Dandalin Ishak Idris Gulbi" />

Daga Juma’a 20 Zuwa Alhamis 26 Ga Almuharram 1441, Bayan Hijira

20 Ga Muharram 1441 (20/9/2019)
Assalamu alaikum barkanmu da juma’atu babbar rana, ashirin ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin ga Satumba, na 2019. Waiwayen kanun labarun namu zai fara da:
1. Jibi lahadi ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi NewYork/Niyok don halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya da za a yi karo na saba’in da hudu, har shi ne na biyar a jerin wadanda aka tsara za su yi jawabi a wajen.
2. Taron Majalisar Tattalin Arziki da aka yi jiya ya bayyana cewa kamfanin mai na kasa NNPC ya yi korafin a watanni uku na farkon shekarar nan an saci man fetur danye, ganga miliyan ashirin da shida da ‘yan kai, da kudinsa ya kai dala biliyan daya da kusan rabi, da in aka ci gaba da haka to kasar nan za ta ci gaba da tabka asara.
3. Majalisar wakilai ta nemi babban bankin Nijeriya CBN ya dan tsahirta da sabon tsarin nan da ya bullo da shi har ya soma aiki shekaranjiya laraba wato CASHLESS POLICY da ya tsara bankuna za su dinga cire wani kaso idan ka je cire kudi har ya kai naira dubu dari biyar ko ajiyewa da dai makamantansu.
4. Kotu ta umarci rufe kamfanin P&ID a kwace duk dukiyarsa a bai wa gwamnatin tarayya saboda amsa laifin ba ya biyan haraji ga kuma danfara a hukuncin nan na kwangila da ya shafi Nijeriya na dala biliyan tara da rabi da ‘yan kai.
5. Sojojin runduna ta daya da ke Kaduna sun ceto wasu mutum takwas da kidinafas suka yi kidinafin a hanyarsu ta Kano zuwa Ilori suka boye su a yankin Chikun da ke jihar Kaduna. Cikin mako biyu karo na biyu ke nan sojojin rundunar na ceto mutane daga hannun kidinafas.
Haka nan sojoji sun yi korafin wata kungiyar mai zaman kanta AAH wato ACTION AGAINST HUNGER na mata zagon kasa a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabashin kasar nan, inda sojojin ke zargin kungiyar ta AAH na ba ‘yan kungiyar Boko Haram abinci da sauran bayanai na soja.
6. A Kano kwastam ake zargin sun yi wa wani dan jarida duka, da yaga masa sitira, da fasa masa rikoda da waya a lokacin da ya je aiki kasuwar da ‘yan kasuwa ke korafin kwastam na matsa musu. Ya ce duk da ya nuna musu katinsa na shaida, sun masa duka. Sai dai kwastam ta ce bai nuna katin nasa da kyau ba ne. Amma za a sasanta. Gidan rediyon da yake yi wa aiki kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, ya ce zai dauki mataki na shari’a.
7. A jihar Binuwai kuwa dan sanda ake zargin ya harbe wani dan acaba ya mutu don ya hana shi naira dari. Sai dai ‘yan sanda sun ce kokuwa ya nemi yi da su har yana kokarin kwace musu bindiga shi ne suka harbe shi ya mutu.
8. A nemi jaridar Leadership Hausa da za ta fito yau juma’a da safe don karanta rubuce-rubucen da na yi a fesbuk daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.
Af! Na lura a ‘yan kwanakin nan kusan kullum sai babbar mota ta fadi ko ta lalace a babban titin baifas da ya taso daga Unguwar Mu’azu zuwa Bakin Ruwa Rigasa, a Kaduna da ke hada cunkoson ababen hawa. In mutum ya yi wasa ta ritsa da shi sai ya kwashe fiye da awa biyu zuwa uku yana cikin cunkoso daga Mu’azu ko daga Sabuwar Fanteka.

