Daga Littattafan Hausa: Asadulmuluk

Tare da Rabi’u Ali Indabawa

Assalamu alaikum muna sanar da masu karatu cewa wannan Jarida za ta riƙa kawo muku labarai daga littattafan Hausa a duk ranar juma’a, tare da ni Rabiu Ali Indabawa.

Littafin da za mu fara gabatar muku da shi shi ne, wani littafi da ya shiga kasuwa nan kusa mai suna “Asadulmuluuk ɗan Sarki Nurussabri Al’akbar” littafi ne da ya ƙunshi rayuwar larabawa, yaƙi, jarumtaka, soyayya mai sarƙaƙiya, abin mamaki da kuma tausayi. Mai karatu idan ka shirya mu je zuwa

 

Shekarar Zakuna

Asadulmuluuk ɗa ne ga Sarki Nuurussabri Al’akbar, wanda suke zaune a Lardin Tanzeemussalaam, wata mani’imciyar alƙaryar larabawa masu hasken jiki da tsananin kyau.

An haife shi a shekarar Zakuna, shekarar da waɗansu Zakuna da adadinsu ya tasamma dubu biyu suka ratsa ta Lardin ba tare da sun taɓa kowa ba. labaru na da da na yanzu, sun sha zuwa da zantukan waɗannan zakuna, wasu sun ce kakansa ne ya ba da labarin faruwar hakan, wasu sun ce ru’uya ya yi aka nuna masa hakan. Wasu kuma suka ce a’a ai dama shi masanin ilmin taurari ne, to a irin tsatsube-tsatsubensa ne aka ya gano cewa, wata shekara za ta zo daga shekarun mulkinsa waɗansu zakuna za su ratso ta ƙasarsa.

Sashin al’ummar ƙasar kuma suka ce, duk wannan ba shi ne sahihin zance ba, yadda lamarin da sha’anin yake, Uwar gidan Sarkin tana da wata aljana da suke ƙawance da ita, to wannan aljana ita ce ta ba ta labari a kan hakan, kuma ta faɗa mata cewa a duk sa’ilin da aka ga waɗannan zakuna sun shigo yankin, to a wannan rana za ta haifi ‘ya’ya biyu.

Ita kuma matar Sarki ta yi mata alƙawarin in har zancenta ya tabbata gaskiya, to za ta ba ta ɗaya daga cikin ‘ya’yan ta tafi da shi, idan ya girma ya yi hankali sai ta dawo mata da shi.

Ranar wata talata sha biyar ga watan Ramadhan, bayan an fito daga sallar Asubahi gari ya yi haske, jama’a suka fara jin gurnani irin na zakuna daga bayan gari. Mutanen da suke fita gonaki da masunta, wasu sun ɗauki fartanyu zuwa gona, ai sai aka ga suna dawowa cikin gari a guje, suna zuwa da labarin ganin waɗancanan ka Zakuna.

Sarki yana cikin gida lokacin fita fa da bai yi ba, amma dole ta sa ya fito don ya gane wa idonsa abin da yake faruwa. Da zance ya tabbata gaskiya, nan da nan ya bayar da umarni akan jarumai su zauna cikin shiri, jama’a kuma su koma cikin gidajensu su kulle su ci gaba da addu’a, sannan ya ja kunnen duk mai ɗauke da makami  ka da ya sake ya kai wa kowacce dabba hari in dai ba dabbobin ne aka ga za su fara ɓarna ba.

Dakaru suka faɗa cikin shiri kai ka ce za su fuskanci wata rundunar yaƙi ne, aka ware sahun gwanaye wajen iya harbi da kibau waɗanda su ne aka bai wa dama da zarar sun ga zakuna sun fara ɓarna to su fara harbi.

Zakuna ba su shigo garin ba sai daidai lokacin Sallar walha, sai gasu nan sun yo jerin gwano suna tafiya cikin nutsuwa, kai ka ce ba zakunan gaske ba ne. Da suka zo daidai tsakiyar gari inda aka kafa tutar, sai suka zauna kamar tsahon rabin sa’a, sannan babbansu ya miƙe tsaye suka ci tafiya, yadda suka shigo lafiya, haka nan suka fita lafiya ba tare da sun taɓa wani ba, bayan sun wuce Sarki ya yi hawa da sauran jama’a suka raka su har can kan iyakar ƙasar.

An haƙiƙance cewa waɗannan zakuna sun kwararo ne daga kudu maso gabashin ƙasar Huraasaana, daga cikin wata zahzah ta wani babban dogarin Sarki Hasanul Basari, wanda yake mulkin ƙasar Huraasaana, dama su kan yi irin wannan jerin gwano duk shekara su fita shan iska, a cewar masana halayyar jinsi, jama’ar gari ma da suka samu labari ma su iya wa  suka fito aka tafi kallo.

Anan gida kuma Uwar gidan Sarki na ta fama da naƙuda, sauran matan Sarki da Kuyangi an gewaye ta ana sauraron saukarta ga Ungo zomomi a wurin, suna cikin wannan hali sai suka ji wuri ya sauya da ƙamshi na soyayyen nama, kamar cewa ana suyar nama ne a yayin bukukuwan Sallah babba. “Kai ƙamshi na ke ji kamar ana suyar nama.” In ji ɗaya daga cikinsu,” “Ni ma na ji.” Wannan kalamin uwar gidan Sarki ne, “Fatan mu dai Allah ya sauke ki lafiya.” In ji ɗaya daga cikinsu.

To jama’a a gafarce mu adadin kalmomin da aka bamu ya cika, za mu ci gaba a mako mai zuwa idan Allah ya kai mu, ma’assalam mun gode.

 

Exit mobile version