Daga Lahadi 16 Zuwa Laraba 19 Ga Watan Rabi’ul Sani 1443

Rabiul

LAHADI

Assalamu Alaikum barkanmu da asubahin Lahadi,  goma sha shida ga watan Rabi’ul Sani,  shekarar 1443 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta,  Annabi Muhammad S. A. W.  Daidai da ashirin da daya ga watan Nuwamba, 2021.

Asusun ba da lamani na duniya IMF, ya ba Nijeriya shawarar ta cire tallafin mai da na wutar lantarki gabadaya da an shiga sabuwar shekarar 2022.

Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF,  ya ce har yanzun akwai ‘yan Nijeriya su miliyan 46 da ke ba-haya a filin Allah ba a makewayi/bayi ba.

Osinbanjo ya bai wa alkalai da lauyoyi shawarar su daina bata lokaci a al’amuran shari’a

Hukumomin sojan Nijeriya sun ce za su ci gaba da yin tsayin daka wajen kare kan iyakokin kasar nan.

Wani hasashe na nuna nan da shekara ta 2050 Nijeriya za ta zama ta hudu a duniya, bangaren yawan jama’a.

Ana nan ana ci gaba da buga gangar Tinubu da ta Yahya Bello ta neman su tsaya takarar shugabancin kasar nan a zabukan 2023.

Ma’aikatan hukumar yada labaru ta Jihar Kaduna KSMC, da aka sallama aiki ba tare da an biya su ko taro ba,  na ci gaba da godon a biya su hakkokinsu.

Ministan aikin gona da raya karkara Dafta Muhammad na nan yana ci gaba da aikin sa kwalta a wasu titunan Kinkinau da ke Jihar Kaduna.

LITININ

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna gamsuwarsa da aikin hanyoyi da gadoji da gwamnatin tarayya ke kan aiwatarwa a yanzun haka, kuma ake ganin aikin a zahiri a sassan kasar nan,  ciki har da aikin tititin Kano zuwa Abuja,  da titin Legas zuwa Ibadan da na East-West.

Kungiyar nan ta SERAP mai rajin kare hakkin bil’Adama, ta kai shugaban kasa Muhammadu Buhari kara kotu,  a kan ya ki wallafa sunayen gafiyoyin da ake zargin sun wawuri wata Tirilyan shida daga shekarar 2000 zuwa 2019 a hukumar raya yankin Neja Delta.

Malaman makarantun firamare da na sakandare da ke yajin aiki na gargadi a Abuja a kan wasu hakkokinsu har da ariyas na sabon albashi,  sun ce ba su janye yajin aikin ba sai jibi Laraba idan Allah Ya kai mu.

Su ma dai ma’aikatan kwalejojin foliteknik,  da na kwalejojin ilimi,  da na jami’o’i na nan har yau ariyas na sabon albashin da sauransu shiru.

Har yanzun akwai sauran daliban Shiroro,  da na Katsina,  da na Yawuri,  da na Zamfara,  da na Yobe,  da na Chibok,  da sauran jama’a daga jihohi daban-daban,  da fannonin rayuwa daban-daban da ke hannun kidinafas.

Shugabannin sojoji da sauransu,  na ci gaba da yin tururuwa zuwa yankin Manga da ke Jihar Taraba,  da sojoji ‘yan tawaye na Kamaru suka je suka yi barna.

Ma’aikatan hukumar yada labaru ta Jihar Kaduna KSMC da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar nan ba tare da an biya su ko taro ba,  na ci gaba da godon a biya su hakkokinsu.

Sojoji da suka yi juyin milki a Sudan sun mayar da Firaiminista na gwamnatin da suka kifar Abdallah Hamdok kan mukaminsa.

TALATA

Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka/Afirka ta Yamma WAEC,  ta kara kudin da dalibai ke biya don rubuta jarabawarta,  daga Naira Dubu 13:950 zuwa Naira Dubu 18. Ta kara Naira Dubu Hudu da ‘yan kai.

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa NECO,  ta fitar da jarabawar ‘yan Kano da ake ta korafin ta rike.

Gwamna Yahya Bello na Jihar Kogi ya nemi hukumar EFCC mai yaki da laifuffuka na kudi da tattalin arziki,  ta ba shi hakuri a kan abin da ta masa a kan wata Naira Biliyan Ashirin da gwamnatin tarayya ta tallafa wa jihohi,  don iya biyan albashi da sauransu,  aka masa kagen ya cinye kudin,  sai ga kudin sun fito daga inda aka boye su babu laifinsa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,  da Shugaban Majalisar Dattawa sun yi kus-kus a fadar shugaban kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta a watan Fabrairu na shekarar da ke shirin kankama.

Naira ta soma jajircewa tana naushin hancin dalar Amurka,  tana koli-koli da dala tana tandarawa da kasa don rama kayen da take ta mata a ‘yan watannin nan.

Kidinafas na hanyar Kaduna zuwa Abuja sun farfado,  suka jidi jama’a,  suka harbi na harbi,  suka kuma kashe wani dan siyasa na Jihar Zamfara Sagir Hamdan wanda ya taba yin takarar gwamna na Jihar.

‘Yan bindiga sun kashe mutun hudu a Katsina.

‘Yan fashin daji na ci gaba da kashe jama’a a sassa daban-daban na Jihar Sakkwato.

Yawancin ma’aikatan Jihar Kaduna,  har da malaman jami’ar Jihar Kaduna KASU,  na korafin watan Oktoba bai kare ba,  wato yau 53 ga watan Oktoba ba dilin-dilin.

LARABA

Lai Mohammed ministan labaru ya ce abubuwan da ke cikin rahoton bincike a kan zanga-zangar tir da halayen ‘yan sandan SARS masu yaki da ‘yan fashi da makami da neman kawo karshensu, wato ENDSARS,  rahoton da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka fallasa abin da ke cikinsa,  babu komai cikinsa in ji Lai illa karya,  da kage,  da tatsuniya,  da shirbici,  da tarihihi da sauransu.

Ministan harkokin cikin gida Rauf ya ce an kaddamar da E-Passport wato samun fasfo ta intanet.

‘Yan Arewa na ci gaba da sukar yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza kawo karshen matsalar tsaro a Arewa. Suka yi zargin ‘yan Arewa sun zama daga a sace su sai a kashe su tamkar dabbobi.

Af!  Yau za a ga labarun ba yawa.  Matsala ce ta wutar lantarki. Rabonmu da wutar tun jiya da safe wuraren karfe 10. Har zuwa yanzun ƙarfe 4 da wasu mintoci na asubah babu wutar babu dalilinta.  Haka talaka ke ci gaba da biyan kudin zama a duhu,  kudi kuma tsugugu.  Za ma a kara kudin na zama a duhu a farkon shekarar mai shirin kankama. Ga tsadar gas na girki.  Kananzir da gawayi da itace suna ta wasan kura da talaka.  Abinci na wuji-wuji da talaka.  Fetur ma an kara masa kudi a kaikace,  amma za a kara masa a hukumance a sabuwar shekara. Kaico ! Talakan Nijeriya musamman na Arewa sai dai addu’a.

 

Exit mobile version