Daga Na Gaba… Danladi Haruna: Gwarzonmu Na Mako

Tare Da Bilkisu Yusif Ali  – 08054137080– bilkisuyusuf64@gmail.com

Takaitaccen Tarihinka

Cikakken sunana Zakariyya Haruna wanda ake wa lakabi da Danladi. An haife ni a ranar 12 ga Yuli, 1981 a unguwar Gyadigyadi da ke birnin Kano. Daga baya mun tashi daga unguwar zuwa Hausawa Sabon Titi.

Na yi makarantar firamare ta Gandun Albasa Special Primary School, sai kuma Sakandare ta Sharada. A 2004 na yi karatun karamar Diploma (OND), sai  kuma a 2008 na samu shaidar babbar Diploma (HND) duk a fannin nazarin harkokin kasuwanci (Business Administration) duk a karkashin School Of Management Studies, Kano State Polytechnic. Daga nan na tafi hidimar kasa zuwa jihar Osun a 2009 – 2010. A shekarar 2015 kuma na samu shiga jami’ar Bayero inda na yi karatun PGD a fannin aikin Akanta da harkokin kudi (Postgraduate Diploma in Accounting and Finance).

Yanzu haka ina karatu karkashin kungiyar kwararrun Akantoci ta Nijeriya (ICAN) domin samun lasisin zama kwararren akanta. Ina mataki na karshe (Profesional Lebel). Haka kuma na soma karatun digiri na biyu (MBA with Specialization in Finance) a Budaddiyar Jami’ar Nijeriya (NOU).

Bayan wannan ina da satifiket a fannin koyon rubutun fim da kuma Diploma akan sarrafa kwamfuta.

Ina aiki karkashin hukumar zabe ta kasa (INEC) kuma ina ofishin hukumar da ke jihar Kano a ofishin Babban Sakatare.

 

Yaushe ka fara rubutu?

Na soma rubutu daga karanta littatafai. Kusan ba ni da zabi ga duk littafin da ya zo hannuna ina karanta daga farko har karshe. Wasu labaran idan na karanta sai na ga kamar zan iya rubuta irinsu. Da haka dai na soma jarrabawa kuma har yanzu dai ina kan rubutun daidai gwargwado.

 

Wasu na iya mamakin yadda karatunka ba Hausa ba ne, amma kake rubutu da Hausa?

To sha’awa da kaunar da nake yi wa harshen Hausa ya san a dukufa ga rubuce – rubucena cikin harshen Hausa duk da ban koye ta cikin ajin jami’a ba sai a sakandare kadai. Amma idan kin duba littatafaina da sauran rubuce – rubuce na, nakan jefa wasu al’amura da suka shafi lissafi da kiddidigar kudi. Ko a littafin Tekun Labarai na biyu na sakala wasu lissafe – lissafen da suka danganci kudi da al’amuran tattalin arziki.

 

Wa ye ubangidanka ko jagoranka a duniyar rubutu?

To ni dai duk labarin da na rubuta nakan bai wa manyan marubuta su duba kuma su yi gyararraki tun daga ka’idojin rubutu har zuwa ga zubi da tsarin labarin. Kenan zan iya cewa kusan duk manyan marubutan nan iyayen gijina ne. Sai dai wajibi ne na ambaci sunan Farfesa Ibrahim Malumfashi ta karkashin Makarantar Malam Bambadiya inda muka yi karatu da nazarin labarai wanda ban taba samun jagoranci kamar haka ba. Malam Nasiru G. Ahmad kuwa, duk lokacin da na yi rubutu shi ne lambawan da ke duba min ka’idojin rubutu har kuma na soma koyo yadda ya kamata. Malam Khalid Imam kuwa, yakan duba rubutuna daki – daki ya bani shawarar yadda zan inganta shi ta fuskar bincike da nazari.

 

Wadanne kungiyoyin ka yi?

A halin yanzu ina rike da mukamin sakataren kudi na Kungiyar Marubuta Nijeriya (ANA) reshen jihar Kano. Sannan memba ne a kungiyar Marubutan Hausa (HAF) da kuma Kungiyar Marubutan Labarin Fim (Guild of Scriptwriters).

 

Da rubutu ka dogara?

Rubutu dai sha’awa ce ta sa nake yinsa yau da gobe har na saba, amma ba shi ne ainihin abin da ke kawo cimaka ba, sai dai abin da ba a rasa ba.

 

Wadanne ne rubuce-rubucenka?

Rubuce – rubucen suna da yawa, amma dai wadanda nake ganin sun isa a kira su littafi guda 14 ne, sauran kuma duk guntaye ne. Daga cikinsu guda uku sun fita watau, Tekun Labarai na daya da na biyu da Saura Kiris. Ina cikin shirin fitar da Tekun Labarai na Uku da na Hudu da Ciki da Gaskiya da kuma Barayin Zamani. An kammala aikinsu a kwamfuta, nag aba kadan za a gurza su zuwa littafi.

 

Wadanne kalubalen ka fuskanta a rubutu?

Babban kalubale a rubutu shi ne karancin lokaci da kuma gajen hakuri daga mafi yawan masu bibiyar rubutun. Ga kuma matsalar masu halayyar hankaka. Sau da yawa sai na barnatar da lokuta na yi rubutu, kafin a farga sai kurum na ga wasu sun kwashe sun mayar da shi mallakinsu.

 

Wadanne nasarori ka samu?

Nasarorin na da yawa kwarai, daga ciki kuwa har da albarkacin sanin mutane ciki da wajen kasa ta yadda rubutuna ya shiga wuraren da ban taba shiga ba. Haka nan albarkacin rubutu ina cikin wasu kwamitoci da suka shafi rubutu da dab’i a wajen aikina.

 

Wanne abu ne ba za ka taba mantawa ba da ka samu ta hanyar rubutu?

Kamar yadda na fada a baya, abubuwan na da yawa, na ba zan manta da su ba. Na samu takardun karramawa daga kungiyoyi da daidaikun mutane. Haka kuma na samu damar shiga wurare da dama ta dalilin rubutu.

 

Waye tauraronka a marubuta?

Ina so na ga mutum ya yi rubutu cike da hikima da fasaha. Ina kaunar marubucin da ke da manufa wajen rubutunsa. Kuma ina mamakin marubuci mai iya kare rubutunsa komai rintsi.

 

Wacce shawara gare ka ga marubuta sababbi da ma tsofaffin da su ke ganin sun ajiye alkalami?

Nake ga rubutu jinin jiki yake bi, duk fadI tashin da za a shiga bai kamata marubuci ya ajiye alkalami ba sai dai idan ba domin manufa yake rubutun ba. Sau da dama nakan ji manyan marubuta na cewa rubutu tamkar bahaya yake, matukar baka fitar da shi ba, to kuwa zai zauna cikinka ya zame maka ciwo. Zan so na kira manyan marubutanmu da su ci gaba da rubutun da zai iya dora mu mabiyansu kan gwadaben da za a inganta adabin Hausa ciki da wajen Nijeriya.

 

Exit mobile version