Sabo Ahmad" />

Da Mun San Haka Mustapha Zai Karbu Da Takarar Gwamna Ya Tsaya —Injiniya Umar

Injina Umar na daga cikin makusanta dantakarar sanata a inuwara jam’iyyar PDP,  daga mazabar Jigawa ta tsakiya kuma dan tsohon gwamnan jihara Jigawa Alhaji sule Lamido, Mustapha Sule Lamido, ya bayyana cewa, karbuwar da suke ganin dan takararsu na yi a wajen al’ummar jihar jigawa ya nuna cewa da sun san haka dantakar na su zai samu karbuwa a dukkanfadin  jihar dà takarar gwamna suka tsayar da shi, Wanda kuma bisa dukkan alamu da an yi hakan da su ne za su samu nasara.

Sai dai duk da haka Injiyan ya ce, ai tafiya sannu- sannu kwana nesa, wani lokaci bisa ikon Mustapha sai ya zama gwamnan jihar Jigawa, bayan kammala wa’adinsa na wannan zaben da muke da tunanin cewa da yardar Allah shi ne da nasara.

Injiniya ya ci gaba da cewa, dalilai da yawa suka sa Mustapha ya samu karbuwa a wanna mazaba ta jJigawa ta tsakiya da ma jihar Jigawan bakin daya. Domin kuwa kowa ya san mahaifinsa cewa, gogage kuma tsayayen dan siysa ne wanda yake da akida irin ta ‘yan mazan jiya saboda haka yana cin albarkacin mahaifin nasa.

Sannan baya ga wannan kamar yadda Injiniya ya fada cewa, Mustapha mutum ne mai tausayawa jama’a sannan kuma ga taimakon marasa karfi, wannan ta sa al’umma ke ganin cewa zai zama babbar mafita a wurinsu yadda in sun zabe shi zai kara samun damar ci gaba da tallafa musu.

Injin ya kara da cewa shi kansa da suke tare da Mustapha yana manakin yadda al’umma suk nuna cikakken goyon bayansu na tsayawa takarasa, ya ce kawanakin baya da suka je Ringim duk da cewa ba ta  cikin mazabar dan takarar amma haka al’umma suka dinga fitowa suna  cewa sai mai taimako.

Da yake karin haske kan shirin da suke da shi muasamman ga mata da matasa idan Allah ya ba su nasara, Injiniya ya ce abu ne sananne a cikin wannan al’ummar cewa, Mustapha na damuwa da rashin samun kyakkyawan ilimi ga ‘ya’yan talaka,, don haka daga cikin babban burinsa shi ne samar da hanyar da zai tallafa wa ilimin domin shi ilimi shi ne gishirin rayuwar jama’a.

Sannan ga matasa kuwa kamar yadda Injiniya ya ce, su ma yana da kishin ya ga kowa ya kama sana’a yadda zai samu hanyar dogaro da kansa har ma wasu su ci gaba da cin albarkacinsa. Saboda haka kamar yadda ya ce Mustapha tun tuni yake jawo matasa a jika ya tallafa musu da hanyiyin da za su rage radadin talauci.

wani abu da injiniyan kuma ya lura da shi wanda ya karawa tafiyar tasu armashi shi ne yadda jama’a ke dana-sanin zaben da suka yi, sun ce lallai canjin da ake kira musu sun same shi amma daga koshi zuwa yunwa da kuma daga yalwa zuwa talauci., saboda haka ne ma jama’a da dama ke cewa dambakara, ba za su sake yarda a yi musu sakiyar da babu ruwa ba.

Saboda haka ya cewa zaben tumun dare da suka yi a baya ya zame musu darasi babba wanda kuma ba za su yarda su sake maiamaita irin kuskuren da suka yi  a baya ba.

Injiniya ya ci gaba da nuna cewa, gwanin nasa shi ne zai shareawa al’ummar yankin Jigawa ta tsakiya hawayensu wanda ya dade yana zuba sakamakon bakin talaucin da aka jefa su ciki.

Baya wanna Injiniya ya ce Mustapha  kan je gidan yari domi kai wa wadanda ke tsare ziyara ya kuma kai musu abinci, sannan wadanda suke da kanana matsaloli musamman wadanda suke tsare sakamakon rikicin bashi yakan biya ya kuma sama musu ‘yancin kansu, domin su ci gaba da walwala kamar sauran jama’a.

Wani abu da Injiniyan ya ce ya dada jawo wa dantakarar nasu farin jini shi ne yadda  yake da sakin fuska da walwala ga jama’arsa, ga dukkan wanda ya san Mustapha kamar yadda ya ce mutum ne mai sakin fuska cikn al’ummarsa da taimaka musu duk lokacin da suka zo da bukata.

haka kuma wani abu da ya ce Mustaphan ya shahara a kansa wanda shi ma ya kara masa farin jini shi ne yadda yake nuna wa matasa cewa, su yi siyasa mai tsafta dominlokaci ya wuce da za a yi bangar siyasa, saboda haka su dauka duk wanda ya ce su zo su yi bangar siyasa makiyinsu ne, amma idan ya ba su kudi su karbe, kuma su zabi abin da suke ganin shi ne  mafita a wajensu.

Saboada haka ya ce da yardar Allah wannan karon za su ga canji na hakika matutukar al’ummar mazabar Jigawa ta tsakiya sun ba dan takarar na su goyon baya yadda zai samu nasara.

Ya ce a baya an ta yi musu karyar canji amma kamar yadda ya fada a baya canjin da suka samu na wahala ne, daga sauki zuwa wahala. saboda haka ne ma ya yi addu’ar cewa, kada Allah ya sake maimaita musu irin wannan  lokaci

saboda haka dai a halin yanzu an riga an yi walkiya gari yawaye yanzu haka ana kallon kowa tangaran babu wanda zai yaudari jama’a da suanan wani, shi ma wanin ai ga irin ta nan kamar yadda ake cewa.

Don haka ya yi kra da babbar murya ga al’ummar wanna yanki na Jigawa da dukkan wanda ya isa zabe ya tabbatar ya karbi kuri;’a domin da ita ne kadai za ka iya zabar wanda kake so ka zaba, saboda haka da zara lokaci ya yi mutane su fito su karba domin kada kuri’arsu.

saboda haka ya ce su a gurinsu gazawar da jam’iyya mai mulki ta yi alheri, domin kuwa yanzu abin da jama’a ke cewa gara jiya day au. saboda haka wanna karon ba za su yarda da yaudara ba.

Exit mobile version