Da Wa Za A Yi Kuka Bisa Karin Farashin Wutar Lantarki?

Talakawa dai na sane game da yadda aka samu koma baya a dukkan harkokin raya kasa da iganta rayuwar jama’ar cikinta, musamman ma a fannin samar da wutar lantarki, abin da karancinsa ya kawo durkushewar masana’antu da karuwar rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da na rufin asiri. Wadannan ne manyan dalilan da suka jawo rashin zaman lafiya a kasa, domin kuwa matasa, har ma da magidanta sun rungumi ta’addanci da aikata masha’a, talauci da fatara kuma suka mamaye ko’ina, lalaci ya yi katutu a zukatan jama’a, har ta kai shugabannin siyasa na sheke ayarsu yadda suke so, suna koyawa mabiyansu saka da mugun zare bisa akidojin kiyayya da tayar da husumar kabilanci da na addini.

Ta haka ne matasa suka lalace, da yawa daga cikinsu suka shiga fadace-fadace da juna; wasunsu suka koma sace-sace; aka samu gwanaye a harkar kashe-kashe; zaman lafiya da lumana suka gagara, aka komo kamar ba masu tsawatawa, tamkar ba wata kwakkwarar hukuma a kasar. To amma ba wadannan ne kadai illolin da suka dade suna addabar jama’a ba, kuma gwamnatocin baya suka kasa magance su, sai dai ana iya cewa duk wadannan masifun abu guda ne ya jawo su, watau koma bayan karayar tattalin arziki, sakamakon rashin wutar lantarki, kamar yadda sauran ma akwai dalilan da suka assasa su. Tun farkon komowar mulki hannun farar hula a 1999, Shugaba Olusegun Obasanjo ya sha alwashin magance matsalar wutar lantarki kwata-kwata a kasar nan, abin da ya danganta da rashin turzawar gwamnatocin baya da ‘yan Arewar da suka danka masa mulki suka jagoranta, wajen tunkarar matsalar tun tana ‘yar karama har sai da ta gawurta. Kafin kiftawa da bismillah sai ga sabon minista na wutar lantarki a wancan zamanin, Cif Bola Ige ya ce, cikin watanni shida za a samar da ingantacciyar wutar lantarkin da ba za a rika dauke ta ba a ko’ina a fadin tarayyar kasar nan.

Amma me ya faru? Me kuwa in ban da sakaci irin wanda ya dara na sojojin da ake zaton su ne suka hana ruwa gudu? Wasa-wasa dai sai ga wankin hula ya kai gwamnatin Obasanjo maraice, kuma sai da aka yi shekaru takwas, aka kuma narkar da makudan kudade na fitar hankali, amma duk da haka nan wutar ba ta samu yadda ake bukata ba, domin kuwa wadannan kudaden zurarewa suka yi zuwa aljifan shugabannin da aka kasa hukuntawa wadanda aka tabbatar suna da hannu dumu-dumu wajen salwantar dukiyar da aka tanada don giggina sabbin tashoshin bayar da wutar lantarki da kuma kyautata hanyoyin rarraba ta zuwa dukkan lungunan da ake bukatar amfani da ita. Ba abin da aka yi don kwato wannan dukiyar, domin gafiyoyin da suka handame ta sun tsira da na bakunansu.

Gwamnatocin da suka biyo baya ma haka nan suka shantake game da batun karfafa wutar lantarki, ba wani abin da suka yi sai burgar aiki da yankawa talakawa karerayi game da wa’adin kammala ayyukan, sai kuma daga bisani a sake yankan wani wa’adin, a kuma kawo wata ladifiyar hujja a dangana ta da gazawar da aka yi wajen cika alkawurran. Ba wani abu ba ne ke hana kammala ayyukan samar da wutar lantarkin ba illa jajircewar shugabanninmu wajen sayar da hukumar wuta ta PHCN ga wasu attajirai, wadanda ke wasa da hankalin gwamnati wajen biyan awalajar kamfanonin da suka taya, aka kuma sallama masu, amma ba ki biya kan kari. To yanzu ga shi nan kowa ya gani, wai an yi wa ‘ya mugun miji, tabarbarewar wutar lantarki ta kai intaha a kasar nan kafin saukar gwamnatin da ta gabata wacce haka nan ta danka wa Shugaba Buhari mulkin kasar na cikin matsanancin duhu, kuma babu wata na’urar da ke motsawa saboda karancin wutar da ta talauta talakawan kasar nan. Haka nan dai wadancan gwamnatocin da shugabansu suka shantake, suka shiga sharholiyar banza da dukiyar da ya kamata a sarrafa ta wajen inganta hanyoyin samar da wutar lantarkin da za su farfado da masana’antun da suka durkushe da siradansu. Babu kunya, ba tsoon Allah, suka yi ta cika baki da fariyar banza, wai suna samar da wadatacciyar wuta, kuma hakan na amfanan masana’antu, alhali kuwa kowa ya san sun dade da zama fanko.

