Mairo Muhammad Mudi" />

Da Kakata Na Da Rai Yau: Me Za Su Kira Ta?

A lokacin da na ke makaranta in na dawo hutu na kan zarce dakin kakata ne don jin labarin abubbuwan da suka gabata bayan ba na nan.

A cikin labarun wannan hutu ta fada mani an samu sabon dan haya a sassan su yayanku Hauwa sannan yana sayar da kayan wuta a shagon babanku. Igbo ne sunansa Bituwis, na yi murmushi don na san kakarmu da iya juya sunan mutane tun wanda ke mata wahala ta fade shi ta yadda ta ke ganin za ta iya so sai na saka a raina sunan wannan bawan Allah Bitrus ne. Kanwata na shigowa na ce mata ashe an samu sabon dan haya mai suna Bitrus? Ta kalle ni ta ce, “Bitrus ko Cletus?” Na ce mata Bitrus dai! Ta ce wa ya fada maki, na ce mata kakanmu.
Muka dunguma zuwa wajenta, muka tambaye ta, ta fah ce sunansa Bituwis ne sai kanwata ta ce Cletus dai, ta ce ita fa ta sunnansa kenan. Da muka ga babu yadda za mu yi canza mata ra’ayinta, muka gyale ta. Haka kuwa ta ke kiransa, shi kuma a haka ya ke amsawa.

Watarana sai Cletus ba ya da lafiya aka kwantar da shi a asibiti sai ta sa jikokin a gaba sai sun kai ta ta gaishe shi,a lokacin ta tasan ma shekaru 100 amma kuma alhamdulillah tana da karfin ta don kowace yamma sai ta debi ruwa ta kai masallaci. Abu guda ne kan dan ba ta wahala, shine kafarta. Da suka kai asibitin, akwai matakala don gidan sama ne. Ta taka na farko da ta kai na biyu ta kasa, sai ta rike karfen ta tsaya shiru tana kallon sama ta ce, “Ya Allah Ka gani, zumunci ne ya kawo ni, don Allah ku …gai da kakarmu,sai ta yi ta sa mata albarka tare da mata fatan samun sa’a. Ana nan ranar za ta wuce ta kofar gidanmu, ba ta ga kakarmu ba, (dama nan ne wajen zamanta da jikokinta ana ta hira) sai ta tambaya ina kaka, aka ce mata rai ai ya yi halinsa, mata ta zube ta yar da kwanon kanta tana ta kuka tana yarbanci, an ce tana ta tambaya a ina za ta samu mai saka mata albarka haka? Kakanmu dai ina ga har ta koma ga Allah ba ta san inda matar nan ta fito ba balle sanin addininta kuma bai hana ta mata fatan alheri ba.
Allah Ya sa na tashi cikin babban gida ne, muna da yawa sosai a gidanmu da sasa-sasa daban-daban. Na tashi ba ni da wayau sosai na ga Tib a gidanmu mai suna magarahama, ban san ki na fadi sunan dai-dai ba, amma shine Sarkin Tib na wannan lokacin, a duk lokacin da kismeti ya zo, mu kan fito mu sha kallo don a kan zo har gidanmu yi masa wasansu. Kullum mu kan yi daukin wannan lokaci saboda irin rawarsu ma, a haka har Allah Ya ba shi iko ya yi gininsa ya koma amma duk abinda ya faru a gidansa wasu manya kan tafi shima matansa kan zo.

Exit mobile version