Da yawa mata masu sana’a kan shiga cikin rudani wurin zabar hanyoyin da za su bi wajen bunkasa sana’arsu. Sai dai bakuwarmu ta wannan makon ta ce ta zabi yanar gizo domin ta rika yin amfani da ita wajen bunkasa sana’arta. Ku kuma fa masu karatu? Ga hirar da muka yi da ita wadda a ciki ta bayyana takaitaccen tarihinta da yadda ta fara sha’awar sana’a har ta kama yi:
Da farko masu karatu za su so jin cikakken sunanki, da sunan da aka fi sanin ki da shi.
Sunana Rukayya Saeed amma an fi sani na da Rukky.
Ko zaki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarinki?
Ni ‘yar jihar Kano ce amma Kaduna na tashi, na yi primary da secondary da Jami’a duka a Kaduna kuma English Language na karanta a Jami’ar Kaduna wadda aka sani da KASU.
Shin kina ci gaba da karatu ne ko wata sana’a ko zaman gida kawai kike?
Na kammala karatu na yanzu haka dai sana’a nake yi.
Ina ‘baking’ irin su cake su cincin da samosa da small chops sai kuma ina girke- girke na biki.
Za ki kamar shekara nawa da fara sana’ar?
Na kai shekara uku da farawa
Me ya ja hankalinki har kika fara sana’ar?
Mamata ta kan yi irin abubuwan nan a gurin ta na sama ‘inspiration’kuma ita ta sa ni a kan hanya.
Kafin ki fara ita sana’ar da kike yi, shin kin nemi shawarar wasu dan neman sanin yadda ake yinta, ko zuwa kikai aka koya miki, ko dai kawai farawa kikai da kanki?
Mamata ta koya mun komai da komai.
Ya karbuwar sana’ar ta kasance wajen su masu sayan kayan, kasancewar shi ne farkon farawar ki a lokacin?
Da farko dai kawaye na da mutanen kusa da ni suke siya suka ji dadin shi suke fada wa mutane har na fara samun ‘customers’ da yawa.
Ta wacce hanya kike bi dan ganin kin bunkasa kasuwancinki?
Daga lokacin da kika fara ita wannan sana’ar har kawo iyanzu, wanne irin nasarori kika samu game da sana’ar?
Nasarar da muka samu a wanan sana’ar ita ce yadda mutane suke san mu kuma suke sayen kayanmu.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta game da ita sana’ar, musamman ga su masu sayen kayan?.
Masu karban bashi da masu ‘late order’ shi ne babban kalubale da muke fuskanta.
Ko akwai wadan da kike koyawa sana’ar, idan babu, shin kina da sha’awar koyawa wasu?
Eh, ina koya ma mutane sosai.
Me za ki ce ga mata na gida musamman wadanda suke zaune kawai ba tare da wata sana’a ba, wacce shawara za ki basu?
Shawarar da zan bawa ‘yan uwa na mata shi ne su tashi su nema sana’a dan zama haka ba zai amfane su ba.
Idan kika ci karo da matan da suke zaune a gida basa wata sana’a ya kike ji a cikin zuciyar ki?.
Gaskiya ba na jin dadi kuma suna ba ni tausayi.
Wacce shawara za ki bawa mata na gida masu jiran miji?.
Shawarar da zan ba su ita ce yanzu ba a jiran miji, ya kamata su ma su dinga tallafawa.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati wajen ganin ta taimakawa masu sana’a?
Su ci gaba da tallafa mana yadda suke yi.
Menene burin ki na gaba game da sana’ar ki?
Ina son na ga na bude babban shago na cin abinci da siyar da cake kuma mu Dauka ma aikata suma mu tallafa musu.
Ko kina da wata shawara ko dan tsokaci da za ki ga sauran ‘yan uwa masu sana’a?.
Su ci gaba da sana’ar su kuma su tallafawa al’umma.
Me za ki ce ga makaranta wannan shafi na Adon Gari?
Su zo su siya abubuwan da muke yi kuma na tabbatar musu ba za su yi nadama ba.
Me za ki ce da ita kanta LEADERSHIP A Yau Juma’a?
Ina godiya da bani wanan dama da lokacin da kuka yi hira da ni, Allah ya sa ku fi haka.