Dabarun Noman Tafarnuwa A Saukake

Daga Abubakar Abba,

Tafarnuwa na daga cikin nau’o’in abubuwan da ake nomawa musamman domin sayarwa. Ba za a iya tasa tafannuwa a ci ba a matsayin abinci, sai dai a nomata a matsayain abar sayarwa, musamman a wannan kasa ta mu ta Nijeriya.

Noman Tafarnuwa, hanya ce ta samun kudi ga manoma masu yawa, domin kuwa takan yi tsada matuka.

Baya ga hada-hadar kasuwancinta a cikin gida ana fitar da ita zuwa wasu kasashen duniya. Tafarnuwar da ake yi a Nijeiya na cikin sahun gaba wajen daraja a duniya. Wani gari da ake kira Kofa da ke karamar hukumar Bebeji.

Inda aka amfani da tafarnuwa:

Ana yin amfani da tafannuwa kusan a dukkan fadin duniya. An  gano ta ne shekaru masu yawa da suka wuce, inda wasu masana a fannin noma ke nuna cewa, an samo ta ne tun kimanin shekara 5,000  da suka gabata.

Yadda Ake Samun Kudi Da Noman Tafarnuwa:

Da farko dai, ka tanaji kayan aiki,dole sai da kayan aiki  za ka cika burin da ka sa a gaba.

Yanayin Girman Gurin Da Za Ka Shukata.

Akwai bukatar wanda zai dasa ta, ya kasance ya samar da kamar da sararin da ya kai kimanin inci 4 zuwa 6, haka ana bukatar  zurfin ramin da za a dasa ta ya kai zurfin daga 10 zuwa 1

Dabarun Fara Wannan Noma Don Kasuwanci:

Kana iya fara dasa ta a bayan dakinka kuma wajen ya kasance ya na da fadin da ya kai kafa 500 zuwa 600, musaman idan kana son ka samu kudi.

Kana iya dasa ta da kaka, musamman ganin cewa, akwai masu bukatar ta da dama, kuma kana iya fara nomanta dan kadan daga baya kuma ka kara yawanta.

Ana bukatar manominta ya kasance yana kiyaye ta daga kamuwa da cuta, mussaman ya kamata ya tabatar da yana yi mata feshe.

Bukatar Dasa Ta  A Yanayin Da Ya Kamata:

Tafarnuwa na bukatar yanayi mai kyau, musamman mai sanyi don ta fi saurin girma domin bata jure wa yanayi na zafi.

Kasar Da Ta Dace A Dasa Ta:

Duk wanda zai yi nomanta ya tabbatar da samar,mata da kasa mai kyau.

Yadda Ake Noma Ta Da Rani:

Idan da lokacin nomanta za a nomata, ya kamata wanda zai yi ya tabbatar da samar mata da wadataccen ruwa domin rashin hakan, zai iya hana mata girma da wuri haka, ana kuma bukatar a tanadi kayan ban ruwa na zamani.

Bukatar Ci Gaba Da Habaka Nomanta:

Idan za ka yi nomanta a shekara daya, musaman don samun riba, ya zama wajibi ka fara shiri a kan lokaci, inda hakan zai ba ka damar samun kasuwancinta.

Hanyar Da Za Ka Tallata Ta A Kasuwa:

Kana iya kaita kasuwa don sayarwa ko kuma a dinga tallanta a kafara yanar Gizo da kuma wallafa ta mujallu. Za ka kuma iya kai ta kasuwa.

Ribar Da Ake Sa Ran Za A Iya Samu A Nomanta

Iadan manominta ya noma kamar mai yawan 400 zuwa yawan 500, zai iya samun riba mai yawa.

Exit mobile version