Rabiu Ali Indabawa" />

Daga littattafan Hausa (3)

Na’ara ashussa’a daaniyyah wata baiwar Allah ce mai hakuri, kuma tanakaya daga cikin dawayen Zeenatuz-zaman a bangaren Bin Adama, mata ce ga wani mutum manomi, ita ce ta karbi Hamdiyatul’aini don shayarwa, har ta kai matsayin ‘ya mace. Ganin haka ya sa ta rika biyan lada ana koya mata harkokin yaki da sauran abubuwa na bajinta, domin ta san daga Nahiyar da aka dauko ta, amma a boye ake koya mata ba tare da sanin Zeenatuz-zaman ba, saboda a duk sa’ilin da Zeenatu za ta zo sai ta zo mata a suffar mutane, sannan ba ta ta ba yarda an bayyana mata daga inda aka dauko ta ba.

Wani masani akan kabi’un dan Adam da kwarewa wajen bayar da horon yaki, wanda kuma ya halarci yake-yake da dama, wanda ke da rike da makullan Hadeekaturrauhaniyyah tsohuwar fadar babban dogarin Sarki Sulbaanil’usfuur, ana kiransa Nuurul’ainaini, shi ne yake ba ta horo, shi kuma an hakikance cewa in dai ya baka horon yaki, to sai an sanka a wasu sassa na duniya. Bayan an gamsu da horon da ta samu, sai aka mayar da hankali wajen janye hankalinta ga barin bibiyar kawaye na nesa da na kusa don gudun kada wancananka sirri ya bayyana, ta gane su ne iyayen ta ba, saboda wadanda suke rike da ita ba su taba nuna mata ba sune iyayenta ba.

Al’amarin Zeenatuzzaman kenan a gonakin Shahyaalu. Sarki Nuurussabri Al’akabar  mahaifin Asadulmuluuk, ne sadauki, yana da tarin dukiya da dakaru majiya karfi da jarumtaka, kai al’amarin ya wuce kwatance, kai dai ka iya kalonsa daga nesa a marmarce, amma idan ya fito fili, to aikin fa sai jurarre. Adali ne cikin lamarin mulkin da ya ke gudanarwa, ba ka iya jin da kai wani talaka a kasarsa yana kukan yinwa ko abin da ya yi kama da haka. Sa’ilin da Asadulmuluuk ya cika shekaru ishirin da biyar, kamannin mahaifinsa suka fara bayyana a jikinsa, ga kyau kai ka ce shi ya zaba, ga kira irin ta ‘yan mazan jiya ga karfi kamar zaki a jeji, farin jini kuwa kamar an rubuce masa Suratu Yusufa, iya magana ko Hukuba cikin fasihancin kalami wane Imru’ulkaisi, haddar Kur’ani kuwa wane. Hudah-hudah, hakuri kuwa kai ka ce damo wurinsa ya gada. Haka ya taso kowa yana haba-haba da shi. sai ya zama a wannan shekara babansa ya yi kuduri niyyar wata tafiya zuwa kasar da abokinsa ya ke mulki, wato Sarki Ainunnasruddeen Al’askandari, wanda ya ke sarauta a kasar Masar don yin ziyara. Ya aika masa cewa ga shi nan tafe, zai zo ya yi wata guda. ya fadawa ‘yan aiken idan sun je su zauna, domin tafiyar kwanaki tara ce daga Lardin Tanzeemussalaam zuwa can. Bisa al’adarsa idan zai yi irin wannan tafiya mai nisa ya kan bar babban dansa Abdulwahhab wanda ake masa lakabi da Sulkaan, da kuma wazirinsa su rike kasar.

To da ya ke Asadulmuluuk shi ma ya fara girma sai Sarki ya yanke shawara kan ya yi wannan tafiya da shi, lokacin ya zo dai-dai lokacin da Sarakuna manya da kanana ke zuwa don kallon kayan tarihi.

A ranar daya ga watan Almuharram tawagar Sarki ta kama hanya, tawaga ce mai kama da ayarin fatake daga nesa saboda mutum dari da hamsin kacal suke cikin tafiyar, wadda idan yaki za su yi sai su iya gamawa da runduna guda, saboda ko wanne daga cikinsu sadauki ne, kuma dukkaninsu sun halarci yabe-yabe ba daya ba, ba biyu ba.

Ranar tara ga Muharram suka doshi ga kasar Bahrun Nil, misalin lokacin sallar azzuhur, suka samu jama’ar Sarkin sun zo dan tarbar su, bayan sun yi salla suka dora dawakan su cikin kwale-kwale aka ketare da su kogin.

Sun samu garin a cike da Sarakuna wadanda suka zo daga kasashe daban-daban, aka ba su masaukai na alfarma kowa ya je ya ajiye kayansa ya dan huta kafin lokacin sallar la’asar. Sun isa ranar Alhamis baban Asadulmuluuk ya ce; “Idan Allah ya kaimu ranar asabar za su je kallon kayan tarihi, sannan ya umarci Asadulmuluuk lallai a cikin wannan dare ya je ya gaida iyayensa wato yana nufin matan Sarki. Da dare ya yi aka hada shi da wani bawa ya yi masa rakiya, suna cikin tafiya suna hira sai aka zo wata farfajiya wani wuri mai fili da wasu fitilu masu haske, sai bawa nan ya ce; “Ranka ya dade wannan hanyar ita za ka yi ta bi za ta sada ka da wata doguwar rumfa, to wannan rumfar ita ce za ta kai ka har wurin da matan Sarki suke hutawa.”

Asadulmuluuk ya dube shi ya ce; “Bawan Allah kana sane da kalaman su ke fita daga bakin ka kuwa?” “Ina sane da abinda na ke fada mana, ai yana yin gidan ne haka, idan ka yi gaba ba zaka rasa wadda za ta jagorance ka zuwa ciki ba.” Ya sake kallonsa ya ce; “Ba ka tunanin ni bako ne? ni ma fa dan Sarki ne, kuma na san yadda irin gidajenmu suke da sarkakiya, ba ka tsoron kada in bi wata hanya da zan ga wani abu da bai halatta ba, gidan iyaye na fa zan shiga?”  Bawa ya ce; “Ranka ya dade ai irinmu ba ma wuce nan, duk namijin da ka gani a ciki, to tuni an dade da fikiye shi.” Asadulmuluuk ya yi firgigit ya ce; “Fikiya kuma ajikin dan Adam?” bawa ya amsa “kwarai kuwa fikiya, babu a masarautar ku ne?” Asadulmuluuk ya yi shiru zuwa wani lokaci sannan ya ce; “Ka jira ni a masauki na idan fito zan nemeka.”

Exit mobile version