Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RIGAR 'YANCI

Da Sauran Rina A Kaba Kan Daina Kama ’Yan Fim A Kano, Cewar MOPPAN

Kungiyar Ta Nemi Hada Kan ’Ya’yanta Don Cimma Nasarar Yarjejeniyar

by Sulaiman Ibrahim
March 11, 2021
in RIGAR 'YANCI
2 min read
MOPPAN
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Nasir S. Gwangwazo

 

Uwar Kungiyar masu shirin fim a Arewa, ‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’ (MOPPAN) ta yi karin haske tana mai jan kunnen mambobinta da cewa, sabanin yadda aka fahimta tun da fari, har yanzu da sauran rina a kaba kan yarjejeniyar da suka cimma da Hukumar Tace Finafinai ta Kano kan daina kama masu sana’ar shirin fim a jihar. Don haka tana neman hadin kan ’ya’yanta, domin a samu nasara mai dorewa.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta aikewa da LEADERSHIP A YAU mai dauke da sa hannun Kakakinta, Al-Amin Ciroma, inda ta yi kira ga dukkanin ‘ya’yanta dake Arewacin Nijeriya da su bayar da gudunmawar samar da hadin kai a tsakanin juna domin cimma nasarori a cikin tsarin shirinta na inganta masana’antar fim din Kannywood.

Kungiyar ta bayyana hakan ne jim kadan bayan wani zama na musamman da ta yi da Hukumar Tace Finafinai da Dab’ita Jihar Kano, a karkashin jagorancin Alhaji Isma’il Na’Abba Afakallah, wajen samar da hadin kai da kuma yin aiki tare.

Haka kuma kungiyar ta yi kira da kakkausar murya, tare da jawo hankalin ‘ya’yan nata a kan wannan zaman na musamman da ta yi da hukumar, inda aka cimma manufar fahimtar juna, ta inda bangarorin guda biyu suka samar da kudurorin da suke gani za su iya kawo ci gaba mai dorewa a masana’antar ta Kannywood.

Kan haka ne MOPPAN ke kara bayyana wa dukkanin masu ruwa da tsaki cewar, matakan cimma waccan yarjejeniyar sun hada da;

“Rubuwa hukumar takardar bayan zaman da aka yi, tare da neman yardarta a kan dukkanin bukatun da aka bijiro da su.

Na biyu, ita ma hukumar za ta yi zama na musamman da kwamitinta na zartaswa, domin samar da yanayi mai inganci dangane da bukatun bangarorin, sannan a samar da sahalewar gwamnati.

Na uku, za a sake wani zama tsakanin bangarorin biyu domin bin kudurorin daya-bayan-daya, da fitar da hanyoyin aiwatar da su.

Na hudu, MOPPAN za ta tattauna da sauran kungiyoyin da ke kawance da ita da kuma membobin da ke cikinta, a’inda zata wayar mu su da kai dangane da yarjejeniyar, kana ta nemi amincewarsu da kuma fitar da yadda za a yi aiki tare.

Na biyar, MOPPAN zata kafa kwamitin Ladabtarwa mai zaman kansa, kana kuma da sauran kwamitocin gudanarwa.

Na shida, sannan a yi gangami (Conference) na wayar da kai da kuma tattaunawa a kan gudurorin sannan a tsayar da ranar fara aiwatar da su yadda yarjejeniyar ta tabbatar.”

A karshe, Shugaban MOPPAN na kasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga ‘ya’yan wannan masana’anta da su bayar da hadin kai, kuma su guji yin duk wani lafazi ko abin da zai dakile wannan ci gaban da ake kokarin samarwa ga masana’anta.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ba Ma Tunanin Korar Mourinho – Tottenham

Next Post

An Yi Wa Gwamnan Jigawa Allurar Rigakafin Korona Jiya

RelatedPosts

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

Kansila Mai Mataimaka 18 Ya Sadaukar Da Albashinsa Na Farko

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Daga Abdullahi Muh’d, Kano Shugaban Gidauniyar ‘Charity’ mai rajin tallafa...

APC

Sanata Al-Makura Ya Cancanci Rike Kujerar Shugabancin APC, Inji Gwamna Sule

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Zubairu M Lawal, A yayin da uwar jam'iyyar APC...

Shafukan

Bagudu Ya Bukaci ’Yan Nijeriya Su Zama Masu Kishin Kasa A Shafukan Sada Zumunta

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Umar Faruk, Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, a...

Next Post
Gwamnan Jigawa

An Yi Wa Gwamnan Jigawa Allurar Rigakafin Korona Jiya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version