Juma’a 2 Ga Sha’aban 1441 (27/3/2020)
Assalamu alaikum barkanmu da Juma’atu babbar rana, a wannan makon, waiwayen kanun labarun namu zai fara da ranar biyu ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Maris, shekarar dubu biyu da ashirin.
- Sun hana mu wutar lantarki tun kusan wayewar garin jiya, haka muka yini jiya, muka kwana, har zuwa yanzun da asubah da nake wannan rubutu ba wuta. Ga zafi ga sauro. Ga kulle ga ba wuta kuma dole talaka ya biya kudin zama a duhu.
- Femi Adeshina ya ce tsarin mulkin shugaban kasa Buhari ba na yawan surutu ko magana ba ne. Tsarinsa na ya sa a yi ne, da barwa duk wanda ya sa aikin cikekken ikon tafiyar da komai. Femi na mayar da martani ne ga masu korafin shugaban kasa Buhari ba ya yawaita jawabi a kan halin da ake ciki na cutar kwaronabairos kamar yadda sauran shugabannin duniya ke ta yi wa jama’arsu.
- Shugaban ‘yan sanda Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce a shirye yake ya yi aiki da rundunar tsaro ta yankin yarbawa wato AMOTEKUN don yakar aikata miyagun laifuka a can yankin. Ya ce ba a dai yarda AMOTEKUN su tsare mutum, ko yanke masa hukunci, ko daukar makami da ire-iren wadannan ayyuka na ‘yan sanda ba. Za dai su iya yi wa jami’an tsaro rakiya zuwa gudanar da aiki, da taimakawa da bayanai na sirri.
- ‘Yan kungiyar Boko Haram na ci gaba da barna, bayan sojojin Nijeriya arba’in da ‘yan kai da suka kashe a jihar Barno, can wuraren Chadi/Cadi sun kashe sojojin Cadi su casa’in da biyu. Sojojin Nijeriya sun kashe dukkan wadanda suka kashe musu soja, da ci gaba da kai hari inda ‘yan kumgiyar ke boye. Su kuma sojojin Cadi sun ce sata gidan barawo rance.
- Cikin masu taimaka wa shugaban kasa Buhari, an gano wani yana da cutar kwaronabairos.
- A jihar Bauci an gano mutum na biyu da ke dauke da cutar kwaronabairos. Sai wani bayani da ke cewa mutum shida sun warke a jihar Legas, kodayake akwai karin wadanda suka harbu da cutar a jihar ta Legas.
- A jihar Kano ba shiga ba fita, ta kasa ko ta sama ko ta ruwa saboda rigakafin cutar kwaronabairos.
- A jihar Kaduna an rufe dukkan kasuwanni da umartar kowa ya zauna a gida ba fita, amma matafiya daga wasu jihohi da za su bi ta titin bayan gari na Namandi Azikiwe, za a barsu su wuce ba wata tsangwama. Da bayani za a raba abinci gida-gida don jama’a su samu abincin da za su ci.
- A jihar Filato wasu ‘yan bindiga ne suka kashe wasu mutum biyar.
- Gwamnatin tarayya na shirin hana tafiye-tafiye a tsakanin gari zuwa gari, ko jiha zuwa jiha a fadin kasar nan, saboda cutar kwaronabairos.
- A shekarar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta kashe fiye da naira biliyan dari biyu da goma sha takwas wajen gyaran wasu matatun kasar nan.
- Hukumar tara kudaden shiga na/ta cikin gida FIRS a takaice, ta sallami wasu manyan daraktocinta.
- Kamfanin BUA ya ba da naira biliyan daya don taimaka wa yaki da cutar kwaronabairos a kasar nan.
- Zuwa yanzun Legas na da mutum arba’in da hudu, babban birnin tarayya Abuja na da mutum goma sha biyu, jihar Ogun na da mutum uku, jihar Ekiti na da mutum daya, Oyo na da mutum daya, Edo na da mutum daya, Bauci na da mutum biyu, Osun/Oshun na da mutum daya, sai jihar Ribas mai mutum daya da ke dauke da cutar kwaronabairos.
- A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito yau da safe, don karanta labarun da na rubuta a dandalina na soshiyal midiya, daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.
