Abdullahi Muhammad Sheka" />

Da Gina Masallaci Gara Gina Masana’antar Fim – Momoh

Shahararren dan wasan finafinan Hausa na Kannywood Aminu Sherif Momo ya bayyana cewar raya harkar Fim a yanzu ya fi raya masallatai ko makarantun Islamiyya, inda ake karatun Alkur’ani muhimmanci nesa ba kusa ba.

Fitatcen dan wasan finafinan ya kara da cewar muhimmancin harkar Fim a cikin al’umma ta fi muhimmancin akan Massalatai ko Makarantun Alkur’ani, ba ma zai yi yiwu a hada su ba inda yayi kira ga masu hannu da shuni da su zuba kudi cikin harkar masana’antar Kannywood.
A ra’ayin Aminu Momo da a zuba kudi wajen gina Masallatai ko Islamiyyu a kasar Hausa, gwara a zuba kudin wajen harkar shirya fina-finan Hausa, duba da irin muhimmiyar rawa da ‘yan wasan kwaikwayon ke bayarwa wajen gina tarbiyyar al’umma.
Fitaccen Jarumi a masana’anatar Kannywood ya bayyana wannan kalaman a cikin shirn ‘Barka da hantsi’ na rediyo freedom dake Kano a safiyar yau Laraba.
Ya ce: “A halin da ake ciki yanzu da a gina Masallatai da Islamiyyu gwara a zuba kudaden a harkar shirya fina-finan Hausa.” Saboda muhimmancin harkar akan gine ginen Masallatai ko Makarantun Islamiyya.

Exit mobile version