cikin watan Janairun 2020, hukumar...

Hannun Mata

Waya A Hannun Mata: Alheri Ko Sharri? 

by Muhammad
5 days ago
0

DAGA SAMEERAH BELLO SHINKO, mameerah@gmail.com   ,A wannan zamani da...

Kabarin Annabi

Manyan Yunkuri Biyar Da Aka Taba Yi Na Dauke Kabarin Annabi (SAW) Daga Madina

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Rabi’u Ali Indabawa, Annabi Muhammad (SAW), shi ne Annabin...

Next Post

Za A Binciki Kayayyakin Da Hukumar UNICEF Ta Kawo A Kebbi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version