Rabiu Ali Indabawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home SANA'A SA'A

Da Sana’ar Dinki Na Mallaki Abubuwa Da Dama –Lawan Gogori

by Rabiu Ali Indabawa
June 30, 2019
in SANA'A SA'A
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Da farko za mu so ka fadawa masu karatu sunanka

Sunana Alhaji Lawan Gogori, ni mutumin Jihar Kano ne cikin Karamar Hukumar Bagwai, amma ni a yanzu mazanin Abuja ne nan Garki.

To mecece sana’arka?

Sana’ata dunki 

Wane irin dinki, dinkin dai-dai ko surfani ko kuma dinkin hannu?

A’a dinkin da-dai

To iya saninka meye tarihin wannan sana’a ta dinki?

Eh, to tana da tarihi, tun da tarihi ne da samu tun kafuwar duniya, domon akwai Annabin da ya zama shi ma madinki ne, to daga kansa aka fara samun tela. Don haka dinki abu ne mai asali da tarihin gaske ba wai karamar sana a ce ba.

To wannan sana’a gadonta ka yi ko kuwa dai ka ga yadda samunta yake ne ka shiga?

A’a ni ban gad aba, iyakaci ina matashina tun ina Kaduna tun da a Kaduna na tashi a nan Barnawa a nan ne na koyi sana’ar dinki Allah ya kaddara dama ita ce, za ta zama abincina. Kuma da ita na yi aure, na gina gida da duk wani matsayi da na kai a halin yanzu da ita na samu, duk shi ne sila.

Kawo yanzu ka kai kamar shekara nawa kana gudanar da wannan sana’a?

Na fara dinki, na kuma zama telan kaina tun a shekarar 1980 cif-cif, na fara zama mai gidan kaina ina shago a nan kuma Garki. Da na baro Kaduna an yaye ni na zo nan A buja wajen mahaifiyata na nemi shago na zauna na zama tela.

To tun da wannan sana’a kai ma koyonta ka yi, shin akwai wasu a karkashinka da ka koyar da su suke cin gajiyarta?

Eh, gaskiya akwai su suna da dama, akwai wadanda suke a raye, wasu kuma sun koma ga Allah, duk teloli ne kuma duk ni na koya masu. Ina ganin a nan Garki dai kafin ka samu tsohon tela kamar ni, gaskiya babu gaba da ni.

Baya ga shekarun da ka shafe a kan sana’ar, iya zamanka na Abuja ka kai kamar shekara nawa?

Ai kamar yadda na gaya maka a 1980 na zo.

Ita Abujan?

Eh kwarai kuwa, shagon farko ni na fara yinsa a nan Garki.

To baya ga abubuwan alkhairi da ka lissafa, akwai wasu abubuwa na ci gaba da ban?

Ci gaba da dama kai, tun da a yanzu a matsayina ina da jarin da zan iya sayen filaye da kudina, kuma ina da gida a nan nawa na kaina, kuma a Kadunan ma Allah ya kaddara ina gidana nawa na kaina, ai ka ga maganar ci gaba ma bata taso ba,sannan ga ‘ya’yana nan suna karatun Islamiyya da na zamani, kuma da wadannan na aurar, ai ka ga an samu ci gaba.

To tun da an tara iyali, kuma sana’ar ba ta ga maza ko mata kowa zai iya koya, shin kana son ‘ya’yanka su gaje ta?

A’a to sata ce? Ai tunda ba sata ba ce zan so a ce sun gaje ni mana, ai abar alkhairi ce, muka koya wa ‘ya’yan wasu? Kai akwai yaro da ya zauna a wurina har dan hali yake yi amma na rike shi don dai ya daina. Kuma hatta a shago na yana daukar min wasu abubuwa, amma ban kore shi ba, saboda ina so ya zama na kirki. Kuma a yanzu ina ‘ya’ya mata da suke karatu kuma suna nan suna koyar dinkin, kuma idan aka ce kana sana’a b aka so danka ya gada to ai magana ta lalace.

Shin ka taba samun tallafi daga hukuma a matakai daban-daban?

A’a ban taba samu ba.

Kenan hakan ya nufin ba ku da wata kungiya kenan?

