Aliyu Dahiru Aliyu dahiraliyualiyu@gmail.com +2349039128220 (Tes kawai)
Daga Ghenghiz Khan zuwa Adolf Hitler, daga Benito Mussolini zuwa Bin Laden, duniya ta samu kanta a hannun wadanda suke ganin kisa shi ne hanyar cigaba. Kungiyoyin zubar da jini domin cimma manufarsu da kuma ta’addanci domin tilastawa ta hanyar tsoratarwa a kan lallai sai a yi musu biyayya. Mun ga kungiyoyin ta’addanci da suke fakewa da kabilanci kamar Ku Klux Klan, da masu fakewa da son kasa kamar Nazi, da masu fakewa da addini kamar Lord Resistance Army a Kiristanci, ko ISIS a cikin Musulinci, ko kuma Zionist na Yahudawan Israel. A kullum za ka tashi ka kunna rediyo, ko ka karanta jaridu sai ka ga tashin hankali da yake-yake, walau a kasashen Larabawa ko Syria da Irak da ake yakin basasa, ko a kasar Yemen da take shan wahala a hannun tarin kasashen da suke yakarta bisa jagorancin kasar Saudiyya. Ko kuma ka ji cacar baki da barazanar yaki tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa. Donald Trump, azababben shugaban kasar da yake ganin zai iya taka kowa da karfin mulkin kasar Amurka yana fada wa Kim Jin Un, matashin shugaban kasa da baya jiran ko-ta-kwana, cewa yana shirin fara yaki da su. Wannan sai dai idan ba ka saurari wani labari kenan da ya ce kungiyar Boko Haram ta tashi bam a Maiduguri da kewayenta ba. Kana hawa shafukan sada zumunta za ka ga hotuna marasa kyawun gani (wasu na gaskiya wasu na bogi), a kan rikicin da ya barke tsakanin tsirarun Musulman Rohingya da kuma mafi yawan mabiya addinin Buddha a garin Rakhine na kasar Myanmar.
Duniya ta rikice. Kololuwar ilimin kimiyya ta tashi daga binciken lafiyar dan Adam daga zamanin Galen, Ibn Razi da Pasteur zuwa binciken tashin hankali da tsoratarwa tun bayan da Albert Einstein ya gano yadda za a iya samar da makamin nukiliya kuma an gwada ta a Hiroshima da Nagasaki. Kasashen da suke da karfi su ne wadanda suka taba gwada karfinsu a kan raunana kuma aka ga dole a ji tsoronsu. Kamar kasar Rasha (tarayyar Soviet) da ta lalata kasar Afghanistan, ko kuma yadda take ci gaba da tashin hankalin Ukraine. Kuma babu yadda za a yi a manta da irin su Benito Mussolini ko kuma Joseph Stalin. Uwa-uba kuwa ita ce Amurka.
Kusan duk shugaban kasar da ya hau kan mulki a kasar, kamar yadda Ali A. Mazrui ya bayyana a littafinsa mai suna, “Islam Between Globalisation And Counterterrorism”, bayan Franklin D. Roosebelt, sai da ya zabi kasar da zai kashe ‘yan cikinta domin ya gwada karfinsa. Harry Truman a Koriya, Dwight Eisenhower a Cuba, John F. Kennedy da Lyndon Johnson a Bietnam, Richard Nixon a Kambodiya, Jimmy Carter a Iran, Ronald Reagan a Lebanon, George Bush Sr a Panama, Bill Clinton a Yugoslavia, George W. Bush a Irak, Barrack Obama a Siriya da Libya. Karshen kololuwar karfi a yanzu ba shi ne ka koyi halin Mahatma Mohandis Gandhi ko Martin Luther King na zaman lafiya ba, sai dai ka koyi tashin hankali da zubar da jini da tsoratarwa a wurin irin su Adolf Hitler da Osama bn Laden. Wannan ta sa a zahiri muka ga tasowar Ku Klud Klan a Amurka don cin zalin wadanda ba Turawa ba, da kuma canjawar Aung San Suu Kyi daga mai son zaman lafiya a Myanmar zuwa mai shiru ana ta’addanci a kan miskinan Rohingya.