Af! Allah Ya mana katangar karfe da wannan cuta, Ya mana maganin duk abin da ke damunmu. Makiya na fili da na boye, munafukai, magulmata, magibata, mahassada, mamugunta, masharranta, maciya amana. Allah Ya Allah. Allah Kai ne Allah. Ka fi mu saninsu, kada Ka ba su nasara a kanmu. In masu shiryuwa ne Ka shirya su, in ba masu shiryiwa ba ne Ka fi mu saninsu, kada Ka ba su sa’a a kanmu, Ka mayar musu da aniyarsu. Ka gaggauta aiko musu da cutar da ta fi kwaronabairos ta gama da su.
Amin Ya Allah. Haba me ake yi da munafuki! Kuna tare yana maka dariya faram-faram da haba-haba da kai, ashe ta ciki na ciki. Allah Ya isa.
Asabar 3 Ga Sha’aban 1441 (28/3/2020)
A asabar, uku ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da takwas ga watan Maris, na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Na ji wasu ma’aikata sun soma korafin hantsi ya soma duban bakin ludayi, yau ashirin da takwas ga wata suna tambayar ina labarin dilin-dilin ne?
- Ana dara ga dare ya yi. Ana kulle masu wutar lantarki sun hana wutar, ga zafi. Mun kwana da wutar amma gaskiya ba ta da karfin da za ta iya juya fanka. Haka muka wayi gari jiya, da yini ba wuta.
- Jiya da yake gwamnatin jihar Kaduna ta sanya doka kowa ya yi zaman kulle, duk gidajen mai da na zaga in dan samu na sa wa a janereta babu. A karshe da na taso aiki karfe bakwai na dare haka na tarar da talakan da a kullum nake tausayinsa, yana sayar da galan daya naira dubu daya da dari biyar. Kaico! Talakan Nijeriya kai ma ba ka yi ba wallahi.
- Talakan dai na fito sallar asubah jiya na tarar ya kwashe mun takalma, sai dai hadin bauta ya sata. Da na ga suna ta kwashe mun takalma a musamman sallar asubah har silifa bai tsira ba, sai na koma ina yin hadin bauta. To da alamu ban tsira ba. Kodayake an ce barawon idan ya je gida ya ga hadin bauta ne zai dawo da shi. Haka nake ta safa da marwa gida da masallaci jiya ko zai dawo da shi shiru.
- Talakawan jihar Kaduna da aka sa kulle sun ce suna nan suna dakon a cika musu alkawarin da aka daukar musu na agaza musu da abinci har gida.
- Sojojin Nijeriya sun ce babu gaskiya a labarin da wasu ke yadawa cewa sojojin da aka kashe musu a harin da kungiyar Boko Haram ta kai musu sun kai arba’in da bakwai. Hukumomin sojan sun ce soja ashirin da bakwai ne aka kashe musu.
- Gwamnatin tarayya ta mayar da sansanonin horas da ‘yan bautar kasa da ke kasar nan, da manyan filayen wasa na kasar nan a matsayin wuraren killace masu fama da lalurar ciwon kwaronabairos.
- Kotun koli ta yi watsi da bukatar da jam’iyyar APC ta gabatar mata, ta neman ta sauya hukuncin da ta yanke a kan zaben gwamnan jihar Zamfara, da kotun ta tabbabar dan jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben. Kotun ta kuma bukaci APC ta biya wadanda ta kai kara naira miliyan biyu.
- Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule, da na jihar Ekiti Kayode sun ce gwajin da aka musu ya nuna ba su dauke da cutar kwaronabairos.
- Zuwa yanzun akwai mutum saba’in da aka gano suna da cutar kwaronabairos a Nijeriya kamar haka: Legas na da 44, Abuja na da 14, Ogun na da 3. Osun/Oshun na da 1, Ekiti na da 1, Oyo na da 3, Bauci na da 2, Edo na da 1, Ribas na da 1.
Af! Annamimanci bai yi ba. Karshen alewa kasa. Karya fure take yi ba ta ‘ya’ya. Komai nisan jifa kasa za ta yo. A dai naba’a don lokaci ne wallahi.
Lahadi 4 Ga Sha’aban 1441 (29/3/2020)
Idan muka dubi lahadi, hudu ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da tara ga watan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Abin ya zo in ji mai tsoron wanka! Gwamnanmu na jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwajin da aka masa ya nuna yana dauke da cutar kwaronabairos. Ya ce babu wata alama da ta bayyana yana da cutar. Ya dai sa an masa gwajin ne, kuma sai ga shi da ita.
