Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home NAZARI

Daga Na Gaba… Bilkisu Goggo Shehu: Gwarzuwarmu Ta Mako

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in NAZARI
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hajiya Bilkisu Goggo Shehu, haifaffiyar garin Hadeja, ta zama wani madubi kuma abin koyi gun mata kan su jajirce a duk abin da su ka sa gaba. Kamar yadda Hajiya Bilkisu duk da wahalar da ta sha kan ganin tabbatuwar makarantarta, a yau hakan ya zama tarihi. Dutse Standard ta zamo zakaran gwajin dafi a Dutsen Jihar Jigawa.

Hajiya Bilkisu an haife ta a garin Hadeja ta jihar Jigawa a 15 ga watan Janairu 1966 (ranar da a ka kashe tsohon firimiyan jihar Arewa, Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato). Ta yi makarantar firamare ta Kofar Arewa, daga baya ta koma Abdulkadir Memorial duk a garin Hadeja. Ta na aji hudu a ka yi wa mahaifinta sauyin wajen aiki su ka koma Kano, inda a ka sa ta a makarantar firamaren Shekara ta ’yan mata ta kwana. Nan ta yi har aji bakwai.

Bayan ta gama ta shiga makarantar ’yan mata ta Saint Lous da ke Bompai a Kano, inda ta kammala a shekarar 1984. Daga nan ta wuce makarantar share fagen shiga jami’a da ke Kano, CAS, ta yi shekara biyu. Ba ta shiga jami’a ba a wannan shekarar, saboda doguwar jinya da ta kwanta ta wata goma sha takwas. A 1987 ta sami gurbin karatu a jami’ar Bayero, inda ta karanta harshen Turanci ta kuma kammala a 1990.

Bayan Hajiya Bilkisu ta kammala bautar kasa ne ta fara aiki a bankin Union tsahon shekara biyu. Sai ta bar aiki ta koma karatu, ta yi babbar difloma a fannin gudanarwa (Management) daga 1996 zuwa 97. Sai kuma ta yi digiri na biyu (MBA) 1997-98 a jami’ar Bayero.

Bayan ta kammala ta tafi Ingila ta yi wasu kwasa-kwasai a bangaren kasuwanci da gudanarwa (Business and Management). Ta dawo Nijeriya a 2002 ta fara aiki da Nigerian Re-Ensurance Co-Operation, ta yi shekara daya, sai mahaifinta ya koma Ingila da zama tare da su har zuwa lokacin da ya rasu.

Bayan ya rasu su ka dawo gida. Gwamnatin Jigawa ta Alhaji Saminu Turaki a 2003 ta ba ta mai ba wa gwamna shawara ta musamman kan haraji da kudin shiga (Rebenue and Inbestment). Da a ka kuma yin zabe, a ka ba ta mataimakiya ta musamman kan kasuwanci (Commerce) ga gwamna. Duk wadannan mukaman ofishinta na Gumel.

A karshen mulkin Saminu Turaki sai ta bar aikin ta koma aiki da wata kungiya mai zaman kanta, Diamond Debelopment Initiatibe, a karkashin United State African Debelopment Foundation. Ta yi aiki da su na wani lokaci, sai ta katse ta koma digiri na biyu a Bissness and Commercial Law, inda ta kammala a 2009.

Daga nan hankalinta ya fara karkata kan ta bude makaranta. Wannan ya sa ta fara bincike kan abin da ya shafi koyarwa. Ta je ta yi kwas kan Educational Psychology, kafin ta bude makarantar Dutse Standard a babban birnin jihar Jigawa cikin watan Satumba na 2010. Allah Ya sanya wa makarantar albarka, inda ta yi fice kuma ta zama zakaran gwajin dafi.

 

Dalilin bude makaranta

Kishi ya sa ta ji ta na son ta bude makaranta a Dutse duk da ta san in har kudi ko su na ta ke bukata ba Dutse ya dace ta je ba, don ta na zaune a Kano nan ya dace da kasuwanci. Lokacin ta na mashawarciyar gwamna ta musamman sai su ka je Abuja a cikin taro sai wata ’yar Kudu ta fara zolayarsu ba gidaje a Dutse a ina su ke kwana, sannan a Dutse babu Standard Schools (Ta nan ma ta samo sunan makarantarta). Shi ya sa ma mutane ba sa son a turo su aiki Jigawa. Bayan sun dawo sai abin ya tsaya mata har ta fada wa abokanan tafiyata cewa wannan fa kalubale ne a kansu.

Sannan dalili na biyu ba ta taba haihuwa ba don haka ta ga ta ina za ta yi ta ta sadakatul jari’a inda za ta tallafi yara su tashi ta sami ladan ko da ba ta raye? Kafa makaranta shi ne amsar da ta ba wa kanta.

 

Gwagwarmaya

Hajiya Bilkisu ta sha gwagwarmayar rayuwa musamman lokacin da ta yunkuro za ta kafa makarantarta Dutse Standard, inda sai da ta shafe shekara biyu ta na jiran takardar sahalewa daga ofishin kwamishinan ilimi na jihar. Sai dai kullum abinda ta ke fada shi ne, “in ka sa ranka za ka yi abu, to kawai ka yi”.

Sannan su ma wadanda su ke bangaren ilimin a gwamnati lokacin babu wanda ya goyi bayanta; su na fada ma ta kada ta fara. Su na cewa su mutanen garinsu talakawa ne. Don haka ba su yarda a zo a matsanta mu su ba. Nan ma dai sai da a ka kai ruwa rana su ka amince.