Shi ya sa Shugaba Buhari bai yi wani kawaici ba wajen fayyacewa ‘yan Nijeriya cewa kasar fa ta tsiyace, kuma gwamnatinsa ta tashi tsaye wajen daukan matakan magancewa da suka hada da kwato dukiyar haram din da azzalumai suka handame da kuma dukufa ka’in da na’in wajen fadada ayyukan gona da hakar ma’adinai, domin wadannan ne kawai masana’antun da aka tabbatar za su iya samar da ayyukan yi ga milyoyin matasa da magidantan da ba su da abin yi. Yin haka shi ne mafi a’ala, kuma gwamnatin shugaba Buhari ta samu nasarar kwato dukiyar da aka sassace, aka tsibe a ketare. Sai dai kash! Maimakon wadannan kudade a yi wa talakawa amfani da su wajen inganta rayuwarsu da samar da masana’antun da milyoyin matasa za su samu aikin yi; sauran kuma a karkata su wajen hakar ma’adinai. Amma abin takaici ga kudaden nan kowa ya san cewa an kwato su a hannun azzalumai amma an rasa abin da aka yi da su, ko an yi watangaririya da su ne wasu mahandaman sun kafa musu kahon zuka?

Babu wani talaka wanda bai fada ko ya ayyana a zuciyarsa ba cewa kamfanin wutar lantarki ta Nijeriya da gwamnatin baya ta sayarwa ‘yan kasuwa suke damawa yadda suke so, Buhari ba zai maido ta hannun gwamnati ba idan ya samu nasarar cin zabe a 2015; kuma ko shi Buharin da bakinsa sa ya sha fada a wajen yakin neman zabe cewa shi bai san wani kamfani da ake kira PHCN ba, da NEPA ya sani tun tuni; to ba mu sani ba ko yana fada ne cikin raha a wancan lokacin?

To ga shi nan dai yanzu wutar lantarki ta zama abin da ta zama, bayan biyan kudin zama a duhu, da talakawa ke yi, sai ga kuma dan karen karin kudin da kamfanin ke yi lokaci zuwa lokaci. A cikin shekarar da ta gabata dai kusan kamfanin ya yi shelar karin kudin wutar kusan sau uku a jejjere, kuma a daidai lokacin da kasar ta shiga masifaffen koma bayan tattalin arziki, a lokacin da annobar Korona ta tagayyara talakan da ke fita kullum domin nemo abin da zai ci ya sha da iyalansa.

Sai ga shi kwatsam cikin satin farko na sabuwar shekarar nan hukumar kula da farashin wutar lantarki a Najeriya ta Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) ta amince da fara aiki da wani sabon karin kudin wutar da kashi fiye da 50 cikin 100. Wannan karin fa ya zo ne wata biyu kacal da yin irin wannan karin kuma na yanzu zai shafe na watan Nuwamba da aka yi.

Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito wata takardar umarni da sabon shugaban hukumar mai suna Injiniya Sanusi Garba ya sanya wa hannu ranar 30 ga watan Disamba na cewa karin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2021. Inda hukumar ta ce ta yi la’akari ne da tashin farashin kaya na kashi 14.9 cikin 100 a watan Nuwamba, da faduwar darajar naira zuwa N379 kan dala daya ya zuwa watan Disamba, da karfin samar da wutar lantarkin, kafin ta yi karin kudin.

Wannan karin zai shafi kowane aji na masu amfani da wutar, sabanin na Nuwamba, wanda bai shafi masu shan wutar a mataki mafi karancia ba. Karin da aka yi a watan Satumba na iya kudinka iya shagalinka ne, wanda ya jawo tayar da jijiyoyin wuya daga ‘yan kasa da kuma kungiyoyin kwadago, abin da ya sa gwamnati ta jingine shi kuma ta shiga tattaunawa da gamayyar kungoyiyin.

