Rabiu Ali Indabawa" />

Daga littattafan Hausa

Assalamu alaikun masu karatu, kayataccen littafin nan da muka fara kawo maku na yake-yake da soyayya da jarumtaka, abin tausayi da ban mamaki mai suna Asadulmuluuk, mun dawo daga farkonsa za mu fara, tare da ni Rabiu Ali Indabawa, a sha karatu lafiya.

 

Shekarar zakuna

Asadulmuluuk ɗa ne ga Sarki Nuurussabri Al’akbar, wanda suke zaune a Lardin Tanzeemussalaam, wata mani’imciyar alƙaryar larabawa masu hasken jiki da tsananin kyau.

An haife shi ranar Juma’a sha biyar ga watan Ramadan daidai lokacin walha a shekarar Zakuna, shekarar da waɗansu Zakuna da adadinsu ya tasamma dubu biyu suka ratsa ta Lardin ba tare da sun taɓa kowa ba. Labaru na da da na yanzu, sun sha zuwa da zantukan waɗannan zakuna, wasu sun ce kakansa ne ya ba da labarin faruwar hakan, wasu kuma suka ce ru’uya ya yi aka nuna masa hakan. Wasu kuma suka ce a’a ai dama shi masanin ilmin taurari ne, to a irin tsatsube-tsatsubensa ne aka ce ya gano cewa, wata shekara za ta zo daga shekarun mulkinsa waɗansu zakuna za su ratso ta ƙasarsa.

Sashin al’ummar ƙasar kuma suka ce, duk wannan ba shi ne sahihin zance ba, yadda lamarin da sha’anin yake shi ne, Uwar gidan Sarkin tana da wata aljana da suke ƙawance da ita a boye, to wannan aljana ita ce ta ba ta labari a kan hakan, kuma ta faɗa mata cewa a duk sa’ilin da aka ga waɗannan zakuna sun shigo yankin, to a wannan rana za ta haifi ‘ya’ya biyu.

Ranar wata Juma’a sha biyar ga watan Ramadhan, bayan an fito daga sallar Asubahi gari ya yi haske, jama’a suka fara jin gurnani irin na zakuna daga bayan gari.

Mutanen da suke fita gonaki da masunta, wasu sun ɗauki fartanyu zuwa gona, wasu kuma dauke da sanhuna, sai aka ga suna dawowa cikin gari a guje, suna zuwa da labarin ganin waɗancanan ka Zakuna. Sarki yana cikin gida lokacin fita fada bai yi ba, amma dole ta sa ya fito don ya gane wa idonsa abin da yake faruwa.

Da zance ya tabbata gaskiya, nan da nan ya bayar da umarni akan jarumai su zauna cikin shiri, jama’a kuma su koma cikin gidajensu su kulle kofofi su ci gaba da addu’a, sannan ya ja kunnen duk mai ɗauke da makami  ka da ya sake ya kai wa kowacce dabba hari in dai ba dabbobin ne aka ga za su fara ɓarna ba.

Dakaru suka faɗa cikin shiri kai ka ce za su fuskanci wata rundunar yaƙi ne, aka ware sahun gwanaye wajen iya harbi da kibau waɗanda su ne aka bai wa dama da zarar sun ga zakuna sun fara ɓarna to su fara harbi. Zakuna ba su shigo garin ba sai daf da lokacin Sallar walha, aka ga sun yo jerin gwano suna tafiya cikin nutsuwa, babbansu yana gaba da matarsa a gefensa, ga ‘ya’yansu gudu hudu suna dara, kai ka ce ba zakunan gaske ba ne.

Da suka zo dai-dai tsakiyar gari inda aka kafa tuta, sai babban na su ya daga kai ya yi nishi, duk sai suka tsaya cak, daga baya suka yi wata da’ira suka sanya shi a tsakiya. Nan dai suka zauna kamar tsahon rabin sa’a, ba tare da sun yi ko da wani baban motsi ba. Daga baya babbansu ya sake miƙewa tsaye aka buda masu hanya shi da matarsa da ‘ya’yan suka wuce gaba sauran suka biyo su a baya, yadda suka shigo lafiya, haka nan suka fita lafiya ba tare da sun taɓa kowa ba.

Bayan sun wuce Sarki da sauran ‘yan majalisarsa suna biye da su a baya sannu-sannu suka raka su can kan iyakar gari aka tabbatar sun shiga jeji, daga baya suka dawo gida.

An haƙiƙance cewa waɗannan zakuna sun kwararo ne daga kudu maso gabashin ƙasar Huraasaana, daga cikin wata zahza ta wani babban dogarin Sarki Hasanul Basari, wanda ya ke mulkin ƙasar Huraasaana. Dama tarihi ya nuna su kan yi irin wannan jerin gwano duk bayan shekara goma su fita shan iska, inji masana tarihi, sai dai ba su taba ratsowa ta wannan kasa ba.

A wani bangaren kuma, labari ya zo ingancin cewa wadannan zakuna sun samu horo ne daga gwanaye masu iya horar da dabbobi, don haka ne suke tafiya ba tare da sun cutar da kowa ba, a cewar masana halayyar jinsi. Jama’ar gari ma da suka samu labari ma su iya fita zuwa rakiya suka fito aka tafi tare da su, al’amarin Sarki da zakoki ke nan.

A nan gida kuma Uwar gidan Sarki na ta fama da naƙuda, sauran matan Sarki da kuyangi an gewaye ta ana sauraron saukarta ga Ungo zomomi a wurin suna ta aikinsu, suna cikin wannan hali sai suka ji wuri ya sauya da ƙamshi na soyayyen nama, kamar cewa ana suyar nama ne a yayin bukukuwan Sallah babba.

“Kai ƙamshi na ke ji kamar ana suyar nama.” In ji ɗaya daga cikinsu,” “Ni ma na ji.” In ji uwar gidan Sarki, “ To fatan mu dai Allah ya sauke ki lafiya.” In ji ɗaya daga cikinsu. To jama’a a gafarce mu adadin kalmomin da aka ba mu sun cika, za mu ci gaba a mako mai zuwa idan Allah ya kai mu, ma’assalam mun gode.

Exit mobile version