Daga Na Gaba… Ga Wuta Ga Masara: Kalubalen Da Matasa Ke Fuskanta A Makarantun Gaba Da Sakandire (II)

Ci gaba daga makon jiya

Muhalli

Makarantar gaba da sakandire muhalli ne na ka-zo-na-zo, daliban da suke zuwa kowanne ya fito ne daga garuruwa da kabilu masu tunani da tarbiyya da tsarin rayuwa mabambanta. A bayyane take, duk lokacin da aka yi irin wannan gwamatsuwa ta mu’amala, dole wani ya yi tasiri a kan wani. Wannan rayuwa irin ta rashin mafadi ke haifar da zaizayewar tarbiya ga matasa musamman dalibai mata.

Bayan wannan ma, ga matsala ta zaman kuntatawa a dakunan kwanan dalibai da azuzuwa da dakunan gwaje-gwaje ga masu karatun kimiyya. Yawaitar al’umma da yi wa ilimi rikon sakainar kashi daga bangaren gwamnati ya haifar da wannan kalubale.

Bugu da kari, rayuwa a muhalli na makarantun gaba da sakandire tana zama barazana ga tarbiyyar dalibai mata a yayin da suka ci karo da malaman da Aminu Alan Waka ya bayyana su da cewa:

“Wani halinsa kama da halin awakai,

Gun bibiyar mata cikin malumana.”

(Aminu Alan Waka: Wakar Jami’a, Rerawa ta 1)

Wannan babban kalubale ne domin kuwa, tarbiyyar mace, abar riritawa ce domin kyautata nagartar al’umma. Ashe kenan, matsalolin da suka jibanci muhalli sun yi matukar tasiri wajen haifar da kalubalen da matasa ke cin karo da su a makarantun gaba da sakandire.

 

Zuciya

Akan ce zuciya ita ce tamkar injin sarrafa mutum. Galibi kalubalen da dan’adam kan ci karo da su a rayuwarsa suna yin tasiri wajen zame masa cikas ne gwargwadon yadda zuciyarsa ta tunkari lamarin. Shi ya sa masu hikimar magana suka ce, abin da zuciya ta dauka gangar jiki bawa ne. Saboda haka, zuciyar matashi ita kanta kalubale ce gare shi a makarantar gaba da sakandire; zuciya ce take kwadaitar da dalibi ya mai da hankali ga holewa maimakon dagewa wajen yin abin da ya kai shi makaranta; zuciya ke kai matashi ga soyayya da zuwa kulob da fagagen wasanni da sharholiyoyi, a maimakon zuwa aji da laburare da bitar karatu cikin tsara; zuciya ke kai matashiya mace biye wa malamai ko dalibai (na banza) domin kwadayin abin duniya ko kwadayin maki ko kece-sa’a! A takaice, zuciya ke kawar da matashi daga rayuwar zahiri zuwa duniyar mafarkin da ba a farkawa sai an wayi gari an ga shekarun zama a makarantar sun kare. Ga shi babu damar fita, don ba a cika ka’ida ba kuma ba sakamako mai kyau. A nan fa ido zai raina fata. Ashe kuwa zuciya ta zama kalubale ga rayuwar matasa musamman a makarantun gaba da sakandire. Domin kuwa:

“Zuciya takan sa baki ya yi,

Mummunan laffazin da zai ja barna.

 

Zuciya takan sa ido ya yi,

Mummunan kallon da zai ja a yi barna.

 

Zuciya takan sa hannu ya,

Aikata abin da zai ja a yi barna.

 

Zuciya takan sa kafa,

Ta taka har inda za a je a yi barna.

 

Duk wannan yakan faru ne,

Bisa umarnin zuciyar da ta lalace.”

(Abubakar Yarima: Wakar Zuciya)

 

Ina Mafita?

Abubuwan da muka tattauna a wannan takarda suna da bukatar a fara aza masu harsashen nazari ta yadda ba za su kasance labarin Aku ba. Ko kusa ba za mu kalli kalubalen matasa da ido daya ba. A kodayaushe matashi ya kamata ya rika fuskantar kowane kalubale da fahimta biyu; daya irin tasa , daya kuwa ba irin tasa ba, ta magabata. Domin kuwa, dole:

“A nemo manya al’amarin da yai tsawo,

Zaman babban yatsa ko ba ta cin tuwo,

Ta iya bare malmala.”

 

A matsayinka na matashi ka sani, ba ka je makarantar gaba da sakandire don ka yi gayu ba, ko don ka ji dadi ko don ka dauki salon rayuwar da ba taka ba. Ka je ne domin ka samu ilimin da za ka san kanka, ka san al’ummarka domin ka amfanar da kanka, ka amfanar da al’ummarka. Idan kuwa haka ne, shin wace hanya za mu ga rayuwarmu ta amfani al’ummominmu? Ko kuwa burinmu kawai da zarar mun kammala makaranta a saka sunayenmu a jadawalin biyan albashi daga nan sai ritaya? To idan ba a sami aikin ba fa? Idan aikin da aka samu bai isa magance bukatun yau da kullum ba fa? Idan kasar ta shiga wani hali fa? Kaka za  mu yi?

