Rabiu Ali Indabawa" />

Daga littattafan Hausa (2)

Tare da Rabiu Ali Indabawa

An yi haka ba da dadewa ba, sai ta ga duk kuyangin da suke gewaye da ita da ungo zommomin duk bacci ya kwashe su, mamaki ya kamata, ita ma sai ta ji hankalinta ya gushe. Zuwa jimawa kadan sai ta ji kamar tana gyangyadi ne an dan taba ta, tana farkawa sai ta ga jarirai guda biyu kusa da ita a shimfide cikin wani irin mashimfidi na zinare.

Ta yi sauri ta duba ta ga namiji ne da mace suna ta kuka irin na jarirai, ta daga hannu sama ta yi wa Allah godiya. Sai ta ji muryar kawarta Zeenatuzzaman tana yi mata sallama, ta amsa, “Ina yi maki barka da sauka da fatan kina cikin koshin lafiya.” Uwar gidan Sarki ta ce, “Na sauka lafiya, kuma babu abinda yake damuna.”

Zeenatu ta ce, kamar yadda kika yi min alkawari yanzu zan dauki daya daga cikinsu in tafi da shi, sai ya yi wayo zan dawo da shi, amma na yi alkawari ba zan cutar da shi ba. Kafin uwar gidan sarki ta yi magana sai nemi namjin ta rasa, ta fashe da kuka, daga nan ta debi ruwa a hannunta ta watsawa sauran matan da suke gewaye da ita, duk suka farka, suka ga jaririya kusa da ita, amma kuma ranta a bace.

Suka tambaye ta dalilin bacin ranta, ta kwashe labari ta fada masu. Ai daga nan sai gida ya dauki murna da shewa, har sarki ya sami labari ya shigo da kansa don ya ga abinda aka samu. Da zuwa ta kwashe labari daga farko har karshe, da ta zo wurin bayanin Zeenatuzzaman, Sarki ya tambaye ta wacce haka?

Ta ce “Wata aljana ce da muke kawance da ita.” Sarki ya fusata ya ce; “Saboda me za ki kulla zumunta da wata aljana ba tare da kin sanar da ni ba?” nan ta dinga ba shi hakuri, ya karbi jaririn ya yi masa huduba ya ajiyeya fita cikin bacin rai. Da rananr haihuwar ta zagayo, bayan an idar da Sallar asubahi, aka rada wa yaran suna, namijin aka sa masa Asadulmuluuk a matsayin babba, ita kuma aka sa mata Hamdiyatul’aini, aka ci gaba da biki.

Da aka kammala radin suna ne uwar gidan Sarki tana ta yi fito daga wanka tana shirin yin kwalliya, sai ta ji Zeenatuzzaman ta yi mata sallama ta amsa mata, sannan ta ce; “Ga Hamdiyatul’aini na kawo ta ki ganta ki yi mata addu’a, sannan kuma duk na ji sunayensu, Allah ya raya ta Allah ya bani ikon cika alkawari.

Uwar gidan Sarki ta karbe ta ta sumbance, ta ta yi mata addu’a, ta sake kallonta ta fashe da kuka, daga baya ta mika mata ita. Zeenatuzzaman ta ce, “Ki daina kuka na yi alkawarin ba zan cutar da ita ba, sannan idan lokacin dawo da ya yi zan dawo miki da ita kamar yadda na fada, mu aljanu muna da cika alkawari,”

Uwar gidan Sarki ta ce, “Ya Zeenatu kin san fa babu wanda ya san ranar mutuwasa, yanzu duniyar aljanu cike take da rikice-rikice, ina tsoron kada a kawo maku hari a hallaka ku,ko kuma daya daga cikin ku ya hallaka.” Zeenatuzzamana ta ce, “Bari wannan zancen ki rika fadar abinda yake alkhairi ne ga ‘yarki, ai inda zan kai ta ba wuri ne da mai hadari ba, hasali ma ba a taba kai hari alkarayar ba saboda zaman lafiyar da suke da shi.

Daga nan suka yi sallama ta kunshe Hamdiyatul’aini cikin wani kwanso na zinare an shimfide ta cikin wata lallausar shimfida wadda ta fi atafa laushi, ba ta ajiye ta ko ina ba, sai wata alkaryar mutane inda kawayenta suke zaune.

Ta bayar da ita shayarwa, ta fada masu sunanta, kuma ta fada masu labarinta da yadda aka yi ta rabo ta da gida.  Sannan ta yi alƙawarin duk ranar juma’a za ta riƙa zuwa ziyartar su, kuma idan ta tashi dawo wa za ta dawo mata da kayan da za a riƙa sanya mata na ado har ta girma, ta dauko wasu kaya a daure na jarirai masu kyau ta bayar wadanda za a fara yin amfani da su wurin yi mata ado.

Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kaimu. Muna kara sanar da masu karatu cewa, duk wanda yake da littafin da yake sha’awar  mu rika bugawa a wannan shafi mace ko namiji sai ya tuntube mu a wannan lambar 08069824895

Exit mobile version