Daga Kin Gaskiya Sai Bata
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daga Kin Gaskiya Sai Bata

bySulaiman and CMG Hausa
3 years ago
Gaskiya

Yayin da yanayin tattalin arzikin kasashen duniya ke kara fuskantar halin rashin tabbas, kana kasashe da dama na cigaba da fafutukar yadda zasu cike komadar tattalin arzikin dake addabarsu, a hannu guda kuma, wasu daga cikin manyan kasashe masu karfin fada aji ta fuskar tattalin arzikin su ma suna dandana irin tasu kudar.

Koda yake, wasu kasashen suna girbar abinda suka shuka ne a samakon daukar wasu matakai na bisa son zuciyarsu, ko kuma sun dauki matakan a bisa kuskure, ba tare da sun yi dogon tunani mai zurfi gabanin daukar irin wadannan matakai ko kuma yanke irin wannan danyen hukunci ba, wanda galibin wadannan matakai nadama ce ke biyo bayan yankesu, sannan lamarin yayi matukar haifar da mummunan tasiri tare da jefa alummunsu cikin halin ha’ula’i.

Alal misali, a karshen wannan mako, wasu masanan kasar Amurka da dama suna ci gaba da yin kira ga gwamnatin shugaban kasar Amurka Joe Biden, da ta soke harajin da aka sanya a lokacin gwamnatin Trump kan kayayyakin da ake shigo da su daga kasar Sin, inda suka jaddada cewa, kawo karshen yakin ciniki a tsakanin kasashen Sin da Amurka zai yi matukar amfanawa Amurkawa. Anton Bekkerman, wani masanin tattalin arzki a fannin aikin gona ne, kana darakta cibiyar nazarin aikin noma ta jahar New Hampshire ya ce, “lokaci ya yi da ya kamata a fara tunanin yadda za a ci gaba, maimakon kirkiro wani abin da zai mayar da hannun agogo baya,” a cewar masanin, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban sashen nazarin kimiyyar rayuwa da aikin gona a jami’ar New Hampshire ta Amurka.

Ya ce, kara kudaden harajin kwastan ba manufofi ne masu alfanu ba, kamar yadda ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan. Shi ma Vincent Smith, masanin tattalin arziki, kuma shehun malamin jami’ar Montana, ya bayyana a kwanan nan cewa, “Za a iya bayyana takaddamar kasuwancin a matsayin wani babban koma bayan tattalin arziki da gwamnatin Trump ta aiwatar, saboda abin takaici ne da rashin tunani game da hakikanin yadda duniya ke gudana, wanda wasu daga cikin mashawartan tsohon shugaban suka dinga ingiza jagoran kasar na wancan lokaci.” Tun a farkon wannan shekara, wasu alkaluman da sashen ayyukan gona na Amurka ya fitar sun nuna cewa, yakin cinikin da gwamnatin Trump ta assasa, ya jawowa fannin aikin gonar Amurka hasarar dalar Amurka kusan biliyan 27 a cikin shekaru biyun da suka gabata. Ko shakka babu, wannan al’amarin ya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Washingtom, kuma abu mafi muhimmanci shine, ya kamata gwamnatin Biden ta sake tunani, domin ance, “ita gaskiya bata bukatar ado,” kuma “daga kin gaskiya sai bata.” (Ahmad)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Saudiyya Ta Kara Wa Maniyyatan Nijeriya Kwanakin Jigilar Alhazai

Saudiyya Ta Kara Wa Maniyyatan Nijeriya Kwanakin Jigilar Alhazai

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version