Eh ba mu da kungiya cikakkiya gaskiya, saboda na yi kokarin nin kaina na kafa kungiyar, za ka ji yaran nan suna ce min Ciyaman-ciyaman, to dalili ni nayi kokarin na hada kungiya, sai muka dan fara tattaunawa. To irin kwarya-kwaryar mataki da aka fara yi na a samu dai Shugaba, sai aka ce ni na fara rike matsayin Shugaba, shi ne ya jawo har yanzu akwai yara masu kirana da Ciyaman. Amma ba a yi kokari ba, ka san mu yadda muke da sakaci mu Hausawa, sai ya zamto maimakon a yi kowa sai ya fandare, sai an shirya za a yi taron sai ka ga bai fi mutum biyu ne za su zo ba, a gidan sarkin Hausawa nan muke taron, sai mu yi ta zama daga baya sai a ce a daga sai wani lokaci, a haka muka watse.

To wane irin kalubale ka fuskanta a wannan sana’a daga lokacin da ka koya zuwa yanzu?

To ka san yanzu akwai banbancin tarbiyya, domin ka ga a wancan lokacin za a iya aike ni sayen zare daga Barnawa in tashi na tafi Kakuri, a kasa zan je na sayo zaren na kawo, sannan akwai lokacin da nake yin sawu biyu. Idan kuma hali yayi ina dan tarona a lokacin ko sisi sai na dauki haya, awa daya silai ne, rabin awa sisi, minti sha biyar shi kuma taro, a haka zan fafata in je na sayo na kai wa mai gida. Kuma zai iya sani ya ce, yi kaza-yi kaza, na yi masa ayyuka irin nasa na gida, saboda ina karkashinsa dole ne nay i ladabi a gareshi. B irin yanzu ba, yaro yana ganin gas hi ya zo ya koya a ce ya yi kaza ya ki yi, ko ko in ya zo kamar zai yi saboda yanzu tarbiyya yaranmu ba irin ta mu ba ce, sai ka ga yaro yana cikin faraway kafi ya iya sai ka gay a yaye kansa da zarar ya ga ya fara koyon dinka wando mai mazagi shike nan ya zama telayana ganin ya fara dinka ‘yar taguwa idan an huda masa ya dora, shi kenan ya zama tela.

Mu ko a lokacinmu bayan na koya a wurin bahaushe wallahi har komawa nay i wurin Iyamuri na koya, saboda ina dinka turoza, ina dika safari, ina dinka Kot mai shafi. Akwai lokacin da na yi suna a Garki, wallahi teloli daga Area 1 suke zuwa su ga Alhaji Lawan suna mamakin Bahaushe yana dinkin Turoza irin wannan, akwai inda muka je na dinka ma wani yaro wanduna ya sayi yadika daga Legas, da na dinka masa mun je kallon kwallo, sai na ga mutane sun zagaye shi an ace masa ya yi sabon kaya, sai ya ce, ai a Garki Billage aka dinka, kuma a zamanin muna amfani da dutsen gawayi, amma da ya nuno ni ya ce, ai ga wanda ya dinka min, sai na ga an yo kaina a guje, har na juya sai na ji yana cewa, nine Kwastomanka, to a nan sai na tsaya, da suka zo sai suka ce suna so su tabbatar da ni na dinka ko ba ni bane, to dama irin wandon ne a jikina da na daga sai suka ga babu banbanci, to daga nan sama da mutun 10 ne suka kawo min aiki.

To a karshe wane kira zaka yi wa ‘yan baya?

To kiran da zan yi shi ne su daure su koyi sanar su zama masu ladabi da biyayya ga masu koya masu aikin.

To mun gode

Ni ma na gode.   

SendShareTweetShare
Previous Post

Amfani Da Matsalolin Wasanni Ga Al’ummar Kasa (2)

Next Post

Ubangiji Makiyayi Ne

RelatedPosts

Yadda Na Zamanantar Da Sana’ar Xumamen Tuwo – Ummulkhairi

Yadda Na Zamanantar Da Sana’ar Xumamen Tuwo – Ummulkhairi

by Rabiu Ali Indabawa
1 year ago
0

Idan a na maganar matasa masu kishin kansu ta fannin...

Yadda Na Zamanantar Da Sana’ar Dumamen Tuwo – Ummulkhairi

Yadda Na Zamanantar Da Sana’ar Dumamen Tuwo – Ummulkhairi

by Rabiu Ali Indabawa
1 year ago
0

Idan a na maganar matasa masu kishin kansu ta fannin...

Dabarun Fuskantar Kiwon Kaji Don Riba

by Rabiu Ali Indabawa
2 years ago
0

Shi kiwon kajiya ko na sha’awa ko na Kasuwanci yana...

Next Post

Ubangiji Makiyayi Ne

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version