- Har ila yau a jihar dai ta Kaduna an kama wasu limamai guda biyu saboda bijirewa dokar hana jam’i.
- A jihar Kano da babban birnin tarayya Abuja, an soma feshi a kasuwanni da wasu unguwanni don rigakafin cutar kwaronabairos.
- Zuwa yanzun an gano mutun casa’in da bakwai da ke dauke da cutar kwaronabairos a Nijeriya, inda jihar Legas ke kan gaba. Sai Babban Birnin Tarayya Abuja, da su jihar Ogun, da Osun, da Ekiti, da Oyo, da Inugu, da Bauchi, da Ribas, da Binuwai da Kaduna.
- Gwamnatin tarayya ta ce babu gaskiya a labarin da wasu ke yadawa cewa za ta tura wa duk dan Nijeriya da ke da asusu a banki naira dubu talatin.
- ‘Yan majalisar zartaswa ta kasa, kowanne ya yi alkawarin ba da gudunmawar rabin albashinsa na watan Maris ga yaki da cutar kwaronabairos.
- Dangote ma ya ba gwamnatin jihar Legas motocin daukar majinyata gudu hudu ganin a can jihar cutar kwarinabairos ta fi kamari.
- Sojoji sun ce sun kai hare-hare ta sama, wasu muhallai na ‘yan kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa.
- Ana ci gaba da fadakarwar cewa rigakafin cutar kwaronabairos, shi ne yawan wanke hannu, da kaucewa yawan kai hannu fuska , irin su hanci, da ido da wuraren baki. Sai nesa-nesa da juna da kaucewa cincirindon jama’a. Fita in ba ta zama dole ba, mutum ya yi zamansa a gida.
- Sun sace wa JAMES BOND bindigogi a Landon.
Af!! Allah Ya ci gaba da mana katangar karfe da cutar kwaronabairos, da duk sauran abubuwan da suka dame mu Amin. Su kuma wadanda suka kamu da cutar da ma sauran cututtuka, Allah Ya ba su lafiya Ya kare sauran dangi Amin.
Af!! Shi fa zindiki yakan dauka kowa ma zindiki ne irinsa. Asharari kan dauka kowa ma asharari ne irinsa. Mazinaci kan dauka kowa ma mazinaci ne irinsa. Jahili kan dauka kowa ma jahili ne irinsa. Dolo kan dauka kowa ma dolo ne irinsa. Shashasha kan dauka kowa ma shashasha ne irinsa. Annamimi kan dauka kowa ma annamimi ne irinsa. Masharranci kan dauka kowa ma masharanci ne irinsa. Wawa kan dauka kowa ma wawa ne irinsa. Munafiki kan dauka kowa ma munafiki ne irinsa. Magibaci kan dauka kowa ma magibaci ne irinsa. Mugu kan dauka kowa ma mugu ne irinsa. Azzalumi kan dauka kowa ma azzalumi ne irinsa. Mahassadi kan dauka kowa ma mahassadi ne irinsa. Tusa dai ba za ta taba iya hura wuta ba. Duniya ce ta ishi kowa riga da wando. Abin da ka shuka komai dadewa shi za ka girba. In sharri, sharri, in hairan, hairan.
Litinin 5 Ga Sha’aban 1441 (30/3/2020)
Muhimman kanun labarun a litinin, biyar ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Wasu na ta cewa an dai kashe bakin tsanya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi na kusan minti ashirin, daga karfe bakwai na yammacin jiya, ta kafofin watsa labaru. A jawabin nasa ya ba da umarnin hana walwala a jihar Legas, da Abuja, da jihar Ogun, na tsawon mako biyu, saboda alamu na nuna cutar kwaronabairos ta fi cin karenta babu babbaka a wadanban wurare. Dokar hana walwalar za ta soma aiki ne daga karfe goma sha daya na yau litinin da daddare. Zuwa yanzun wadanda suka harbu da cutar ta kwaronabairos a kasar nan, da aka gano sun kai dari da goma sha daya. Mutum daya ne ya riga mu gidan gaskiya zuwa yanzun.
