Daga Likita: Yadda Cutar Mashasshara Ke Addabar Kananan Yara (2)

Yara

A takaice dai akwai cututtuka da suke sa jikin mutum ya rika yin zafi. Likita ya ci gaba da bayani a kan tambayar da ke tafe:

Daga kamar wadanne cututtukan ne?

Daga cikin yanayin su cututtukan akwai kamar Tuberculosis wato cutar Tarinfuka shima ya kan sa mashasshara, akwai kuma cizon sauro, akwai kuma cin wani anu’in abinci, wannan yana nufin abincin da yake da sinadaran kwayoyin cuta a ciki. Shi ma zai iya sa mashasshara, ita mashashsara ana nufin cewa zafin jiki daga jikin wanda take kamawa to kwayoyin cutar da suke cikin abinci akan iya samun irin hakan.

Wanne dalili ne ke kawo shi zafin jiki lokacin da yake fama da cutar mashasshara?

Tsananin zafin jiki idan har akwai kwayoyion cuta a jinin mutum to kaga jini ba zai iya aiki ba da sinadaran da suke cikinsa, ba zai yi aiki kamar yadda ake bukata ba. Ba domin komai ba sai don wadansu abubuwan da bai saba dasu ba sun shiga cikinsa. Hakan ba zai iya bada dama shi ya karya garkuwar jiki ba, da na’urorin jiki ba za su samar yin wani aiki ba domin wani abu bako ya shiga cikinsu.  Ta haka sai shi zafin jiki ya fara haurawa, wannan ake nufi da mashsshara ke nan.

Ta ya ya za a iya magance shi zazzabin mashassara?

Akan iya magance cutar mashasshara ta hanyar zuwa asibiti, ko kuma ta hanyar gwaje- gwaje saboda ita ma hanyar ta kasu kashi biyu. Akwai kuma physical examination inda za a fuskanci mutum a tambaye shi ko kuma a duba yanayin mutum da yanayin da yake ciki. Hanyar nan zata iya bada bayanin cewar lalle cewar akwai mashasshara jikin mutum shi ne ta hanyar amfani da Themometer, ita na’urar da take duba yanayin halin da jikin mutum yake ciki. A duba daidaituwarsa ko kuma ya haura ko gazawa,  to don haka idan har aka bi ta wannan hanyar to duba halin da jikinsa yake ciki, za a iya tantancewa ta hanyar physical edamination. Wani abu ne wanda shi Likita ko kuma Nas wadda take aiki a asibiti akwai alamomi wato sign da symptom. Wani darasi da muke koyarwa da ake kira da suna sympamatology, wannan sympamatology cuta da kuma yanayin da take shiga jikin dan Adam, don haka idan hara an tabbatar da alamun, symptom  shi ne abu yake faruwa a jiki.Wannan darasi ne wanda ake koyar da Likita ko Unguwarzoma ko wanda yake Malamin kiwon lafiya ne, a koyar da shi hanyar da zai gane yadda mashasshara take shiga. Sannan na biyu shi Likita idan ya gano wannan alamun cuta da cutarwa to sai ya yi yadda zai fita daga cikin kokwanto, zai aika da ainihin specimen wato jini na jikin dan Adam wanda za a ja, sai a aika laboratory wurin da za a gwada ko gwaji. A tantance saboda ya fita daga cikin kokwanto, domin tabbatarwa, domin akwai wata cutar da take kama da wata.

Exit mobile version