Abdullahi Muhammad Sheka" />

Da Trump Ya Gayyaci Ganduje, Zai Koya Masa Yadda Ake Cin Zabe – Hon. Doguwa

Hon. Doguwa

Alhassan Doguwa, ya bayyana cewa, Ganduje wata cibiyar siyasace da babu irinta a Nijeriya.
Yace, da Donald Trump ya nemi shawarar Ganduje da ba yadda za’a yi ya fadi a zaben Amurka.

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta Tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya ce tsohon shugaban Amurka Donald Trump ba zai iya faduwa zabe ba idan da ya nemi taimakon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Doguwa, wanda ke wakiltar Mazabar Tudunwada da Doguwa, ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da aka turowa jaridar Daily Nigerian a ranar Laraba, yayin da yake yiwa magoya bayansa jawabi.

“Idan aka duba, lokacin da alkaluman suka fara nuna Trump zai sha kaye, ya kamata ya kira Ganduje a waya ya tura masa Murtala Garo ko Alhassan Ado ko Kawu Sumaila ko dan majalisa Kabiru Rurum. Labarin ba zai kasance haka ba a yau.

“A wurinmu, Ganduje cibiya ce ta siyasa. ‘Yan siyasa za su kwashe shekaru suna gaya muku karya game da cin zabe a 2023, kawai suna gaya muku shirme ne,” in ji Doguwa a cikin gajeren faifan.”

Yawancin masu sa-ido masu zaman kansu suna da ra’ayin cewa jam’iyyar APC mai mulki tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da manyan jami’an Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta, (INEC), sun yi magudi a zaben da aka yi a watan Maris 2019 don goyon bayan jam’iyya mai mulki.

 

Exit mobile version