Babban shugaban hukumar imigireshan na kasa bakidaya Babandede, ya sanar da cewa gwajin da aka masa ya nuna yana dauke da cutar ta kwaronabairos. Sai kuma makudan kudi da ake ta ba jihar Legas don yaki da cutar. Kudi na baya-bayan nan wata naira biliyan daya ce, da Modupe da Fulorunsho suka bayar, haka nan shi ma Tinubu ya bayar da gudunmawar naira miliyan dari biyu. Dangote ya ba jihar Kano gado dari shida na jinyar masu ciwon kwaronabairos.
- Yau biyar ga watan Sha’aban, da ke nuna azumin watan Ramadan saura kwana ashirin da hudu ko da biyar. Na ji kuwa wasu na ta ba da shawarar a tashi da azumi yau litinin, na rokon Allah Ya mana maganin wannan cuta, ta kwaronabairos.
- A jihar Kaduna a yankin Birnin Gwari, jiya kwana bakwai kenan da wasu kidinafas suka yi kidinafin wasu matan aure, suna nan ana ta cinikin sako su har yanzun. A jihar Zamfara kuwa dakaru sun kashe ‘yan bindiga tara, suka ceto mutum goma sha biyu da ke hannunsu.
- Nepa/Nefa fa sun dan yi kokari tsakanin jiya da shekaranjiya. Suna dan barin wutar ana kwana da ita.
- Yau talatin ga wata, na ji wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya na cewa har yanzun fa ba su ji dilin-dilin ba. Wasu kuma na ta korafin ba dilin-dilin, ariyas kuma shiru.
- Isra’ila ta soma kwashe ‘yan kasarta da ke Abuja da Legas saboda tsoron cutar kwaronabairos.
Af! Godiya ta musamman ga Sumaiya Ibrahim ta BBC Media Action, wacce bacin/ba don ita ba, watakila da ba a ga rubutuna na yau da asubah ba, ko a daidai wannan lokaci. Wannan ke nuna akwai ‘yar kwakwar da akan ci wani lokaci kafin in iya hado muku labaruna da kuke bibiya kullum.
Af!! Kwace goriba a hannun kuturu ba wahala gareta ba, kai dai an tausaya masa ne aka bar masa yake ta wata fankanar tsiya da hura hanci, da nuna isa. A dai juri zuwa rafi.
Talata 6 Ga Sha’aban 1441 (31/3/2020)
A talata, shida ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhamnad S.A.W. Daidai da talatin da daya ga watan Maris, na shekarar dubu biyu da ashirin.
- Hmm! Jiya na gama yabon NEFA ashe sa ce mun ka manta cewa mu ba ‘yan goyo ba ne. Ta mahaukaci an ce ba ya jifa, sai ya ce kun tuna mun. Ya fara tsintar dutse da hoge yana jifar jama’a. Tunda suka dauke mana wutar jiya da safe, haka muka yini ba wutar jiya, dare ba wutar, muka kwana ba wutar, har yanzun wuraren karfe biyar na asubah da nake wannan rubutu, ba wutar. Wasu na cewa da alamu haka Baba Buhari zai gama mulkinsa bai iya gyara wutar lantarki ba, bai kuma iya hana a dinga karbar kudun zama a duhu a hannun talaka ba. A daidai lokacin da wasu shugabannin kasashen ke dauke wa talakawansu biyan kudin wuta saboda halin da aka shiga na cutar kwaronabairos. Ga kulle, ga zafi, ga sauro, man ma da aka ce an rage kudinsa babu shi. Wannan ko kwaronabairos bai kashe talakan Nijeriya ba, sauran cututtuka irin su sankarau da danginsa sa kashe shi.
- Na ji wasu lauyoyi na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan, a umarnin da ya bayar na hana walwala a jihar Legas, da Abuja da Ogun. Haka nan sun ce su ma gwamnonin da ke kafa dokar hana walwala da rufe kasuwanni da sauransu duk ba su da wannan ikon idan aka yi la’akari da tanade-tanaden da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar nan. Sun ce a mulkin soja ne da ba a aiki da kundin tsarin mulki ake hana irin wannan walwala ba tare da an bi ta majalisun dokoki ba.
- Kungiyar Jama’atul Nasril Islam ta gargadi malaman da ke karyata akwai cutar kwaronabairos, da sauran fatawoyi da suka saba wa koyarwar addinin musulunci.
- Kungiyar kare hakkin bil’Adama SERAP a takaice, ta nemi gwamnati ta fito tana bayani filla-filla kudaden da take kashewa a kan cutar kwaronabairos.