21 Ga Muharram 1441 (21/9/2019)
A asabar, ashirin da daya ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da daya ga Satumba na 2019, kuwa:
1. A dai-dai lokacin da wasu ke goyon baya wasu kuma ke tir da rufe kan iyakokin Arewa da gwamnati ta yi, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce rufe bodojin kwalliya na biyan kudin sabulu. Sai dai na ji a shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa da suka yi jiya da daddare, ‘yan Arewa da suka koma shigo da motoci ta Legas saboda rufewar, sun yi korafin ba karamin kabilanci ake nuna musu a Legas din ba, kamar ‘yan Arewa ba ‘yan Nijeriya ba ne.
2. Nijeriya na shirin zuwa Bankin Duniya ciwo bashin dala biliyan biyu da rabi da ‘yan kai.
3. An raba naira biliyan dari bakwai da ashirin na watan Agusta tsakanin gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi, da ke nuna an kusan jin dilin-dilin.
4. Shugaban Majalisar Wakilai Gbajabiamila ya nuna matukar bacin ransa da bayyana cewa zai je ya ga shugaban kasa Buhari da kansa ba sako ba, a kan ya kira shugabannin tsaro na kasar nan su yi taro a kan matsalar tsaro, shugaban ‘yan sanda, da na DSS da sauransu kowa ya je amma shugabannin sojoji, na tsaro gabadaya, da na sama da na kasa da na ruwa sai suka aike da wakilai, su suka ki zuwa. Saboda haka ya dage taron sai litinin.
5. ‘Yan sanda a jihar Ribas sun yi nasarar kama mutumin da ya kware wajen kai mata otel ya kashe su. Ya ce tabbas shi ya kashe mata bakwai cikin takwas da aka ce an kashe. Da suka tambaye shi dalili sai ya ce haka kawai yake sha’awar ya kai mace hotel ya biya bukatarsa, in ya gama ya kashe ta.
6. Babban bankin Nijeriya ya ba gwamnatin tarayya shawarar ta sayar da kaddarorinta da ke zaman banza ba sa kawo mata ko taro.
Af! Kusan mako na hudu ke nan katin nan da na saya na wuta na naira dubu daya bai kare ba har yanzun. Saboda ba a kawo wutar, kuma ko an kawo ko dai ba karfi, ko ka ga wasu suna da wutar mu ba mu da ita. Kamar yadda na yi bayani kwanakin baya, makwabtana da ba su da irin mitata ta iya-kudinka-iya-shagalinka, ana cutarsu da suke biyan naira dubu biyar zuwa shida zuwa bakwai a karshen wata. Don a zahiri wutar da suke sha a wata ba ta kai ta naira dubu daya ba.

22 Ga Muharram 1441 (22/9/2019)
Kanun labarun a lahadi, ashirin da biyu ga watan Almuharram, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashiin da biyu ga Satumba na 2019, sun kunshi:
1. Gwamnatin tarayya tana tuhumar Sowore wanda ya yi kiran juyin-juya-hali da lafin cin amanar kasa da kuma zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
2. Sojojin sama sun ce sun ci gaba da yin barin wuta a mabuya daban-daban na kungiyar Boko Haran a jihar Barno.
3. Bangaren kula da albarkatun manfetur DPR ya rufe gidajen mai goma sha biyu a Sakkwato da Birnin Kabbi.
4. Kotu ta tabbatar wa da Masari cewa shi ya lashe zaben gwamna na jihar Katsina, a kalubalantar zaben nasa da Lado ya kai.
5. A jihar Oyo an yi kidinafin shugaban kungiyar malaman kwalejojin foliteknik tare da wasu mutum hudu.
6. Samari da zawarawa sun soma tsoron zuwa tadi da daddare a cikin garin Kaduna saboda yadda kidinafas ke yin awon-gaba da saurayi da budurwa, ko bazawari da bazawara in sun sace su suna kan yin tadi, su ce sai an biya naira miliyan ashirin kafin su sako su.
Af! Na tuna wadanda muke karanta katin zabe da su a shirye-shiryen zabi sonka kamar su asuba ta gari da sauransu na gidan rediyon jihar Kaduna a wuraren shekarar 1994 da na fara aiki da rediyon. Ina nufin da zabe na fara kafin daga bisani in koma yin labaru. Akwai su:
Shuaibu Isa Gimi
Ahmed Idris tsohon hakimi
Kasim Shuaibu Bamalli
Haruna Sidi Makarfi
Sani Aliyu Jaji
Sani Shehu
Mahazaru Ahmed
Dalhatu Usman
Yushau Aliyu Zariya rod
Abdulkarim Mohammed
Abubakar Haruna
Habiba Rabiu Mu’azu
Hadiza Suleman
Balaraba Tanko
Rabi Mamman
Maryam Mohammed
Adamu Mohammed Bako
Musa Dandoka Gubuci
Da sauransu.

