Daga Ranar Litinin 12 Zuwa Alhamis 15 Ga Watan Shawwal 1442

PRESIDENT BUHARI RECEIVES LIBYAN PRESIDENT MENFI 6A&B. President Muhammadu Buhari receives the President of Libyan Presidential Council H.E Mohammed Al-Menfi during a courtesy visit to the State House Abuja. PHOTO; SUNDAY AGHAEZE.MAY 26TH 2021

LITININ

Yau Litinin, goma sha biyu ga watan Shawwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Mayu, shekarar 2021.

Shugaban Ƙasa Muhamadu Buhari ya amince a soma zaman makoki na kwana uku daga yau, da sauke tutar ƙasar nan ƙasa-ƙasa na tsawon kwanakin, su kuma sojoji an ba su hutun aiki yau, saboda rasuwar janar Ibrahim Attahiru babban hafsan hafsoshin mayaƙan ƙasa na ƙasar nan, da wasu manyan sojojin 10 a haɗarin jirgin sama. Tuni Aisha Buhari ta je wajen iyalan marigayi Attahirun domin yi musu gaisuwar ta’aziyya.

Hukumar NDLEA mai yaƙi da fataken miyagun ƙwayoyi da sha ta Buba Marwa, ta kama wani falken ƙwayoyin a tashar jiragen sama ta Murtala da ke Legas, da ƙwaya ta wajen Naira Biliyan takwas.

Ƙungiyar SERAP mai kare hakkin ɗan Adam da bunƙasa tattalin arziki, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yi bayanin yadda ta yi niyyar kashe Fam miliyan 4.2 da aka karbo daga Ingila da Ibori tsohon gwamnan Delta ya sata ya kai can, da kuma wata Dala Miliyan 700 ita ma da aka ƙwato daga bakin wata riƙaƙƙiyar gafiyar.

A jihar Zamfara wasu ‘yan fashin a babura fiye da ɗari biyu ɗauke da bindigogi, sun kashe mutum fiye da 20, suka ji wa da dama rauni, a Zurmi, da Ƙauran Namoda da Birnin Magaji.

A jihar Binuwai wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 9, kwanaki kaɗan da kashe wasu mutum 7.

A jihar Kaduna sojoji sun ce sun ceto wasu mutane yawanci mata, da aka yi kidinafin a yankin Igabi. Sai yankin Birnin Gwari da mutanen yankin ke ci gaba da ƙorafin kidinafas ke ci gaba da cin karensu babu babbaka. Su kashe na kashewa, su yi kidinafin na kidinafancewa.

Malaman kwalejojin foliteknik, na ci gaba da yajin aiki babu ranar komawa.

Mu wayi gari lafiya. Wasu ma’aikata a jihar Kaduna na ci gaba da ƙorafin albashi na watan jiya shiru. Wasu ma tun na watan shekaranjiya. Sannan na ji wani abokina na tambayar gwamnatin jihar Kaduna, da take ta cewa tana kashe yawancin kuɗin da take samu daga gwamnatin tarayya ga biyan ma’aikata da ba su wuce cikin cokali ba, sauran jama’a kuma da su suka fi yawa su tashi a tutar babu, ba a samun rarar na yi musu aikin komai, to, ina kuɗaɗen shiga da gwamnatin jihar Kaduna take samu fa? Ya kuma yin tambayar basussukan da aka ciyo/ciwo fa? Ya ce a ƙasashen da aka ci gaba ana yin hanyoyi da gada ne da za su kai ma’aikata ma’aikatu ko ‘yan kasuwa kasuwanni, ba ana yin hanya ko gada don ƙawata gari ba ne, da rushe ma’aikata da ‘yan kasuwa saboda ƙawa ba. Zai ci gaba da magana, na kwaɓe shi na ce ni fa ban faye son jin tsegumi da raɗa ba.

TALATA

Talata, goma sha uku ga watan Shawwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Mayu, shekarar 2021.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce za a kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa a ƙasar nan.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da gwamnonin jihohin Ekiti, da Neja da Yobe.

Yau ake shiga rana ta biyu ta zaman makoki da ake yi na kwana uku, na rasuwar su Janar Ibrahim Atrahiru. Kuma yau sojoji za su koma bakin aiki, bayan hutun yini guda da aka ba su a kan rasuwar.

Gwamnatin Tarayya ta tarbe wasu matafiya su wajen casa’in daga ƙetare, saboda karya dokoki da sharuɗɗan hana yo tsarabar kwaronabairos.

Majalisar Wakilai ta soma binciken yadda aka yi da kuɗaɗe da kaddarori na ƙasar nan da aka ƙwato daga bakin wasu riƙaƙƙun gafiyoyi, daga shekarar 2002 zuwa 2020.

Zuwa yanzun an ƙona ofisoshin hukumar zaɓe ta ƙasa fiye da guda goma a jihohin Inyamurai.

Gwamnonin jihohin Yarbawa da sauran jiga-jigansu, sun ce ba su, ba maganar goyon bayan ɓallewa daga ƙasar nan, saboda sun gano kafa ƙasar Oduduwa ba alheri ba ce gare su.

