Rabi'atu Sidi Bala" />

Daga Littafin Bakar Guguwa (5)

Gargadi: Labarin nan kagagge ne, ban yi dan cin zarafin wani ko wata ba. Na yi shi ne dan fadakarwa da nishadantarwa, kuma ban yarda wani ko wata ya juya munshi ba ta kowacce siga, dan Allah a kiyaye!

Da sauri ta kai hannu ta dau wayar Najib ne a sanyaye ta latsa wayar ta kai kunne ranta a bace ta tabe baki kadan tace “Hello! Ka kyauta” yana dariya yace “Da me na kyauta gimbiya ta?,  zuciyarta cike da takaici tace “hmm…  Da abinda kayi mana” dariya ya kyakya ce da shi tamkar wanda akaiwa albishir “kin kasa fadan komai sai kuma bata rai kike wai meya faru? Allah sa dai ba wani laifin na k”ara yi ba” ranta har yanzu a bace yake tace “da badda kamannin da kayi” cikin rashin fahimta yace “badda kamani a ina baby na?” mamaki ne ya kara kamata ganin yadda yake magana kamar be san meya aikata ba a hankali tace “wai kana nufin baka san me kayi ba? Ko kuwa kana nufin kace mun zuwan da kayi yanzu ba zan iya gane Kaine ba?” da sauri ya mike daga kwanciyar da yake ya dada gyara zamansa dan yanzu kuma be fahimci ina ta dosa ba, dan besan me take nufi ba “ baby na ina naje kuma?” wani takaicin ne ya kara kamata “bari kaji na fada maka na ruga dana gama gane ko kai waye, ko kana tunanin ni irin ‘yan matan nan ne masu soyayya da samari sama da daya ko kuwa kayi haka ne dan ka gwada soyayyar da nake maka? Kana tunanin ba dan Allah nake sonka ba sai dan abin duniya” ranta a bace ta runka fada masa zafafan kalamai cikin rawar murya ya runka yi mata magana “haba baby wai meya faru ne? Be kamata ki kama ni da laifin da ban

san na aikata ba, ya kamata ki fada mun abinda ya faru” “daga lokacin dana dauki wayarka  na fara gane Kaine ba wani ba ko kana nufin kace mun ba Kaine kazo yanzu ba” mamaki ne ya kara kama shi “wallahi baby ba ni bane” “hmm ni na yarda da kai ashe kai baka yarda da ni ba” marairaicewa yayi “ya kamata ki fahimce ni wallahi nace miki ba ni bane” shuru tayi masa sabida ta kasa yarda da magan ganunsa zuciyarta kadai take saurara idan har ba shi bane taya zai kirata bayan sun rabu kuma taya zai kyalkyale da dariya? Haka taci gaba da wannan tunani kamar me shirin yin kuka ya sake magana “baby na ba zan yi miki karya ba rantsuwa fa nake miki “ ko sauraransa bata yi ba ta jiyo hajjiyarsu na kwala mata kira ta katse wayar ta ajjiye gefe ta futa a guje, tana fitowa falo mahaifinta ta gani zaune kan daya daga cikin kujerun falon da suka kewaye tuni har ya shigo ta durkusa kasa tayi masa sannu da zuwa cikin fara’a da walwala yayin  data danne zuciyarta sabid͠a takaicin da Najib ya saka mata.  Alh. Kabir yace “yauwa ya jikin naki?” tana murmushi tace “Abbah jiki yayi sauki na warware “ dariya Abbah yayi tare da cewa “aifa jiki yayi sauki ga fuska nan tasha kwalliya toh Allah kara lafiya” dariya duk-kaninsu suka yi sannan suka ce “Amin”.  Komawa daki Zarah tayi ta tarrar da Missed calls har biyar tedt message  guda uku nan ta duba taga Najib ne takaici ya kamata ko karanta sakon bata yi ba ta kashe wayar gaba daya ta zauna tunani dole ne taji haushin Najib tunda suke bata taba ganinsa ba yanzu kuma yazo yace ba shi ne yazo ba toh taya kalamansu ya zamo iri daya sunan da yake fada mata taya shi wannan ya sani idan har ba shi ne ba, zuciyarta ce take ta raya mata tayi zaune ta hada kai da gwiwa ba shiri ta tashi ta nufi toilet dan dauro alwalar magriba dan tuni magriba har tayi.

   Can kuwa Hajjiya Usaina sai da ta gama hadawa mijina nata komai a sashin sa yayi wanka yayi sallah ya samu yaci abinci sannan ta zauna kusa da shi dan taba hira suna cikin hira Hajjiya ta kalli mijina nata tayi dariya “akwai abinda ya faru dazu” dago kansa yayi ya kalle ta sosai “ina jinki” “hmm dazu ba ka aiko Nauman ba?” “eh! Meya faru?” hajjiya ta kara gyara zama “bayan da yazo yake tambaya ta Zarah ko tana nan? Nace eh ba tada lafiya sai ya shiga ya duba ta dazu kafin ka dawo kuma ina tunanin shi ne ya dada dawowa,  anya babu wani abu a tsakaninsu kuwa?” Alh. Kabir ya kura wa matarsa idanu sannan yace “Idan har tana son shi shik-kenan zan aura mata shi muddin bata san shi ba zan mata auren dole ba dan ina son ‘yata ta samu kwanciyar hankali duk da cewa mahaifiyarsa ‘yar uwa tace bana son na dauki yarinya ta na hada ta da ‘ya’yanta amma in tana sonsa haka Allah ya tsara ba tsumi babu dabara ba zan hana ba” “Hajjiya tace “Gaskiya ne Allah dai ya zaba mata mafi alkhairi dan yadda na ganta tasha kwalliya ba mamaki tana sonnsa a tunani na sanda ya shiga duba ta kila anan ya fada mata zai dawo” “koma dai mene Allah zaba mata miji na gari “ hajjiya tace “Amin”.

Exit mobile version