Dandalin Ishak Idris Gulbi" />

Daga Juma’a 27 Ga Muharram Zuwa 4 Ga Safar 1441, Bayan Hijira

Juma’a 27 Ga Muharram, 1441 (27/9/2019)

Assalamu alaikum barkanmu da juma’atu babbar rana, ashirin da bakwai ga Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da bakwai ga Satumba, na 2019. Waiwayen kanun labarun namu zai fara ne da:

1. Wata kotu a Landan ta yarje wa Nijeriya ta daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke mata na sai ta biya wani kamfani P&ID dala biliyan tara da rabi da ‘yan kai, kudin da in ta biya, kashi ashirin ne cikin dari na kudaden Nijeriya na ajiya na ketare.

2. Da yake na tabo batun kudaden kasashen ketare shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki kasashen duniya su agaza wajen hana satar kudade na gida ana kai wa kasashen ketare. Ya ce a duk shekara ana sace dala biliyan hamsin daga Afirka ana kaiwa kasashen ketare, kudaden da sun isa su bunkasa Afirka. Ya yi rokon ne a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya a Niyok.

3. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya nemi kamfanin gugul/google ya cire faifan bidiyon da ke yawo a intanet da ke zarginsa da damfara ta naira biliyan casa’in ko ya dauki mataki na shari’a, da yi wa sauran ‘yan jarida gargadi.

4. Da yake na tabo batun shari’a kotu ta yi barazanar za ta daure shugaban hukumar SSS in ya ci gaba da bijirewa umarnin da ta bayar na a saki Sowore. Sai dai mai magana da yawun hukumar ya ce Soworen ne bai cika sharuddan sakin nasa ba. Lauyan Sowore Femi Falana ya ce tuni suka cika sharuddan ba sa dai son bin umarnin kotu ne.

5. Gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago na kokarin warware inda suke da takaddama a batun soma biyan ma’aikata sabon albashi.

6. Da yake na tabo batun sabon albashi, gwamnatin jihar Kaduna ta cika alkawari ta soma biyan ma’aikatan jihar Kaduna sabon albashi na naira dubu talatin mafi karanci/kankanta a watan nan.

7. Sojojin sama sun kai hare-hare ta sama sansanin horas da ‘yan kungiyar ISWAP da lalata musu kayan aiki a kusa da tafkin Cadi da ke jihar Barno.

8. Da yake na tabo batun soja, an kama wani soja da ya silale daga fagen daga na yaki da kungiyar Boko Haram ya je yana yi wa wata motar wuiwui rakiya a jihar Jigawa.

9. ‘Yan sanda sun gano wasu manyan kabaruka da kidinafas ke kashe mutane suna bisne su a jihar Binuwai.

10. Da yake na tabo ‘yan sanda a jihar Kaduna ‘yan sanda sun gano wani gida da suke zargin an tsare mutum dari uku ga yunwa ga horo da sunan gyara hali.

11. Ministan sadarwa Dafta Pantami ya kaddamar da lambar wayar kiran agajin gaugawa ko neman agaji a jihar Katsina, da ya ce za a kaddamar a sauran jihohin kasar nan. Ya ce kiran lambar ta 112 kyauta ne. Ya ce tun shekarar 2005 aka yi niyyar samar da wannan tsari ya gagara, sai shi da ya hau cikin kwana talatin ya tabbatar da shi.

12. Da yake na tabo batun sadarwa, a nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a da za ta fito yau da safe don karanta rubuce-rubucena da na yi a fesbuk daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Mu yi juma’a lafiya.

Af! Da yake ina tabo wuraren da na yi aiki na rediyo da talabijin, na yi aiki na shekara daya a babban kamfanin nan na NewAge Network daga 2009 zuwa 2010. Kamfanin da ya yi suna wajen hada shirye-shirye na rediyo da talabijin. Na yi aiki da shugaban kamfanin Ibrahim Buba, da Muhammad Aminu Jika, da Toyin Alabi, da Adama Jafar, da Yusuf Usman, da Malam Ahmad da sauransu.

Asabar 28 Ga Muharram, 1441 (28/9/2019)

A asabar, ashirin da takwas ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da takwas ga Satumba, na 2019. Kanun labarun su ne:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baro Niyok zuwa gida Nijeriya bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.

2. Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN ta ce tana tare da mataimakin shugaban kasa Osinbanjo, a wannan lokaci da suke zargin an tasa shi a gaba da zargin ya wawuri wata naira biliyan casa’in da ake zargin ya karba daga hukumar tara kudaden shiga a lokacin yakin neman zabe.