23 Ga Muharram 1441 (23/9/2019)
A litinin, ashirin da uku ga watan Almuharram, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da uku ga Satumba na 2019, Muhimman kanun labarun su ne:
1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi Newyork/Niyok jiya don halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na 74.
2. Sojoji sun damke wani jigo na kungiyar Boko Haram a Maiduguri.
3. Wasu sun kai hari wani kauye da ke jihar Adamawa, suka kashe mutum biyu, suka ji wa mutum shida rauni.
4. An gano gawar wata babbar sojar ruwa a wata rijiya a Jaji da ke jihar Kaduna.
5. ‘Yan bindiga da suka tuba a jihar Zamfara na ci gaba da mika makamansu.
6. Nijeriya za ta soma sayar da takin zamani ga kasashen waje.
Af! Jiya na lissafo wasu daga cikin wadanda muka yi aiki da su a rediyon jihar Kaduna bangaren gabatar da zabe a 1994, to yau zan waiwayi wasu daga cikin wadanda muka yi aiki da su a NTA Kaduna bangaren labaru a shekarar 1995. Ina fassara labaru da karanta su a NTA da fassara labaru da karanta su duk a lokaci guda a rediyon jihar Kaduna.
1. Adamu Lawal Mijinyawa
2. Sani Gwarzo
3. Aminu Yahya
4. Aminu Is’hak Abbas
5. Anthony Forson
6. Garba Saidu
7. Femi Okeowu
8. Abdullahi Ogirma
9. Amina Lamido
10. Idris Ibrahim Umar
11. Wasilatu Tanko
12. Nafisatu Adeniji
13. Sani Mulumfashi
14. Kajuru
Da sauransu.

24 Ga Muharram 1441 (24/9/2019)
Muhimman kanun labarun a talata, ashirin da hudu ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da hudu ga Satumba na shekarar 2019, sun fara ne da:
1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabi a kan sauyin yanayi a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Niyok.
2. Manyan hafsoshin soja na tsaro sun amsa gayyatar shugaban majalisar wakilai inda suka yi taro na sirri, sai dai an ce shugaban ‘yan sanda da na sojan kasa Tukur Buratai ba su samu damar halarta ba.
3. An rantsar da manyan lauyoyi guda talatin da takwas inda babban mai shari’a Tanko ya jaddada samun ‘yancin kai bangaren kudi, da aiki da hukuncin da kotu ke yankewa.
4. An kori sojoji uku daga aiki a jihar Barno saboda zargin suna da hannu a laifin kidinafin.
5. A jihar Binuwai kidinafas sun yi kidinafin wani jigon jam’iyyar PDP.
6. Za a soma biyan ma’aikatan jihar Kabbi sabon albashi na naira dubu talatin mafi karanci daga wannan watan, kamar na jihar Kaduna da su ma za su shaida daga wannan watan.
Af! Labarin da yake ta karakaina jiya ko’ina shi ne gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya cika alkawarin da ya dauka na idan dansa Abubakar Sadik ya cika shekara shida zai sa shi a makarantar gwamnati. Ya sa shi jiya a makarantar Capital School da ke Malali. Sai dai na ga wasu a fesbuk na cewa me ya sa bai sa shi a L.E.A. Unguwar Sarki ba? Ni dai na ji BBC Hausa ta yi hira da shugaban makarantar a shirinsu na dare, na kuma ji yana shaidawa BBC cewa kudin makarantar naira dubu bakwai ne zangon karatu na farko. Har wanda muke tare da shi a lokacin ban sani ba ko dan PDP ne yake cewa to ai shi ma dansa makarantar kudi yake zuwa kuma naira dubu bakwai yake biya a zangon karatu. Ni dai na lura da ake zantawa da Abubakar Sadik na ji yana zuba turanci ko jakin Ingila albarka.
Af!! Tun jiya da wuraren karfe tara na safe da suka kawo wuta, har yanzun ba su dauke ba, ga ta da karfi. Ko sun dauke ba ta kaiwa awa guda sun dawo da ita. Ayyyuurruurriii NEPA. Af! Ba a saurin yabon dan wane ma? Sai ya girma da yatsunsa. Ko dai za su shigo yanka ne yau?

