Abba Ibrahim Wada" />

Dabid Silba Ya yi Ritaya Daga Buga Wa Sipaniya Wasa

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Dabid Silba dan asalin kasar Sipaniya ya bayyana yin ritayarsa daga bugawa kasar ta Sipaniya wasa bayan ya bugawa tawagar wasanni da dama.
Silba, wanda yakoma kungiyar kwallon kafa ta Manchester City daga Balencia ta kasar Sipaniya a shekara ta 2011 ya buga wasanni da dama a Manchester City kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin firimiya guda uku.
Har ila yau dan wasan dan shekara 32 a duniya ya taimakawa Sipaniya wajen lashe kofin duniya a shekara ta 2010 da kuma kofin nahiyar turai na kasashe a shekara ta 2008 da shekara ta 2012 a jere.
“Daina bugawa kasa ta wasa abune mai wahala kuma sai da nayi dogon nazari akan wannan matakin dana dauka a rayuwata saboda haka babu abinda zance da magoya baya sai fatan alheri” in ji Silba
Yaci gaba da cewa “Lashe kofin duniya a shekara ta 2010 shine abun tarihin da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwa sannan kuma da lashe kofin nahiyar turai har sau biyu a jere shima ba karamar nasara bace”
A karshe ya ce yabar tarihin da bazai taba mantawa dashi ba a rayuwarsa kuma bazai taba mantawa da tsohon kociyan kasar ta Sipaniya ba Luis Aragones wanda yafara gayyatarsa a shekara ta 2011.

Exit mobile version