3. Kotu ta amince a karbe duk wata kaddara da ke da nasaba da tsohuwar shugabar ma’aikata Winifred Oyo-Ita.

4. Sojoji sun dakile wani yunkurin hari da kungiyar Boko Haram ta kai jiya Bale Shware kilomita uku daga Maiduguri, da ke kusa da barikin sojoji na Giwa.

5. ‘Yan sanda na ci gaba da kama kidinafas da suka kashe mutane da dama a jihar Binuwai suka bisne su a manyan ramuka, suka shuka rogo da sauransu a wajen.

6. Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kai wa gwamna Nasir El-Rufai ziyara fadar gwamnati ta Sa Kashim Ibrahim da ke nan Kaduna.

7. A Kadunar an kai mutane dari uku da ‘yan sanda ke zargin an tsare su ana cin zarafinsu da sunan gyara hali sansanin alhazai da ke Mando, bayan an kai su filin wasa na Ranchers Bees, don ci gaba da bincike.

Af! Yau ashirin da takwas ina labarin dilin-dilin ne? Don na ji wasu ma’aikata suna ta wayyo Allah ga hidimar komawar yara makaranta an sha ga dilin-dilin shiru.

Lahadi 29 Ga Muharram, 1441 (29/9/2019)

Muhimman kanun labarun a asubahin lahadi, ashirin da tara ga watan Almuharam, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da tara ga Satumba, na shekarar 2019, su ne:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso gida Nijeriya daga babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ya halarta a Niyok.

2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai ji dadin rahoton da ya samu daga Kaduna na an tsare yara da manya su wajen dari uku da ake zargin cin zarafinsu da sunan gyara hali ba. Ya yaba wa jami’an tsaro da suka ceto yaran. Sai dai wasu mata daga cikin iyayen yaran sun bayyana cewa suna goyon bayan tarbiyyar da ake koyarwa a makarantar shi ya sa ma suka kai ‘ya’yansu.

3. Kwamitin Majalisar Wakilai ya soma rangadin sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Barno.

4. Jami’an imagireshan sun ce sun kama wasu ‘yan kasar Nijar su biyu da makamai a wuraren kan iyakar Katsina.

5. Ana nan ana ci gaba da shirye-shiryen bikin cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kan Nijeriya.

6. An bisne gawar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.

Af! Nepa suna kokari fiye da kwanakin baya, tun dai da ministan lantarki ya zo Kaduna wutar ta dan inganta. Don katin naira dubu daya da na ce yana kai mun wata daya, wani lokaci har wata daya da rabi, to a yanzun kwana shida zuwa bakwai ya kare. Da ke nuna in wutar ta dore a haka duk wata zan sayi katin naira dubu hudu zuwa biyar. Ka ga idan ba ka da irin mitata ta iya-kudinka-iya-shagalinka, Nepa suka kawo maka takardar biyan kudin wuta, ka ga sun sa naira dubu hudu ko biyar, to ka biya ta hakan ka sha, ba cuta ba cutarwa. Amma fa a unguwarmu. In kuwa suka kawo maka naira dubu bakwai ko takwas ka ce kana da ja.

Litinin 1 Ga Safar, 1441 (30/9/2019)

A litinin daya ga watan Safar, shekara ta 1441 bayan hijirar cikamakin annnabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da talatin ga Satumba, na 2019. Kanun labarun sun kunshi:

1. A yanzun haka wuraren karfe hudu da rabi na asubah ana ta ruwan sama. Ruwan da aka soma shi tun jiya da daddare wuraren karfe tara.

2. Sojoji na ankarar da jama’a cewa idan sun ji rugugi na wuta da amon bindiga kada su tsorata, domin hakan na daga cikin bikin cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kan Nijeriya da za a yi gobe talata daya ga watan Oktoba idan Allah Ya kai mu.

3. Majalisar wakilai ta ce za ta bibiyi kudaden da ake hankada wa hukumomin tsaron kasar nan don bincikar hanyoyin da suke bi wajen kashe su.

4. Jami’an hukumar kula da kiyaye hadurra sun kama wani fasinja da bindiga kirar AK47 a jihar Taraba.

5. Kidinafas sun sako mahaifiyar Samson Siasia bayan ta kwashe kwanaki a hannunsu, da biyansu kudin fansa ko ajiyarta. Sai dai an ce wanda ya kai kudin sun rike shi suka sakota, shi ma sai da aka biya nasa sannan aka sako shi amma fa a jihar Bayelsa.