Za dai mu iya cewa a halin yanzu kowane bangare na ma’aikatu da kamfanoni sun raina baba Buhari, suna aiwatar da duk abin da suka ga dama, kuma abin da ransu ke so, ko da kuwa ba zai yi wa talaka dadi ba, ko hakan na nufin sun dauki Buharin irin karkatacciyar kuka din nan mai dadin hawa, sun dauke shi haka-haka, wanda ba ruwan shi da shiga lamuransu, ba Buharin da suka sani ba ne a baya shi ya sa ma’aikatan gwamnatin da kamfanoni suke rawarsu yadda suke so.

Shi dai shugaban kasa Muhammadu Buhari talakawa da masu kudi da ‘yan siyasa sun yi masa kyakkyawar shaidar bai barawo ba ne, ba kuma a taba samun shi da cin dukiyar kasa ko cin amanar ‘yan kasa ba, kuma tun kafin ya yi nasara a zaben 2015 yake fada a wajen yakin neman zabensa cewa zai yaki cin hanci da rashawa, zai dakile duk wata barna da azzalumai suke yi.

Sai dai kamar muradansa da burinsa na yin hakan ba su cika ba, saboda yadda aka fara aiwatar da kakkamo ‘yan rashawa da masu cin hanci tun farkon hawansa, kamar ana yi ne don yi wa jam’iyyun adawa bi-ta-da-kulli da kuma lalata kadarinsu a wajen al’ummar da ke ganin su da mutunci. Kamar hakan ya sa duk wanda ke cikin jam’iyya mai mulki ya zama dan lele, babu mai tuhumarsa da sata sai dai idan ya nemi ya yi wa shugabanni da iyayen jam’iyya rashin da’a da biyayya; to a nan fa sai masu azata ta zauna su cinna shi da hukumar  EFCC ta dinga tatsar sa kamar nono, sannan kuma a bata masa suna.

A irin wannan marrar da talakawa suke fama da bakin talauci da takaicin hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen mutane da dabbobi musamman a jihohi 19 na yankin Arewa, wanda kusan kullum ake daukar ran dan Adam, sai kuma a ce gwamnati ta zura ido ta kyale ana cutar da talakawan da suka jure zafin rana da yunwa don dora su kan kujerun da suke kai a yanzu, a maimakon ta tabuka ko ta tsawatar don saukake wa talakawa, amma kullum sai tsawwala musu ake yi. To yanzu da me talaka zai ji, da biyan zunzurutun kudin wutar da sai a karshen wata ake samunta ko kuwa da kudin sayen masarar tuka tuwo?

Wai ko dai gwamnati ba ta san cewa akwai cuwacuwa da magu-magu tare da tsananin cin hanci da rashawa da ta kaka-gida a hukumar samar da wutar lantarki ba ne? Cin hanci da cuwacuwa ya riga ya zama dabi’un wasu daga cikin ma’aikatan su, mafi akasarin su ba suna aikin ba ne don al’umma, suna aikin ne don karawa aljifansu nauyi.

Ya kamata a gwamnati ta sani cewa hatta mitar da aka kawo don kamfanin ya sayarwa kwastomiminsa kudi hannu ko bashi, to ita ma akwai harkalla a cikinta. Hatta kamfanonin da ke samar da mitar, wadanda kuma kamfanin samar da wutar lantarkin ya dauke su don aikin makalkala mitocin, su ma akwai ayar tambaya akan su, ya kamata gwamnati ta binci kowane bangare da ya shafi wutar lantarki don sanin gaskiya al’amari.

Da karshe ina kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da kuma ministan wutar lantarki Mista Fashola da sauran masu ruwa da tsaki a fannin akan su dubi halin da talakawa suke ciki na kuncin rayuwa, fatara, yunwa da tashe-tashen hankulan da ke damunsu, a waiwayi wannan al’amari na karin farashin wutar lantarki da hukumar ke yi ba kaukautawa, a saukaka wa talakawa. Idan ba haka ba da wa za a yi kuka? In ce da gwamnatinku, kuma wadda jama’a suke yi wa kallon gwamnatin mai gaskiya.

Exit mobile version