Daga Asabar 5 Zuwa LARABA 9 Ga Watan Muharram 1443

Muharram

Lahadi

Labarin da ya fi daukar hankali a jiya,  shi ne na wasu al’umar musulmi matafiya,  su fiye da mutum 25 mutanen jihar Ondo,  da suka fito daga Bauci za su gida jihar Ondo,  wasu suka tare su a Ɓukur / Rukuba da ke Jos ta Arewa, suka musu kisan gilla.  Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yarda da wannan dabbanci wanda da ma al’adar arnar Jos ce ba tun yau ba.  Shi kuma gwamnan jihar Filato ya fusata ya ce a farauto masa wadannan dabbobin na Jos,  kuma tuni aka ce an kama wasu an sa su cikin keji,  domin ci gaba da barinsu a sake,  na da hadarin gaske ga al’umar musulmi da Hausawa.  Shi ma gwamnan jihar Ondo wanda musulimin jiharsa ne dabbobin na Jos suka tare a hanya suka kashe,  ya roki al’umar jihar Ondo,  da kada su ce za su dau fansa a kan dabbobin Jos da ke zaune a jihar Ondo. Ya ce shi kansa ba zai kyale wannan kisa ya tafi a banza ba,  sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi.  Ba tun yau ba, wasu dabbobin jihar Filato ke tare hanya suna yi wa Hausawa da Musulmi da Fulani kisan gilla.  Ba babba ba karami.  Janar Alkali na cikin wadanda suka tare a hanya suka kashe,  suka jefa motarsa cikin kududdufi kuma har yau shiru ba a ce ga hukuncin da aka yi wa dabbobin ba.  A yanzun dai an dora gangamin wayar da kan jama’ar musulmi da Hausawa da Fulani,  su daina bin yanke ta inda dabbobin nan suke,  idan sun fito Bauci ko Gwambe ko Kaduna ko Abuja.

Sojoji sun sake mika wa Gwamna Zulum na jihar Barno wata daga cikin ‘yan matan Chibok,  Hassana Mohammed da ‘ya’yanta biyu a Gwoza.  A ‘yan kwanakin nan ‘yan matan na Chibok da ke hannun Boko Haram,  har da ‘ya’yan da suka haifa na ‘yan Boko Haram,  suna ta dawowa gida

LITININ

‘Yan Taliban sun kwace Kabul da fadar shugaban kasan Afganistan,  kuma tuni shugaban kasan ya tsere ya bar kasar.  Kungiyar ta ce nan gaba kadan za ta kafa Masarautar Musulunci ta Afganistan.  Amurka ta tura karin dakarunta don kwashe mutanenta daga kasar.

An killace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,  saboda ya yi musabaha da wasu mutanen Ingila da suka harbu da kwaronabairos a tafiyar da ya yi Ingila.

A jihar Jigawa wata gada da ta rifta,  ta yi sanadiyyar mutuwar mutum ashirin da daya.

TALATA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannun a kudurin dokar masana’antar manfetur da aka fi sani da PIB ya zama doka.

Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa ASUU ta soma barazanar komawa yajin aiki muddin gwamnatin tarayya ba ta cika alkawarin da ta daukar musu ba.

Babban Mai Shari’a na Kasa ya rantsar da masu shari’a su biyar,  na kotun daukaka kara ta musulunci.

Gwamnatin Tarayya za ta ci bashin Naira Tiriliyan 5.7 don kasafin shekarar 2022.

A jihar Zamfara ranar Lahadi da daddare,  kidinafas sun jidi mutum goma sha tara,  a kwalejin aikin gona da nazarin kiwo ta Talatar Mafara,  har suka kashe dan sanda daya,  da masu gadi biyu. Shugaban kwalejin wanda sun taɓa kidinafin dinsa wacce hakan ta sa ya sansu,  ya kira su a waya,  sun ce sai an ba su Naira Miliyan 250 kudin fansa.

Af!  Ni fa na daina jin duriyar gwamnana na jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai. Sai Aruwan sai Hadiza.  A matsayina na dan jihar Kaduna ina da hakki idan na ji gwamnana shiru in tambayi ko lafiya.  Ko tafiya zai yi ina da hakki in sani wato a sanar da ni. Da dalilin tafiyar,  da abubuwan da yake yi a can,  da ranar dawowarsa. Yana dawowa ina da hakkin a sanar da ni. Gwamnana ne kuma shugabana da ni na zaɓe shi.  Dole ina da hakki ko jama’a? Shirun da ake yi ba a sanar da ni inda ya je ko halin da yake ciki,  yana sa na kusa da ni su dinga jita-jita da shaci-fadi da rada.

LARABA

Gobe Alhamis idan Allah Ya kai mu, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi taro da manyan hafsoshin tsaro na kasar nan,  don nazartar halin da ake ciki a ɓangaren na tsaro.

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da tayin jinginarwa da ‘yan kasuwa wasu tashoshin jiragen sama na kasar nan.

Gwamnati ta ce ba ‘yan Nijeriya kadai ke cin gajiyar tallafin da take yi wa manfetur ba,  har da masu simogar man zuwa kasar Mali.  Da ke nufin tallafin na kaiwa har Mali,  abin da bai kamata ba.

Gwamnatin Tarayya ta ce in za ta janye tallafin man da take yi a yanzun haka,  za ta yi shi ta yadda ba za a jefa talaka cikin tsananin rayuwa ba.

Wata Kungiya ta Arewa, ta ce ba ta goyi bayan gwamnati ta yi wa ‘yan ta’adda da suka tuba ahuwa ba.

A bikin cika shekara tamanin a duniya da tsohon shugaban mulkin soja,  Ibrahim Badamasi Babangida ya yi jiya,  ya ce jama’a ne ke tunanin ba ya shiri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Amma suna shiri sosai.  Ya kuma amsa tambayar da aka masa ta har yanzun jama’a sun kasa gane ko shi wane ne. Ya ce da sun gane ko shi wane ne da tuni ya sheka lahira.

 

Exit mobile version