- Mutum na biyu ya mutu a sakamakon cutar kwaronabairos a kasar nan, sai mutum dari da goma sha daya da ke da cutar, ana kuma neman mutum dubu shida da suka yi ma’amala da wadancan mutane dari da goma sha daya.
A mutum dari da goma sha dayan, Legas na da mutum sittin da takwas, Abuja ashirin da daya, Oyo bakwai, Ogun uku, Bauci biyu, Edo biyu, Oshun biyu, Inugu biyu, Binuwai daya, Ekiti daya, Kaduna daya, sai Ribas daya. Mutum biyar sun warke an sallame su. Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya sanar da ya harbu da cutar.
- Sanatoci sun amince za su rage kasafinsu na shekarar 2020, da kuma ba da rabin albashinsu ga yaki da cutar kwaronabairos.
- Kungiyar gwamnoni ta yi taronta na farko kowanne yana daga gida wato TELECONFERENCE MEETING saboda kwaronabairos.
- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta ba da umarnin a samar da Kulorakwin don ci gaba da gwajinsa wajen maganin kwaronabairos.
- Wata cibiya ta binciken da ya shafi lafiya NIMR a takaice, ta ce tana gwajin cutar kwaronabairos kyauta, a samu sakamakon cikin sa’a ashirin da hudu.
- Yau wata talatin da daya, gobe daya ga watan Afrilu, yawancin ma’aikata na tarayya na cewa ba su ga dilin-dilin ba. Kuma an cika shekara daya da soma aiwatar da sabon albashi, wasu na korafin har yanzun ariyas shiru.
- Natanyahu ya sanar da ya harbu da cutar kwaronabairos.
Af! Ana ta tambayata wa ya taba ni nake ta kurman zance ne? To ba wanda ya taba ni. Jinga ce aka ba ni ta ana so a koyi yadda ake irin wannan zance. Jingar ta kare. In kuma akwai wanda ya tsargu don ya yi mun wani abu, to ya sha kuruminsa, na wuce wannan matsayin don ko kallo bai ishe ni ba, ballantana in tsaya ina antaya masa magana ko martani. Don ba a girma ana cin kasa. Ina kuma kyautata zatton an karu.
Laraba 7 Ga Sha’aban 1441 (1/4/2020)
A laraba, bakwai ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Afrilu, shekarar dubu biyu da ashirin.
- Yau daya ga watan Afrilu, ma’aikata na kwalejojin foliteknik, da na jami’o’i da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, da suka yarda suka shiga tsarin IPPIS, na ci gaba da korafin albashin watan jiya shiru, ariyas ma ya shekara daya shiru.
- ‘Yan majalisar wakilai sun sadaukar da albashinsu na wata biyu, Maris da Afrilu ga yaki da cutar kwaronabairos. Su kuwa ‘yan Majalisar Dattawa rabin albashinsu suka sadaukar ga yakin. Sai dai wasu na tsokacin ai albashin nasu ba yawa yake da shi ba. In da gaske suke yi, su sadaukar har da alawus dinsu. Don su ne makudan.
- Hukumar da ke yi wa lamuran lantarki a kasar nan linzami NERC a takaice, ta dakatar da batun karin kudin wutar lantarki da aka tsara zai fara aiki daga yau daya ga watan Afrilu. Ta ce ta tsahirta ne saboda halin da ake ciki na kwaronabairos, sai nan da karshen watan Yuni an ga yadda abubuwa suka kasance. Wasu ‘yan majalisar wakilai sun ma roki gwamnatin tarayya ta dauke wa ‘yan Nijeriya kudin wuta da na ruwa da sauransu saboda an sa talaka kulle, ba inda zai iya zuwa ya samo kudin lantarki. Af! Ga wani can ya ce kudin zama a duhu a duhu dai.
- Gwamnatin tarayya ta ce ta soma tura wa marasa karfi wasu ‘yan kudade na kashewa cikin asusunsu. Kuma a dokar hana walwala ta mako biyu da shugaban kasa ya sa a Abuja, da Legas da Ogun, ban da bankuna.
- A jihar Kaduna, an kama ababen hawa guda dari biyu da biyar, da mutum dari da sittin da biyar da ake zargin sun karya dokar hana fita.
