Connect with us

KIWON LAFIYA

Dafin Kudan Zuma Na Kashe Kwayoyin Cuta –Malamin Jami’a  

Published

on

Dakta Mkabwa Manoko na jam’ar Darul Salam dake kasar Tanzania ya bayyana kari da dafin kudan zuma a matsayin wani dafa’i da za iya amfani da shi wajen magance kwayoyin cuta, da kuma warkar da gyambo cikin kankanin lokaci.

 

Manoko shugaban tsangayar kimiyar amfanin gona da kiwon kudan zuma na jami’ar Darul Salam din ya shaida wa manema labarai matsayar sa ne a tattaunawar bayan fage da ta gudana yau bayan kammala taron ApiExpo karo na shida a garin Abuja, yau Laraba.

 

‘Zuma tana samar da abubuwa sosai da suke da matukar amfani a kamfanonin magunguna, daman a abinci da abin sha, zuma tana yin magunguna da dama, ana iya amfani da zuma don warkar da gyambo, ga ta da arha, tana warkar da gyambo cikin kankanin lokaci, sannan bata da illa kamar sauran kwayoyin warkar da cutukka.’ Inji Manoko

 

Malamin jami’ar ya kara da cewa; dafin kudan zuma yana iya magance cutar kanjamau, sannan bashi da illa ga kwayoyin halittar dan adam, yakamata masana su fadada bincike wajen gano hanyoyin da al’umma zata amfana sosai da kiwon kudan zuma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: