Connect with us

NOMA

Dabarun Noman Tattasai

Published

on

07084634387 09096984945 NAERLS/ABU ZARIA Samaru Zariya

Gabatrawa

 

Tattasai daya ne daga cikn kayan miya wadanda muke bukatarsu a gidajenmu ko otal-otal da sauran wuraren sayar da abinci. A kan noma shi da damina ko kuma da rani. Ana dasa shi a kan kunya ko fangali. kafin a kai ga dasa shi sai fara yafa shi a cikin komi inda za a raine shi har ya kai minzilin da za tuge shi a kai shi gona a ci gaba da dasa shi kwatya daidai.

 

Zaben wuri

Kasar da ta fi dacewa da noman tattasai ita ce, ita ce kasa mai isasshen taki  wadda ruwa ba ya kwantawa  na tsawon lokaci a kanta. Ana bukatar kasa wadda za ta yi saukin aikatawa

Zaben Iri. An sani cewa akwai tattasai kala biyu; wato, mai yaji da kuma maras yaji mai dan zaki ken an. Yana da kyau ka tanadi irin da ya fi dacewa da bukatarka, kuma ma fi kusa da kai a karkararku. Idan kuma kana bukatar wani ingantaccen iri ne, to sai ka hanzarta zuwa gidan gona ma fi kusa da kai ko kuma inda ake sayar da ingantaccen iri.

 

Renon Kananan Dashe

Tattasai kamar sauran kayan lambu  shi ma sai an fara rainonsa a cikin komi wanda aka kebe musamman domin yin hakan. Wadansu kuwa sukan yi rainon ne a dan akwaku na katako ko kuma kwano.

Idan za araini tattasai a komi, to sai a shata shi na fadin mita1.3 tsawo kuma akwance kamar mita1.8, ya kamata a yi kaftu mai zurfi kuma abuge bangorin kasar sosai a share tsakuwoyin da kyau. Bayan haka sai a samu takin zamanina kamfa mai lamba NPK 15:15:15, idan an samu takin sai zuba shi daidai gwargwado a cikin kowane komi. daga nan sai a yafa irin tattasan a cikin wannan komi, sai a barbada kasa a kan irin da aka yafa, Daga nan sai a samu shuci ko ganye a rufe shi, yadda zai samu kyakkyawan yanayin da yake bukata wanda kuma shi zai say a tsiro. Za a ci gaba da ba shi ruwa  na ‘yan kwanaki, sannan sai a yaye wannan ciyawa ko gaye da aka rufe shi da shi.

duk da haka za aci gaba da rainonsa  har lokacin da zai isa dashe a tuge shi a kai shi gona ko kuma lambu domin dasawa.

Gyaran fili Ana bukatar manomi ya yi kaftu  kamar mako daya kafin ya yi dashe. Bayan an yi wannan kaftiun sai a samu wadataccen takin gargajiya a watsa awrin ko kuma a samu takin zamani na NPK mai lamba 15:15:15 kimanin buhu 5 zuwa 10 na kowace hekta.

Daga nan kuma sai a shirya kunyoyin da za a dasa shi a kai ko in a bajiya za a da sahib a sai an yi kunya ba. Ma fi yawan lokacin damina ne ake yin kunya saboda ba za a iya sarrafa ruwan da zai zo ba. amma lokacin noman rani da yake ana iya sarrafa ruwan akan dasa shi a cikin komi mai fadi.

 

Lokacin Dashen Tattasai

Ana dasa tattasai bayan shuka ta kai tsawon inci 3 a yi dashen a kan kunya ko a cikin komi za a bayar da fili tsakanin shuka da shuka yadda zai samu hasken ranar da zai yi amfani da shi da kuma wadatacciyar iska.

Tattasai ya fi son takin gargajiya fiye da na zamani, amma idan na gargajiyan bai samu ba ana iya sa masa  takin  zamani. Takin zamanin da tattasai ya fi  bukata shi ne CAN ana sa shi kafin ya fara ‘ya’ya da kuma lokacin da ya fara ‘yaya.

 

Nomansa

Tattasai na bukatar a nome masa haki a kai a kai yadda ba zai dame shi ba wajen ci gaba da yaduwarsa. bayan an nome hakin ana iya shimfida ciyawa a cikin komi ko a kan kunyakan domin zai yi masa maganin zafin rana da kuma samar da lema a kowane lokaci.

Kwari da cuce-cuce.

Tattasai na da saukin kamuwa da cututtuka  ko kwari in an kamnta shi da sauran kayan lambu. Amma kuma an lura da cewa kwarin tumatur na dan bata shi. Babbar cutar da ta fi addabar tattasai ita ce kuturta, wadda maganinta ya shafi yin amfani da kyakkyawan iri nwanada ke jurewa wannan cuta. Duk gindin shukar da kuturta ta kama sai a cire shi kuma arufe kasar. Karancin ruwa na kawowa tattasai wata cuta wadda ke sa ‘ya’yan su rube daga kasa.

Diban Tattasai Ana fara diban tattasai da zarar ya nuna, nunarsa kuwa ita ce ya yi ja, a jikin icensa. Ga koren tattasai kuwa alamar nunar ta sa za a ga yana sheki, wanda bai kosa ba kuma za ji shi yana da taushi in an taba.

 

Abubuwan Amfani A Jikin tattasai

Masu bincike suna cewa tattasai ya kunshi abubuwa da dama masu kara lafiyar jiki irin wadanna abubuwa kuwa su ne BitaminC da BitaminA da Proteins. Haka kuma tattasai ya kunshi wadasu abubuwa da ake kira riboflarine da thiamine da calain da kuma Phosphorni da sauran wasu sinadarai masu muhimmancin gaske wajen kara lafiyar dan’adam.
Advertisement

labarai