Sulaiman Ibrahim" />

Dabarun Fuskantar Kiwon Kaji Don Riba

Shi kiwon kajiya ko na sha’awa ko na Kasuwanci yana kawo jin dadi sosai, da nutsuwa musamman ma in an yi shi yadda ya dace.

Wa’annan shawarwarin ana samun sune daga https://farmright.co ta yadda zai koya maka yadda za ka Noma gonarka sannu-sannu, kuma ka koyi noman, shi kanshi, kuma ka koyi yadda ake gyaran gona, kai harma yadda ake aje rubutaccen shige da fucen harkokin Gona. Shin wai me kake bukata ka fara kiwon kaji?

Jari

Tanan ne ake farawa, lallai kiwon kaji yana bukatar kudi a koda yaushe, amma ribarshi ta can-can-ci hakan. Na farko dai kasan girman gonarka. Duk da cewa dai burin kowanne manomi ne yaga yana da babbar gona, to lallai kuwa ya dace manomi ya dinga shirin kiwon babbar gona. Mafi yawancin manoma suna farawa ne da karamar gonar da suke da ita, sai dai ana basu shawara da cewa ya kamata su fara da karamar, sai dai in suna da jari mai yawa to ba laifi su fara da babbar gonar.

Wannan shine kimantawa na ribar gonarka in kana kiwon Broilers.

In kana kiwon kaji daga 100–1,000 kana bukatar akalla daga N100,000 zuwa N700,000 Don kiwon su, to harajin ka zai zama tsakanin N200,000 zuwa N2.5 Million sannan dai-dai girman jarinka dai-dai girman ribarka. Matukar kana da kayan aikin ka to zai ishe ka zuwa wasu shekaru masu yawa. Amma ga sabon manomi akwai wurare da yawa inda zai iya aron wa’annan kayan aikin.

Ya dace kafara wannan kiwon da kudin asusunkane ba da rancen Banki ba, kamar kashi goma (10%) zuwa Kashi (30%) ace kudin ajiyar kane, lokacin da ka fahimci kiwon da kyau ka iya zuwa Banki don neman karin jari. Ka tuna cewa, fara wa da kadan shi ne burgewa, Ka bar nasarar kiwonka ta bayyana yiwuwan karuwar jarinka.

Samar Da Gona

Ita nasarar kiwon kaji ya danganta da inda gonarka take. Shi kiwon kaji yafi kyau a kwayuka ta yadda tsadar gonar da ta ma’aikatan gonar ba tsada sosai.  Duk da hakan dai, kasa a ranka cewa inda za ka sa gonarka ka tabbatar akwai hanya ta shiga da fucen kayan gonarka, kuma akwai ruwa a garin. Kuma ka tabbatar ruwan zai ma saukin samu, kuma sannan in san samune, gonarka ace tana kusa da inda kake zaune da iyalenka ko kuma duk dai wanda zai kula da gonar ace yazama mazaunin unguwar da gonar take ne.

Abincin Kaji Da Kyankyasar Farko

Wannan yana tafiyane kai-da-kai: Abincin Kajin da yadda ake samo shi, ya danganta da kalan irin kajin da kake so ka kiwatawa, amma dai in kanason kajinka suyi girman daya dace to dole kanemo kamfanin abincin da ka tabbata kowa yana yabonsu akan yin abinci mai kyau.

Yana da matukar amfani kasan cewa dai ingantaccen kiwo yana daga Farkon kajin daka siya. To duk sadda za ka sai kajin kiwo ka tabbatar kayi bincike da tambayar masana kafin siyan. In aka samu akasi wajen siya aka siyo wanda ke da matsala to tun daga nan fa kasa kanka cikin asara.

Tsarin Gidan Gona Da Kayan Gidan Gona

Akwai abubuwa da dama da ya dace a lura dasu lokacin gina Gidan Gona. Wannan abubuwan su za su taimaka wajen sanin irin tsarin gidan gonar da za ka gina. Shi tsarin Gidan Gona an kasa su ne kamar haka: Karamin Tsari, Tsari Matsakaici da Kuma Babban Tsari. Ga sabon Manomi, ya dace ya fara da tsarin daya dace da Jarin da yake dashi a yanzu (Wato karamin tsari). Shi Matsakaicin Tsari da Babban Tsari mafi yawanci masu manyan jari da Babbar Gona su suka fi yinshi ta yadda kajinsu za su samu kula da sakewa sosai. Sai dai babbar matsalar wannan tsarin shi ne sata.

Kuma kayan kiwon kaji ana kawo musu irin na  sune kamar, abincinsu, kayan Shan Ruwansu, Kayan jin diminsu, kejinsu, da dai sauransu.

Ciyarwa Da Shayarwa

Kashi tamanin cikin dari na ayyukanka da lokutanka dole su tafi cikin ciyarwa da shayarwa. Kayi abin da duk ya dace kayi to yanzu wannan shi ne aikin yau da kullum. Kuma dole ka tabbatar da cewa kajinka suna samun ingantaccen ruwa kullum. Musamman ma In kaji ne masu kwai. Don in babu ruwa ingantacce To lallai lokacin haihuwar su zai yi Jinkiri.

Haka ma ciyar wa, In basu samu ingantaccen abinci ba za a samu Jinkiri wajen Samun kwai. Dole ka tabbatar da cewa kajinka sun samu ingantacciyar kulawa ta ciyarwa da shayarwa. Ciyarwa da shayarwa ita ce babban kalubalenka na yau da kullum.

Yin Magani Da Allurori Don Kula Da Lafiyarsu

Yanzu ne lokaci na kira Likitan dabbobi akan lokaci. Akwai jerin lokutan bada magunguna da allurai don kula da lafiyar kajin da ake kiwo. Kuma lallai kana da bukatar neman shawarwarin kwararrun Likitan dabbobi kamar yadda Ake karin magana da cewa wai “Taya Allah kiwo yafi Allah na nan”.

Da yawa wasu manyan gidajen gona kajin gaba daya suka kare saboda wani ciwo da ka iya afkuwa, ko rashin kyakkyawan kula wanda da an kula da hakan da bata faru ba. Musamman ma abun da ya faru 2007/2008 Lokacin da masassarar tsintsaye Ta afko Nijeriya.

Kasuwanci Da Sayarwa

Bayan dukkan Kula da jarumta, kaima kana bukatar riba ko biyan bukatar ayyukanka da wahalhalunka. To a nan ne za kai duk lissafin abun da akai a baya. Kamar yadda suke cewa “Kafin kafara tafiya, kasan inda zaka” Yana da matukar amfani ka yanke shawara kan yadda zaka saida kayan gonarka. Sananne ne cewa dai kayan gona ba masu tabbata bane–in lokacin su ya yi dole ne a rabu dasu. To anan abun da ya dace afi lura da shi shi ne yadda za a dibesu akai su wajen saidawa.   

Ajiye Tarihin Gona

Rubuta lamarin gona na yau da Kullum ya dace a rubuta kuma a ajiye. Kamar ajiye yanayin cin abincin kajin dai-dai da yadda suke kara girma, Yanayin shan ruwansu, magungunansu da alluransu, kullum kwai nawa suke yi, kwaya nawa suka mutu, da dai rubuta duk wani tsarin gudanarwar gonar. Shi ajiye irin wannan tarihin yana taimakawa wajen kawo sauki agaba (wajen sake gudanarwa da hangen Nesa).

Exit mobile version