25 Ga Muharram 1441 (25/9/2019)
A laraba, ashirin da biyar ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyar ga Satumba na 2019.
1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa fatara ce babbar matsalar da ke barazana ga duniya, da kuma kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen kawar da ita. Ya bayyana hakan ne a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a Niyok.
2. Majalisar Dattawa ta bukaci ministan shari’a Malami ya je ya mata bayani a kan hukuncin nan da aka yanke wa Nijeriya na sai ta biya dala biliyan 9.6, wato dala biliyan tara da rabi da ‘yan kai.
3. Majalisar Wakilai za ta binciki dukkan kungiyoyi masu zaman kansu da ke gudanar da aikace-aikacensu a Arewa Maso Gabashin kasar nan.
4. Atiku Abubakar ya garzaya kotun koli a kalubalantar zaben shugban kasa Buhari.
5. Kotu ta ba da umarnin a saki Omosore jagoran juyin-juya-hali da gwamnati ta gurfanar da shi a gaban kotu tana tuhumarsa da laifin cin amanar kasa da zagin shugaban kasa Buhari.
6. Jami’an kwastam sun bindige wasu ‘yan simoga su biyu a Jibiya sun mutu.
7. A jihar Sakkwato an yi kidinafin wani dan kasuwa a karamar hukumar Denge/Shuni
8. Gwamnatin jihar Zamfara ta haramta duk wani taro ko jerin-gwano a jihar.
8. A jihar Ondo an wayi gari an ga shanu talatin da shida a mace a al’umar Ijare, mutuwar da mutanen garin ke dangantawa ga wani fushi da abubuwan da suka gada na bauta suka yi.
9. Da alamu na tuna wa NEPA. Gaskiya jiya ma an yini da wuta, ko an dauke cikin mintoci sun dawo da ita, sai dai mun kwana babu wutar.
Af! Wai a nan Arewa ba mu da manyan lauyoyi irin su Femi Falana ne? Na lura kamar su kadai nake gani suna tsaya wa ‘yan kudu da Arewa sun kankane ko’ina kuma suke samun nasarar shari’a da gwamnati.

26 Ga Muharram 1441 (26/9/2019)
Muhimman kanun labarun a alhamis, ashirin da shida ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. da ya zo dai-dai da ashirin da shida ga Satumba na 2019, sun kunshi:
1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya ce a shirye yake ya cire rigarsa ta kariya don wanke sunansa daga zargi daban-daban da wasu suka dage suna masa. Ya kuma soma daukar matakai shari’a.
2. A yanzun haka shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, da ministan shari’a Malami, da ministan labaru Lai Mohammed, da gwamnan babban bankin Nijeriya da shugaban hukumar EFCC Magu, duk suna Landan suna kokarin nuna damfarar Nijeriya aka yi a hukuncin da kotun Landan ta yanke na P&ID na Nijeriya sai ta biya dala biliyan tara da rabi da ‘yan kai.
3. Femi Falana ya yi korafin duk da sun cika sharuddan sakin Sowore, har zuwa jiya da daddare ba a bi umarnin kotu an sako shi ba.
4. Wasu ‘yan bindiga a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun kashe mutum daya, suka yi kidinafin mutum a kalla goma sha hudu.
5. Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar talata mai zuwa a matsayin ranar hutun waiwayar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya.
6. Shugabannin kwadago sun ce dauke Kiyamo da aka yi daga ma’aikatar Neja Delta zuwa ma’aikatar kwadago na iya saukaka tattaunawarsu a kan sabon albashi da gwamnatin tarayya.
7. Majalisar Dattawa ta yaba da rufe kan iyaka da aka yi, a Majalisar Wakilai har wasu sun yunkura kan sai an yi bincike a kan rufewar, mafi rinjaye suka yi fatali da kudirin.
Af! Da yake ina ambato sunayen wadanda muka yi aiki da su a gidajen rediyo da talabijin yau zan tabo gidan talabijin na jihar Kaduna KSTb.
Ni ne na farko da ya soma karanta labaru na Hausa a tashar KSTb Kaduna. Muhammadu Dantankon Sa’i ne ya fassara mun labarun na karanta shi a wuraren shekarar 1996 da aka bude tashar ta KSTb. Esther Tachio da Hadiza Bayero suka soma karanta labarun turanci. Sai su Jummai Hamza da su Henry Iro Sanda. Mu kuma a Hausa Ibrahim Musa Yusuf, da Daharatu Ahmed Aliyu da Ibrahim Shehu Liman suka biyo bayana. A zamani Felid Sanda, gwamna kuma kanal Lawal Jafaru Isa. Kada a manta da ma na yi labaru a NTA a 1995.
Nan gaba zan kawo sunayen wadanda muka yi aiki da su irin su Abba Ahmed Abdullahi da ke BBC Hausa, da Saidu Adamu tsohon kwamishina da su Abba Zayyan.

Exit mobile version