Jama’a labarun ke nan saboda hutu ne na karshen mako labarun kan dan yi karanci.

Af! Me ma zan ce ne ma?
Ai kuwa an ce mun an so a ji famfo a Kinkinau na hucin kawo ruwa jiya wuraren la’asar, bayan kusan shekara daya rabonmu da mu ga ruwan famfo. Saukin abin su ba sa zuwa su ce sai an biya kudin ruwan da ba a sha ba ko ba a kawo ba irin yadda su wa’e suke yi na biyan kudin zama a duhu.

Talata 2 Ga Safar, 1441 (1/10/2019)

A talata, biyu ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da daya ga watan Oktoba, na 2019. Kanun labarun su ne:

1. Yau Nijeriya ke cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kanta, kuma anjima kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi wa ‘yan Nijeriya jawabi kai tsaye ta kafofin watsa/yada labaru. Tuni shugaban Amurka Donald Trump ya aiko wa da shugaban kasa Buhari sakon tayin murnar waiwayowar ranar samun ‘yancin kai.

2. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ce an yi wadataccen tanadi na tsaro don jin dadin bikin ranar ta samun ‘yancin kai.

3. Sojojin runduna ta bakwai da ke jihar Barno sun ce sun kama wani mutum da suke zargin shi ke samar wa ‘yan kungiyar Boko Haram kayan aiki. A dai jihar Barno a Gubio ‘yan kungiyar sun kai farmaki har suka ce sun kashe sojoji da yawa da kwasar ganimar kayan yaki. Sai dai sojoji sun musanta ikirarin na kungiyar, inda suka ce sun kai hari tabbas amma sojojin sun dakile su.

4. Kotu ta bai wa DSS unarnin tsare Sowore.

5. Wasu da suka fusata a Dutse Alhaji da ke Abuja sun kama wasu mutum uku, wata ruwayar ta ce mutum daya, da suke zargi kidinafas ne suka cinna musu wuta suka kone kurmus.

6. Gobe laraba idan Allah Ya kai mu kotu za ta yanke hukunci a shari’ar Ganduje da Abba.

7. Mutanen yankin Arewa maso gabashin kasar nan su wajen dubu arba’in suka gudu Nijar neman mafaka saboda rikice-rikicen yankin.

8. Kidinafas sun sace mutum ashirin a Katsina, suka je Burkina Faso suka sayar da su a matsayin bayi.

Labarun ke nan kuma da ma na yi alkawarin zan kawo muku sunayen wasu daga cikin wadanda muka yi aiki da su a rediyon jihar Kaduna KSMC da talabijin na jihar Kaduna KSTB da Capital TB daga shekarar 1994. Ga su kamar haka sai dai na san na manta wasu:

1.Danladi Dawn, 2.Salisu Makarfi, 3.Joseph Audu, 4.Tijjani Ibrahim, 5.Felid Sanda, 6.Aminu Abubakar, 7.Shu’aibu Abdullahi Makarfi, 8. Farfesa Bashir Muhammad Ali, 9.Hassan Makarfi, 10.Shehu Mohammed, 11.Kabir Bawa, 12. Shehu Sa’i, 13. Bashir Sa’i, 14. Saidu Ismaila Ahmed,, 15.Mohammed Mahmud, 16. Nasiru Sidi Liman, 17.Mairo Adamu, 18. Umar Faruk Ahmed, 19.Umar, Faruk Musa, 20.Zubairu Idris Abdulrauf, 21.Muhammadu Dantankon Sa’i, 22. Muhammad Dantani. 23.Tanimu Ibrahim Albarka, 24.Mahmud Dantsoho 25.Mahmud Barwa 26.brahim Musa Yusuf 27.Stella Bature 28.Husseini Ibrahim Alhaji 29.Yakubu Salihu 30.Rhoda Yakudima 32.Bictoria Duru 33. Maikano Abdullahi 34.Yahaya Abubakar Yero 35. Ahmed Yusuf 36. Lukman Musa 37.Mustapha Ibrahim Gangara 38.Umar Kuyello 39. Abba Ahmed Abdullahi 40.Abubakar Zakari Adamu 41. Balarabe Lawal Zariya 42. Zakari Ahmed 43.Husseni Ibrahim Ahmed 44.Esther Tachio 45.Hadiza Bayero 46.Henry Iro Sanda 47.Eberest Allah Magani 48.Funmi Oni 49.Libinus Otte 50. Bilkisu Ige 51.Bala Turundu 52.Sani Magaga 53.Maumud Sani 54. Daharatu Ahmed Aliyu 55. Jummai Hamza 56. Danbaba Kallamu Hunkuyi 57.Ibrahim Shehu Liman 58.Yusuf Ibrahim Kudan 59.Abdulrazak Yahuza Jere 60.Hajiya Maryam Ibrahim 61.Binta Musa Yusuf 62.Mairo Tahir 63.Zulai Balarabe Musa 64.Ahmed Usman Kidandan 65.Abba Zayyan 66.Bala Dankyang 67. Danlami Bawa Jama’a 68. Maikano Mahmud 69.Aminu TC 70 Akilu Atiku Abubakar 71.Zheroh James 72.Binta Saidu 73.Saidu Adamu 74.Amina Adamu 75. Iliyasu Suleman 78.Amina Mohammed 79. Danladi Zoaka 80. Danjuma Mohammed 81. Daharatu Ahmed Aliyu 82. Zakari Aminu 83. Tamani Yusuf 84. Maryam Maiyanga 85. Ishak Idris Gayan 86.Amina Abba 87. Daniel Duniya 88. Aliyu Suleman 89. Mahmuda 90. Dahiru Iyal 91. Sani Cameraman Zariya 92. Sabo Suleman 93. Sahura Maidoki 94. Husseini Baba 95. Adamu Lawal Mijinyawa 96. Isiyaku Store 97. Mu’azu Durum 98. Aliyu Tahir 99. Ado Tata Rigasa 100. Bulus Kuyop 101 Bitrus 102. Dorathy Abiriyi 103. Peter Yero 104. Raliya Sani 105. Ummulkhair Sani 106. Aminu Lere 107. Saleh Abdullahi Hunkuyi 108. Madam Catherin 109.Zhiporah 110. Peter Gulbi 111. Sani Suleman 112. Sani Ahmed Lere 113. Farida Abubakar 114. Ladi Mairabo 115. Aisha Ibrahim 116. Bashir Ahmed Mayere 116. Abubakar Mayere 117. Mayere Programmes 118. Mukhtar Dan Alhaji 119. Musa Kachacchare 120. Hajara Lawal 121 Yusuf Idris 122.Habiba 123. Aisha Gambo 124. Yusuf Muktar Yusuf 125. Abbas Bamalli 126. Nasiru Yakubu Birnin Yero 127. Ayuba Zubairu 128. Kasim Idris Abdulrauf 129. Zubairu Faruk 130. Ahmed Usman 131. Maria Phil Ario 132. Ibrahin Usman 133. Bara’u Usman Pambegua 134. Abdulrasheed Zangon Aya 135.Saminaka 136. Sa’adatu Abubakar 137. Wahal 138. Aminu Kelechi 139. Salisu Reza 140. Zakari Aliyu 141. Salisu Mashi 142. Andy Gabriel 143. Ambrose Benna Gowon 144. Musa Dan Gwari 145. Hauwa Abdullahi Gambo 146. Gambo Abdullahi 147. Shehu Sport 148. Hajara Newsroom 149. Musa kafinta 150. Musa Marketing 151. Ashafa 152. Kabiru Marketing 153. Isiyaku Chairman 154. Fatima Idris 155. Inusa Kauru 156. Kauru Marketing 157. Madam Dowyaro 158. Zakari Isa 159. Habiba 160 Thabita Bunshak 161. Hajara Attahiru 162. Binta Mazadu 163. Rabi’at Nura 167. Zulaihat Jibrin 168. Safiya Adamu/Samaila Mijinyawa 169. Bashir Haruna 170. Bashir Muhammad 171. Maimuna Abdulrahman 172. Ibrahim Ammani 173. Yusuf Jibrin 174. Shuaibu Isa Gimi 175. Ahmed Idris tsohon hakimi 176. Kasim Shuaibu Bamalli 177. Haruna Sidi Makarfi 178. Sani Aliyu Jaji 179. Sani Shehu 180. Mahazaru Ahmed 181. Dalhatu Usman 182. Yushau Aliyu Zariya rod 183. Abdulkarim Mohammed 184. bubakar Haruna 185. Habiba Rabiu Mu’azu 186. Hadiza Suleman 187. Balaraba Tanko 188. Rabi Mamman 189. Maryam Mohammed 190. Adamu Mohammed Bako 191 Musa Dandoka Gubuci 192. Salamatu Abdullahi 193. Abubakar Gambo 194. Mustapha Idris 195. Usman Yaro (Manu) 196. Mica Shaby 197.Maureem Sheyin 198. Abubakar Umar 199. Salamatu Yakubu 200. Fatima Mohammed 201. Nma Mohammed 202. Umma Nimrod 203. Muhammad Danbala 204. Hafsat Suleman 205. Haruna Nasarawa 206. Kabiru Admin 207. Ramatu Adamu 208. Larai Mohammed 209. Hassana ‘yan biyu 210. Kabir Korau 211. Salisu Abdullahi 212. Hadiza Fate 213. Amina Sanusi 214. Shaifu Na Maigero 215. Ado Bako Danhauya 216. Elizabeth Anche 217. Emmanuel Anche Af na manta ban sa suna na ba!

