Connect with us

LABARAI

Da Na Sani Da Tuni Na Koma Jam’iyyar PDP – Godwin Obaseki

Published

on

Gwamnan jihar Edo, Godwin Nosaghase Obaseki, ya bayyana cewa da ya sani da tun kafin yanzu ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP maimakon zaman azabar da yayi a jam’iyyar APC.

Ya ce maimakon APC da ta ci mutuncinsa lokacin da yake fuskantar kalubale, PDP ta nuna masa kula da soyayya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayinda ya ke karbar takardar shaidar nasara a zaben fidda gwanin jam’iyyar tare da mataimakinsa, Philip Shaibu.

Obaseki yace: “Sai da muka shigo gidan nan (PDP) muka gano ashe nan ya kamata ace mun kasance tun farko.”

“Ni da mataimaki na muna matukar godiya ga wannan babbar jam’iyyar. Kuma kamar yadda nace, mutum bai sanin abinda Allah ya tanadar masa.”

“A lokacin da muke cikin halin kunci, lokacin da aka koremu cikin ruwa daga jam’iyyarmu, kun zo mana da babbar lemarku kuma kuka lullubemu.”

A bangare guda kuwa, Gwamnan Godwin Nosaghase Obaseki, ya yi ikirarin cewa lallai zai zarce kan kujerarsa na gwamna na karin shekaru hudu.

Obaseki ya bayyana hakan da safiyar Juma’a, 26 ga Yuni yayinda ya ke godiya bayan an bayyanaahi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP a taron gangamin da ya gudana a Benin, babbar birnin jihar.

Ya siffanta nasararsa matsayin wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben gwamnan 19 ga Satumba matsayin babbar nasara kan makiya dake kokarin kwace dukiyar jihar don cin gashin kansu.

Yace: “A yau, an kafa tarihi a Nijeriya, saboda nasarar da muke murna yau wata sufuri ce zuwa yanci na siyasa. Idan Allah ya yarda zan sake zama gwamna na karin shekaru hudu.”

Obaseki ya jinjinawa sauran yan takaran, shugabannin jam’iyyar PDP, gwamnonin jam’iyyar da magoya bayansu da suka “sanyashi karkashin lemarsu lokacin da APC ta sharoshi cikin ruwa.”

Yayin sanar da nasararsa, shugaban kwamitin zaben fidda gwanin kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Kauran Bauchi, ya ce Obaseki ya samu kuri’u 1,952.
Advertisement

labarai