A tawa fahimtar, mafita ita ce mu matasa mu taka rawa gwargwadon takawarmu don ganin mun tunkari duk wasu kalubale da muke cin karo da su a fafutukar gina rayuwarmu da ta al’ummarmu, ba wai sai a zaman makarantun gaba da sakandiren ba. Domin kuwa, shi kalubale tamkar gishiri ne a miyar tuwon da dan’adam yake ci don ya girma ya zamto wane, ko da kuwa bai kasance dan wane ba. A wannan gabar, muna tare da malamin kidi Ibrahim Narambada inda ya ce:

Jagora:Da a ce ku gai da dan mai taru,

:Gara a ce mai taru,

 

Yara: Kwak kashe kihinai,

:Sai shi nasa goranai,

 

G/waka: Na rika ka da girma Audu kanen mai daga,

:Kan da mu san kowa

:Kai mun ka sani Sardauna.

 

Saboda haka, mafita ga ire-iren wadannnan kalubale su ma za mu yi masu fyadar kadanya, kamar yadda aka rattabo su a baya; Dangane da yanayin da dalibi ya taso a ciki musamman abin da ya shafi fandisho, ya dace iyaye su yi duba irin na tsanaki domin tsince tsakuwa cikin hatsi game da irin fandishan da ‘ya’yansu suke samu a bokonce ta hanyar zabi na makarantun firamare managarta da kuma bibiyar yadda fahimtar karatun yaran ke tafiya a kai, a kai. Batutuwan da suka shafi matsi na tattalin arziki kuwa suna bukatar kulawa ta musamman daga gwamnati, ta fuskar garambawul da kuma ba bangaren ilimi kaso mai tsoka da za su magance ko kuma su rage matsalolin da suka shafi yanayin da dalibai suke tasowa a ciki ta fuskar tattalin arziki musamman ‘ya’yan masu karamin karfi. Hakan zai haifar da natsuwa ta fahimtar darussa da kuzarin cin jarabawa ga matasan (dalibai).

Dangane da ginuwar kwakwalwa da bakon harshe kuwa, masana tarihi da walwala da harshe, sun tabbatar da gudummawar harshe ga bunkasar kimiyyar da duniyar mutane ta samu. Mafi yawan kasashen da suka buwaya da kimiyya, da harshensu suke amfani. Idan sun ga wani bukata cikin wani harshe, sai su fassaro shi cikin harshensu na gado, su sa zaren tunaninsu na gado(Bunza, 2012:15). Saboda haka, mafita a wannan haujin it ace gwamnati ta yi duba game da amfani da harshen uwa wajen ilmantar da al’ummarta domin matasanmu su yi gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya masu amfani da harasansu wajen karatu da karantarwa. Ko ba komai masu hikimar magana sun ce zanen aro ba  ya rufe katare.

Bugu da kari, mafita ga kalubalen da suka jibinci muhalli kuwa ya hada da iyaye su tabbatar da sun ba ‘ya’yansu ingantacciyar tarbiyya tun suna kanana, ta yadda idan sun tasa ba za su zama bata gari ba. Hakan zai rage matsalar gurbacewar tarbiyyar matasa wadda cudedeniya irin ta ka-zo-na-zo a muhallan makarantun gaba da sakandire kan haifar. Har ila yau, ita kuma gwamnati ta yawalta gine-gine don wadata dakunan karatu da dakunan kwanan dalibai da sauran gine-ginen da ake bukata domin magance kalubalen muhalli a makarantun gaba da sakandire. Tabbasa yin hakan yana da alfanu domin idan aka kyautata muhalli, to duk al’amarin da zai wakana a muhallin zai fi kyautatuwa. Sa’annan muhalli na kara zama kalubale ne gwargwadon yadda al’umma take kara yawaita.

Daga karshe, batutuwan da suka shafi zuciya kuwa, za a iya samun mafita a game da su ne ta hanyar tsarkake zuciyar, tsarki na hakika ba tsarki da kunun kanwa ba. A koda yaushe matashi ya gina tunaninsa ta hanyar sarrafa zuciyarsa ta yadda za ta dace da aikata abin da zai zame masa mafita a rayuwarsa da ta al’ummarsa. Domin haka, a duk lokacin da zuciyar matashi a makarantar gaba da sakandire ta raya masa kaucewa daga ainahin abin da ya kawo shi makarantar sai ya yi kokarin  kale kalubale domin cinkar abin da ya kai shi. Ga dai shi a makarantar, ga malaman, ga kayan karatun me ya rage? Idan dai ga wuta ga masara, ai sai gasawa kawai.

Alhamdulillahi !

 

Exit mobile version