Sai a ka zo maganar muhallin da za a yi makaranta, su ka kira kan ta kama haya ta shirya makaranta, sannan su zo su duba idan ta yi a cigaba da karatu ko kuma a dakata, idan ba ta yi mu su ba.

Inda za ta karbi hayar nan ma ya ki karbar kudin shekara daya, sai na shekara biyu, ga tsadar gaske; Naira miliyan daya da rabi a shekara biyu; miliyan uku kenan, ga babu kudin a kasa kuma abin ma kamar caca ne, don ba ka da tabbas ko kudinka za su dawo. Kuma sun fara da aji guda ne na firamare da na nursery da dalibai 58, ga ma’aikata. Don haka bayan kudin haya sai da ta kuma lalubo miliyan biyu, don biyan ma’aikata.

Lokacin da ta bayar da talla sai a ka hau surutan ba hoton makarantar ne ba, wai hoton wata kasa ce ta saka, don ta yi yaudara, amma ina za a iya irin wannan makarantar a Dutse. Wannan ma ya jawo ka-ce na-ce sai da a ka zo a ka gani, don tantancewa.

A shekara ta biyu sai ga dalibai sababbi 98. Babbar matsalar har zuwa lokacin ta na kan haya ne, don haka sai ta nemi filin da za ta gina makarantar. Nan fa abu ya ci tura. Sai da a ka shafe shekara hudu a haya, ga kudin hayar ya karu, saboda a lokacin gidaje biyu ne za su ishi daliban.

A shekara ta hudu ta sayi muhalli da kudinta, sai dai daga baya ta sami filin daga gwamnati, inda ta gina da kudinta.

A bangaren gwamnati ta zama tamkar kishiyarsu; ba goyon baya ko jinjina bare tallafi sai neman laifi da ganin gazawa. Sai da ’yan kungiyar makarantu masu zaman kansu na Jigawa su ka shiga tsakani, amma a wannan gabar ta so ta sare.

 

Taimako

Duk da makarantar kudi ce, Hajiya Bilkisu ta na bayar da gurabe na musamman kyauta ga makwabtanta inda kowanne gida ta dau yaro daya. Sannan ta dauki yara mata daga sansanin ’yan gudun hijira ta ba su gurbi a makarantarta. Haka duk yaron da ya ke makarantarta mahaifinsa ya rasu, to ya na cigaba da karatu kyauta har sai ya karasa.

Ta na cikin kungiyoyi na Jigawa na mata, wadanda su ke taimakawa al’umma. Sannan yawancin taimakonta ya fi ga yara mata, don ta na kishin mata.

 

Dalilan Nasararta

Babban dalilin nasararta it ace, ba ta shiga harkar ba sai da ta san harkar koyarwa sannan ta gane al’ummar Dutse yadda su ke. Don haka ta sa kudin makarantar daidai yadda za su iya biya.

Ba ta taba wasa da hakkin ma’aikata; ko a na hutu ta na biyan malamai cikakken albashi.

Duk malamanta babu mai kasa da NCE. A duk shekara ta na biyan ma’aikatanta sama da miliyan biyu, bayan kyautatawa ta musamman lokacin azumin Ramadan da Kirsimeti. Sannan ba ta da burin sai ta tara wani kudi. Da kanta ta ke ‘scheme’ duk sati, ta ba da abin da za a koyar. Haka ba ta zauna b;a ta na bin ajijuwa har sai an tashi a makarantar, don ganin abinda malaman su ke yi. Sannan ta na bibiyar littattafan daliban. Ta na labe, don ganin me ke faruwa. Sa-idon da ta ke yi ya taimaka kwarai, don ganin komai na tafiya.

 

Burinta

Ta ce burinta ya cika; bude Dutse Standard ya zama abin alfahari ga mutanen Jigawa. Hatta Sarkin Dutse sai da ya jinjina ya ce, ta yi ne don kishin Jigawa, ba don neman kudi ba.

Dutse Standard sunanta ya riga ya yi nisa; dalibanta ko’ina ta na iya bugun kirji da su cewar ba ma a Jigawa ba har a Kano dalibanta sun je gasa kuma sun yi nasara.

Wani burin nata a kawo mata yaro bai san bihim ba, amma a kankanin lokaci ya zamana ya iya. Yaranta daga aji hudu su ke fita, amma duk inda su ka je su su ke yin na daya a ko’ina. Yaranta sun je gasa sun ci na daya a Turanci a lissafi.

Burinta makarantar firamare kadai, ba ta da sha’awar kara sakandire, don kishinta shi ne yaran su sami ginshikin harsashi mai kwari. Ba ta son raba hankalinta, inda a karshe a yi biyu-babu.

A inda ta tsara; burintaa ta yi shekara 20 ta na gudanar da wannan makarantar a lokacin ta na da shekara 65. Idan har ta na raye za ta tattara ta damkawa gwamnati makarantar a matsayin sadakatul jariya, ta koma gefe ta huta.

Ta kara da cewa, “Ina da burin ganin yaran nan sun kammala karatunsu na jami’a lafiya”.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kassu Zurmi: Mashahurin Makadin Maza A Kasar Hausa

Next Post

An Yaba wa Alhazan Jihar Zamfara

RelatedPosts

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga A'isha Muhammad A wanna Mukalar zan yi duba ne...

Lokaci

Muhimmiyar Tsaraba Ga Ma’auratan Jiya Da Na Yau

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Yusuf Kabir Aure yana daya daga cikin abin da...

Maleriya

Yaushe Za A Samar Da Riga-kafin Maleriya A Nijeriya?

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Najeeb Maigatari, A rubutun da ya gabata na dan...

Next Post

An Yaba wa Alhazan Jihar Zamfara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version