Gwamna Ortom na jihar Binuwai, ya yi kira ga jama’ar jiharsa kowa ya kare kansa.

Mutum goma sha shida aka kashe a Jos ta Arewa.

Mutanen Gauraka ta jihar Neja, sun fusata sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna jiya, saboda an dame su da yawan kidinafin, da kisa da sauransu.

A Katsina -Ala ta jihar Binuwai, an kashe mutum a ƙalla biyar, aka ta da ƙauyuka masu yawan gaske.

LARABA

Laraba, goma sha huɗu ga watan Shawwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da ashirin da shida ga watan Mayu, shekarar 2021.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ɗage taron da Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta saba yi duk Laraba, saboda zaman makoki na yini uku, da a yau ake cika uku, na rasuwar su Janar Ibrahim Attahiru. Har ila yau Shugaban Ƙasa Buhari ya nemi ƙasashen duniya, su ba da goyon baya da haɗin kai, ga sojojin da ke mulkin Chadi, a watanni 18 da za su yi kafin miƙa mulki ga farar hula.

A Majalisar Dokoki ta Ƙasa, an yi wa kudirin dokar soke tsarin bautar ƙasa NYSC karatu na biyu.

Malaman kwalejojin foliteknik na ci gaba da yajin aiki.

‘Yan fansho na jihar Kaduna na nan suna ci gaba da ƙorafi, a kan matakan da gwamnatin jihar Kaduna ta ɓullo musu da shi, da suke zargin dabara ce ta daina biyansu haƙkinsu na fansho.

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta mayar da martani ga Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, cewa ya rage yawan surutu da ƙage, da sharri da ƙarya da yake mata.

Al’umar Birnin Gwari ta jihar Kaduna na ci gaba da ƙorafin ba su da mataimaki sai Allah. Kidinafas na ci gaba da kashe na kashewa da kidinafin na kidinafancewa, da kora musu dabbobi.

Ɗaliban jami’ar jihar Kaduna, na ci gaba da ƙorafin gwamna El-Rufai na ƙoƙarin hana ɗan talaka yin karatu ne, shi ya sa ya ƙara musu kuɗin makaranta tsugugu.

A jihar Bauci, mutum wajen 20 ya riga mu gidan gaskiya sakamakon ciwon kwalara, mutum 322 na can yana jinya.

A jihar Jigawa mutane wajen dubu biyar suka tsere daga muhallinsu sakamakon wata taƙaddama, tsakanin wani bafulatani makiyayi da wani manomi.

ALHAMIS

Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta soma zaman sauraron ra’ayoyin jama’a a faɗin ƙasar nan, a kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasa na shekarar 1999 gyara.

Wani kwale-kwale ya nitse da mutum 100 inda duk suka riga mu gidan gaskiya a jihar Kabbi.

Gwamnan jihar Kaduna El-Rufai kamar yadda ya bayyana zai rage ma’aikata da masu mukaman siyasa don tsimin ‘yan kuɗaɗen da ake samu a jihar, ya sallami masu riƙe da mukaman na siyasa jiya, wato masu taimaka masa, da sauransu, su goma sha tara.

An kammala zaman makoki na kwana uku, da ƙasa-ƙasa da aka yi da tutocin ƙasar nan, sakamakon rasuwar su Ibrahim Attahiru.

daliban jami’ar jihar Kaduna, na nan suna ci gaba da kai gwauro da kai mari, na ganin an rage musu kuɗin makaranta. A jihar Jigawa kuwa zabge kuɗin makaranta gwamnatin jihar ta yi.

Malaman kwalejojin foliteknik na ci gaba da yajin aiki, ɗalibansu na ci gaba da zama a gida karatun ya tsaya cik.

Af! A dinga hattara da yawancin matan da ke fesbuk musamman na wasu dandali na samari da ‘yan mata da sauransu. Don a zahiri ba mata ba ne, maza ne katti, ke sa sunan mace, su sa duk wani bayani a matsayinsu na mace, har da hoton budurwa tsirara, ko nono rabi a waje, alhali katon gardi ne. Ka ɗauka ka samu budurwa ko bazawara ko matar aure abokiyar hira, ashe kana hira da katon gardi ne. Haka nan mace za ki ɗauka kina hira da namiji ne, ashe kina hira da mace ‘yar uwarki ne. Ko ki ɗauka kina hira da da mace ‘yar uwarki, ashe kina hira da ƙaton gardi ne. Ki tura mata tsiraicinki, ashe kato kika tura wa. Ko ki tura wa namiji tsiraicinki, ashe mace kika tura wa. Ko ka tura mata tsiraicinka, ashe kato ɗan uwanka ka tura wa. Yawanci ya fi aukuwa ga mata da ke yawan tura wa mutane tsiraicinsu a soshiyal midiya.

Amma tambayar a nan, ita ce, me ya sa mata ke yawan tura wa maza ko mata da ke soshiyal midiya hotunan tsiraicinsu?

Exit mobile version