- Zuwa jiya da daddare da na kwanta, bayanin da nake da shi, shi ne mutum dari da talatin da tara ya harbu da cutar kwaronabairos a kasar nan. Tara sun warke har da wanda ya kai cutar jihar Ekiti, ya warke an sallame shi. Mutum biyu ne suka riga mu gidan gaskiya zuwa yanzun sakamakon cutar. Ga kason da jihohin da cutar ta bulla suke da shi:
Legas tamanin da biyu, Abuja ashirin da takwas, Ogun hudu, Oshun biyar, Ekiti daya, Oyo takwas, Bauci biyu, Edo biyu, Ribas daya, Inugu biyu, Binuwai daya sannan Kaduna uku.
- Hukumar sojan Nijeriya ta sauya wa kwamandan rundunar ofireshan lafiya dole wajen aiki zuwa sashen bincike.
- Wadanda ke a gidan gyara hali na Kaduna sun so su yi wani yamutsin sai an sake su, amma an kokarta an shawo kansu.
Af! Ina ta tunanin wadanda aka ce an kama ne a jihar Kaduna saboda karya dokar fita, don na ga gwamnan jihar Legas na cewa jami’an tsaro su dinga lallashin jama’a ne su zauna a gida ko bin dokar hana walwala, ba tursasa musu ko kama su, su garkame ba.
Alhamis 8 Ga Sha’aban 1441 (2/4/2020)
alhamis, takwas ga watan Sha’aban, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Afrilu, shekarar dubu biyi da ashirin.
- Azumin watan Ramadan saura wajen mako uku.
- Yau biyu ga watan Afrilu. Ma’aikatan jami’o’i da na kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya da suka amince suka shiga tsarin nan na IPPIS, na ci gaba da korafin har yau ba dilin-dilin na watan jiya. Suka ce ga kulle, ga zafi, ga ba albashi, ga abinci da sauran muhimman abubuwa na bukatu duk sun kare. Wutar lantarki sai an yi sa’a, ruwan famfo babu, ga rashin lafiya da kuma sauran lalurori da ba a rasawa.
- Gwamnatin tarayya ta kara rage farashin mai. Ta rage daga naira dari da ashirin da biyar, zuwa naira dari da ashirin da uku da kwabo hamsin.
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a fito da hatsi tan dubu saba’in don saukaka halin da aka shiga saboda cutar kwaronabairos.
- A Kwali da ke Abuja an soma raba wa marasa karfi naira dubu biyar ko fiye da haka, daga cikin kudin da ake zargin Abacha ya diba.
- Gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sanarwar sassauta dokar hana walwala, a jiya laraba daga karfe uku na rana zuwa karfe goma sha biyun dare, da kuma yau alhamis. Sanarwar wacce farkon fitowarta jama’a suke ta korafin ba su fahimceta sosai ba, daga bisani aka yi wa turancin gyara ma’anar ta dan fito aka soma fahimtar me ake nufi.
- Zuwa jiya da daddare da na kwanta, bayanin da nake da shi, mutum dari da saba’in da hudu ya harbu da cutar kwaronabairos. Tara sun warke, biyu sun riga mu gidan gaskiya.
Legas na da 91, Abuja 35, Ogun 4,Oshun 14, Ekiti 2, Oyo 8, Bauci 3, Edo 4, Ribas 1, Inugu 3, Binuwai 1 da kuma Kaduna 4.
Af! Mai wadannan lambobin waya ya damfari wata kanwata ya kwashe mata dan kudin da ta ajiye a banki. 09033443766 da 0814492561. Ya ce mata sunansa Lamido Muhammad. Wai zai mata hanyar samun kudin Dangote naira dubu dari uku. Ya nemi ta tura masa naira dubu biyu amma kada ta fada wa kowa, kada jama’a su ji su ce su ma suna so a ba su. Ya aka yi, ya aka yi ya lallabeta, ta tura masa lambar asusunta na ajiya wato SABING ACCOUNT. Allah Ya sa kudin karshe da za ka iya bari a cikin asusun ne ke ciki wato naira dubu biyu ba wasu sulalla.. Shi ne ya kwashe. Sai alat ta gani. Har yana kiranta a waya ta tura cikon sulallan asusunta, domin kudin ya cika naira dubu biyu cif-cif ba gibi. An ce idan mutum ya ce zai ba ka riga, to ka kalli ta wuyansa. Wanda yake yi wa jama’a hanyar naira dubu dari uku na Dangote ne, kuma yake rokon a tura masa naira dubu biyu?