218.. Is’hak Idris Guibi

Laraba 3 Ga Safar, 1441 (2/10/2019)

Idan muka duba laraba, uku ga watan Safar, shekarar 1441 bagan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da biyu ga watan Oktoba na 2019. Muhimman kanun labarun su ne:

1. Yau shugaban kasa Muhammadu Buhari za shi Afirka ta Kudu don ziyara ta yini a kan hantarar da ‘yan can kasar ke yi wa musamman ‘yan Nijeriya.

2. Fadar shugaban kasa ta ba da tabbacun shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai yi tazarce ko neman tazarce ba, bayan wa’adinsa ya kare.

3. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba gudu ba ja da baya a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da yaki da rashawa, da yaki da masu zambatar jama’a ta intanet, da kashe kudaden da ake samu a ta hanya mai kyau, da kuma sanya kafar wando guda da masu kalamai na haddasa kiyayya. Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa al’umar Nijeriya jiya da safe na cika shekara hamsin da tara da samun ‘yancin kan Nijeriya.

4. An gudanar da faretin bikin samun ‘yancin kai a farfajiyar fadar shugaban kasa da ke Abuja maimakon dandalin Igul/Eagle da aka saba gudanar da bikin. Wasu sun ce an yi hakan ne saboda matsalar tsaro, wasu suka ce an yi hakan ne don rage makudan kudin da za a kashe, ko tsimin kudin bikin maimakon almunbazzarancinsu.

Af! Na kuwa ji kwastam na yi wa masu sayar da motoci a jihar Kaduna dirar-mikiya. A kan batun kudaden fito da sauransu.

Alhamis 4 Ga Safar, 1441 (3/10/2019)

A alhamis,hudu ga watan Safar, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta. Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da uku ga Oktoba na 2019. Muhimman kanun labarun abubuwan da suka auku sun hada da:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Afirka ta Kudu.

2. Kotunan sauraron korafe-korafen zaben gwamnonin jihar Kano, da Sakkwato da Filato sun tabbatar wa Ganduje da Tambuwal da Lalong matsayin wadanda suka lashe zabukan jihohin nasu.

3. Bayan kusan shekara hudu suna kulli-kurciya da Abdulrasheed Maina hukumar DSS ta ce ta kama shi, ta mika wa EFCC shi a wani zargi da ake masa na wawurar wasu biliyoyin naira, zargin da ya sha musantawa da neman a ba shi kariya ya fasa kwai.

4. Gwamnatin tarayya na nan tana shirin maido da harajin bin manyan titunan kasar nan da aka fi sani da Toll Gate.

5. Kungiyoyin kwadago NLC da TUC sun ce sun gaji da gafara-sa ba su ga kaho ba har yau. Saboda haka suka ba gwamnatin tarayya mako guda, wata ruwayar ta ce mako biyu ko dai ta kammala duk wani abin da ta ce ya yi saura na biyan sabon albashi, ko a tafi yajin aiki.

Jama’a mu wayi gari lafiya.

Af! Gaskiya masu manyan motoci na dandana kudarsu musamman a titin baifas na Namandi Azikiwe. Daga Unguwar Mu’azu zuwa Sabuwar Fanteka kusan kullum sai babbar mota ta lalace saboda lalacewar titin, titin ya cunkushe.

Af! Af!! Nepa ta tuna wutar ta koma ‘yar gidan jiya. Babu ita babu dalilinta sai sun ga dama.

Exit mobile version