Connect with us

NOMA

Dabarun Kiwon Kaji A Zamanance

Published

on

 

Asalin Kajin

Ganin yadda yawan al’ummar duniya ke bunkasa, wanda kai tsaye ke nuna karuwar bukatar abinci da nama. A bangare daya kuma ilimi ma yana ta kara bayyana da saukaka, shi ne ya sa masu ruwa-da-tsaki a harkar dabbobi kamar Malaman noma da kimiyyar halittu, da kuma Likitocin dabbobi (Animal Scientists, Agric Engineers, Animal Doctors, Genetic Engineers etc), suka zauna suka tattauna a kan yadda za’a inganta kajinmu na gida, su zama suna kwai ko wane lokaci, kuma suna saurin girma a kankanen lokaci ta yadda za’a sami isasshen kwai da nama ga al’ummar duniya. Wannan kuwa ya faru ne a kasashe daban-daban, musamman kasashen Turai da Amurka wajen shekaru dari daya da suka gabata. A sakamakon haka, an samu ci gaba sosai a harkar kiwon kaji da sauran tsuntsaye da ma dabbobi gaba daya. Yanzu alkaluma sun nuna cewa sama da kaji Biliyan Hamsin ne ake kiwatawa a duniya duk shekara.

Nijeriya kuma na sahun gaba a Afrika wajen harkar kiwon kaji.

Rabe-Raben Kajin Turawa Za’a iya kasa kajin gidan gona ta la’akari da amfaninsu kamar haka:

  1. Kajin kwai ko Leyas (Layers a Turance): wadanda ake renonsu daga rana ta farko har tsawon sati 16-18 kuma su kan fara nasa kwai a tsakanin satinsu na 16 zuwa 20. Suna ci gaba da yin kwai har shekara daya da ko daya da rabi, in dai akwai kula sosai suna iya kaiwa fiye da haka.
  2. Kajin Nama ko Biloras (Birolas a wata Hausar) (wato Broilers a turance): Wadanda ana renonsu har tsawon sati 7, 8 ko sati 10 gwargwadon yadda mai kiwo ya bayar da dama. A wannan lokacin ake sayar da su a kasuwa.
  3. Kwankwaras ko (Cockerels): wadannan su ne mazajen layers masu kwai.

Kwankwars sune wadanda kamfanin kyankyasa baya bukatarsu sosai, saboda da haka ake sayar da su da matukar arha, su ma suna daukar sati 16-20 kafin su girma. Kuma sun hada da launin farare da bakake masu dishin-dishin fari ko wake-wake.

To ta yaya za a yi kiwon kaji ba tare da samun matsala ba domin kiwon kaji na tattare da matsaloli da daman gaske, yawan asarar da ake tafkawa ya sa mutane da dama ke gudun shiga harkar kiwon kaji, amma wadanda suka jure matsalolin da a kan fuskanta a kiwon kaji suna bayar da labarai masu dadin ji a kan alhairin da suke samu a harkarsuna kiwon kaji, saboda karfafa gwuiwa ga masu hankoron fada wa kiwon kaji, mun dan tsakuro maku wasu matakai masu mahimmanci day a kamata mai sha’awar fara kiwon kaji ya dauka domin samun alhairin dake ciki, matakan sun hada da;

  1. Shawarar irin kajin da kake son fara kiwo.

A nan yana da matukar mahimmanci ka san wadanne irin kaji kake da sha’awar fara kiwo, kuma mene ne makasudin ka na shiga harkar kiwon, kana son mai kwai ne ko domin nama ko kuma dai zaka yi ne domin cinka kai da iyalinka, sanin wadannan bayana,yana da mahimmanci, da yawa wasu na shiga harkar kiwon kaji ne ba tare da sun san ainihin abin da suke so ba.

  1. Zana bangaren Da Kake Son Ka Shahara A kai Ba zai yiwu ka mamaye dukkan bangaren da ya shafi harkar kiwon kaji da muke da shi ba, a kwai bukatar ka zayyana bangaren da kake son ka bayar da karfinka a kai, yin haka kuma zai taimaka sosai ya ba ka natsuwar da za ka amfana da

 
Advertisement

labarai