Bello Hamza" />

Dabarun Tallata Ra’ayin Siyasa ta Kafafen Sadarwa Na Zamani

A dai-dai lokacin da guguwar gangamin zaben 2019 ke kara turnikewa, kungiyoyin siyasa da sauran masu muradin cin gajiyar harkokin zaben da za a gudanar na ta kokarin tallata manofinsu da ra’ayinsu ga dimbin wadanda suke fatan zasu jefa musu kuri’a, wadanda suke waste a lungunan fadin kasar nan, kafafen sadarwa na zamani (Internet) irinsu Facebook da Tweeter da Whatsup da e-mail da Telegram nada tasirin gaske wajen isar da sako cikin gaggawa kuma ga dimbin jama’a a kan kudi dan kakilan.
Yakin neman zaben daya gudana a shekara 2012 in da shugaban kasar Amurka Barak Obama ya yi matukar cin gajiyar kafafen sadarwa ta intanet wajen isar da sakon manufofinsa musamman ga matasa a fadin kasar Amurka babban darasi ne ga kowa da kowa, daga wannan lokaci ne aka samu canji a harkokin isar da sakon manufofin siyasa kamar yadda muke ganisa a halin yanzu da kuma yadda zai ci gaba da kasancewa a shekaru masu zuwa. Shugaban Amurka mai ci yanzu Donald Trump ya fito da nasa tsarin da dabaru da ya yi amfani dasu wajen cin gajiyar social media don samaun gagarumin nasarar isar da sakon manufofinsa abin da tayi sanadiyyar samun nasarar darewarsa karagar mulkin Amurka duk da karfin jam’iyyar Democrat kuma ita ke kan karagar mulki da kuma farin jinin ‘yar takararsu Hilarry Clinton.

Wani dabara Donal Trump ya yi amfani dasu wajen canza hanyoyin tallata siyasa a Social Media?
Zamu duba wadanna hanyoyin domin fadakar da ‘yan siyasan mu ko zasu dauki darasi, tun farkon takarar Barak Obama ya nuna matukar sha’awarsa wajen amfani da “social networks” abin da ya ba shi alfarman kasancewar shugaban kasa na farko a duniya da ya fara yin amfani da “Twiter” , shekara takwas bayan haka kuwa a yanzu amfani da Twiter ya zama ruwan dare ga ‘yan siysan mu, har abin ya zama kamar dole in har kana bukatar bunkasar harkar siyasar ka.
A kasashen Turai, mun ga yadda ‘yan takara suka dukufa wajen amfani da intanet a yakin neman zabe musamman a zabe na baya-bayan nan daya gudana a kasar Faransa inda dukkan masu fafutukan yakin neman darewa karagar shugabancin kasar suka zama masu amfani da intanet, lamarin Donal Trump shugaban kasar Amurka mai ci yanzu, ya koyar damu cewa, kaidoji da dokoki da kuma tabka kurakorai a halin yanzu suna da nasu wani tasirin wajen bunkasar farin jinin dan siyasa, domin kuwa sakin maganar da yi tayi da kai hari a kan abokan takaransa da kuma wani lokaci zage-zagen daya kan yi su suka sa ya zama dole a rinka maganarsa a kafafen watsa labarai mussamnan na intanet ba tare daya kashe Miliyoyin daloli ba, a bin lura a nan shi ne, kamar Trump ya san abubuwan da za a watsa da kafafen yada labarai na al’ada irinsu Radio da Talabiji da Jarida da kuma kafafe na zamani da aka fi sani da social networks suke bukata ta haka ya zama shi ne yake kasancewa baban labari a kusan dukkan kafafen yada labarai gaba daya, a kaikaice kuma suna tallata shi ne ba tare da ko kwabo ba.
Ya kamata duk wani dan siyasa ya zamana yana da tsari na musamman da zai yi amfani da shi wajen jan hankalin masu jefa kuri’a da tafiyar yakin neman zabensa. Idan muka yi nazarin social media zamu fahinci lallai, lamari na gaggawan tafiya ga mutane masu dimbin yawa kuma cikin dan kankanin lokaci, in har an tsara shi yadda ya kamata za a yi matukar amfana, a halin yanzu amfani da abin da ake kira da “Hashtag Campaigns” a manhajar Twitter shi ne kusan jagora a fagen isar da sako, fiye da sauran kafafen social media da muke dasu a halin yanzu. I dan mutum ya lura zai fahimci cewar, hatta sauran kafaen yada labarai suna amfani da sakonnin Tweets da ke fitowa daga masu amfani da Twitter domin samun labaran da suke watsa wa masu sauraronsu da masu karatunsu. Wannan kadai ya isa yasa dansiyasa ya fara jinjina mahimmancin wannan kafar sadarwar ta Twiter. Ya kamata duk wani dan takara ya mallaki adireshinsa na Twiter ko da ba shi da kansa zai rinka sarfara sakonnin da zasu rinka shiga da fita ba, yana iya aiyyana wani ko wasu daga cikin kwamitin yakin neman zabensa su rinka lura da sakonnin, saboda bayar da amsan daya dace a kuma lokacin daya dace na da mahmmancin gaske domin kaucewa fada wa fushin masu bibiyarka.
Tsare-tsaren gangamin yakin neman zabe da tattaunawa da masu jefa kuri’a duk sun koma fagen sadarwa na social media, tsarin “fibe-party twitter” zai iya maye gurbin tattaunawa da ake yi tsakanin ‘yan takara domin kowa ya bayyana manufofinsa, domin a wannan tsarin dan takara nada ‘yancin ya zabi tambayar da zai amsa, masu amfani da twiter kuma na da daman jefa wa dan takara tambaya ba tare da tambayar ta shiga ta hannun wani ko kuma an tace ta ba, a social media ana samun daman hanyoyin isar da sako da taken jam’iyya da zai isa ga dimbim mutane, misali a kwai “Tweeter storm” wannada kan kasance kamar zangazanga, inda dimbin mutane zasu rinka ambaton wani take da aka yi wa “hashtag”, Obama ya yi amfani da irin wannan hashtag din, na #fourmoreyears bayan jawabin daya gabatar na neman karin wa’adi karo na biyu na mulkin kasar Amurka, wannan hashtag din ne masana ke ganin ta yi sanadiyar cin zabensa.
Wani abu mai mutukar mahimmanci a harkar isar da sakon ra’ayin siyasa ta kafafen social media ya hada da manhajar YouTube, a nan dan siyasa zai iya bube sashi yk yi bayanin manufofinsa da abin da yake fatan cimma in ya samu darewa karagar mulki, a takaice mutum na da daman ya shirya takaitatcen shiri kamar na talabijin ba tare daya bi ta hannun gidan talabijin ba ko masu wallafe-wallafe.
A gida Nijeriya, tuni ‘yan siyasa suka fara cin gajiyar social media wajen cimma manufofin siyasarsu, domin kuwa a zabe sherarar 2015, tsohon shugaban kasa Goodkuck jonathan ya yi amfani matuka da kafafen sadarwa na intanet domin isar da sakonsa ga jama’a, a wannan karon kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya sanar da aniyarsa na neman takarar darewa kujera mulkin kasar nan ne ta shafinsa na Facebook.

Exit mobile version