Addini ya zo wa dan-Adam domin ya koya masa rayuwa saboda ya tashi daga dabba zuwa cikakken mutum. Kamar yadda Alija Izzatbegobitch yake cewa, yayin da nazariyyar Charles Darwin (Darwinism) take kara alakanta mutum da dabba, shi addini yana kara bambanta shi da dabbar ne. Lokacin da falsafar Darwinism take nuna cewar duk rayuwarmu daidai take da ta dabbobi (struggle for survival), wanda ya da ce shi ne zai rayu (survival of the fittest), shi kuwa addini sanar da mu yake cewa a rayuwa ayyukan alheri da taimako su ne suke sanyawa a samu ingantacciyar rayuwa ko da bayan mutuwa ne. Dabbobi makaskanta ne idan aka kwatantasu da ‘yan-Adam. Wannan ta sa addinan Musulinci, Kiristanci da Yahudanci suka ce akwai rayuwa bayan mutuwa; su kuma addinan Hindu da Buddha suka yarda da “Karma” ko “Reincarnation” (tashi a wata halittar bayan mutuwa). Dukkan addinai, daga Krishna a addinin Hindu, Gotama Buddha a addinin Hindu, Annabi Musa a addini Yahudanci, Annabi Isah a Kiristanci da Annabi Muhammad a Musulinci suna koyar da kyawawan dabi’u, zaman lafiya da soyayya a tsakanin ‘yan-Adam.
Duk da sakon addinin Musulinci rahama ne da tausayi, amma sai da aka samu mutum ya fake da addinin wajen cin zarafin ‘yan’uwansa. Alkur’ani ya fara da kowace sura da sunan Allah Mai “Rahama” da “Jin Kai” ba mai “azaba” da “zubar da “jini” ba. Annabin addinin aka aiko shi rahama ga talikai kuma domin ya cika kyawawan dabiu. Amma a haka aka samu wadanda suka maida addinin filin kisa da zubar da jini. Suka mayar da Musulincin addinin da idan aka ce ta’addanci, to shi ake fara hasashe saboda ayyukansu. Addinin da takensa shi ne zaman lafiya ya koma alamar yaki. Yaki a Afghanistan, yaki a Siriya, yaki a Somaliya, kashe-kashe a Nijeriya, yaki a Iraki, tashin hankali a Yemen, rashin zaman lafiya a Bahrain da sauran abubuwa makamantan haka na damuwa ga mabiyansa.
Addinin Buddha da aka san shi da zaman lafiya da falsafarsa ta ce wa kada ka taba kowa, ya zama addinin kisan raunana a Rohingya. Litattafan addinin irin su “Sutta-Pitaka” da “Tripitaka” da za a iya samun bayanan Gotama Buddha a ciki, wanda an tattare su a cikin wasu mujalladan litattafai da ake kira “Sacred Books of the Buddhists”, sun nuna addinin na zaman lafiya ne da hakuri. Don haka ake mamakin yaya aka yi Adolf Hitler ya dauki tambarin addinin (swastika) da yake nuna zaman lafiya kuma ya yi amfani da shi wajen kisan kiyashin da ya ya yi wa yahudawa! Da sunan addinin aka samu shugabansa wato Ashin Wirathu a kasar Myanmar yake ta kisan kare dangi ga ‘yan tsirarun Musulmin Rohingya kuma yana tilasa musu barin kasar da aka haifi kakanninsu.
Haka dan-Adam ya maida abin da ya zo saita shi. A Kiristanci aka samu Lord Resistance Army a Uganda, a Yahudanci aka samu Zionist din Israel da suke kashe Falasdinawa da sunan kare kasarsu da suka ce Allah ne ya sa sai sun samu! A hakikar yakin da ke faruwa a duniya duka, burin dan-Adam ne na danne dan’uwansa sai ya fake da wasu abubuwan. Burin samun mulkin kasa ko danyan fetur din da yake karkashinta sai ya sanya mutum yake neman duk hanyar da zai bi don cimma burinsa.
A wannan karni na tsoron nukiliya da tashin hankalin ta’addanci, akwai bukatar mutum ya koma asalin koyarwar addininsa kuma ya gane bambancinsa da dabbobi ta hanyar gano mutuntakarsa. Mabiya addinin Buddha a Myanmar su gane cewa zaman lafiya shi ne tushen addininsu kuma Musulman Rohingya ‘yan’uwansu ne. Kasar Saudi Arebiya ta gane cewa mutanen Yemen ‘yan’uwanta ne a addini da al’ada. Amurka ta fahimci tsoratarwa na sanyawa a guji abu ne amma ba a so shi ba. ‘Yan kungiyoyin da suke kisa da sunan jihadi su kara ganewa cewa ba a kirkirar dan-Adam mai biyayya har zuci da tsoratarwa. Tsoro da fargaba suna sanyawa a kirkiri mutum mai gudun abu ne amma ba mai yi masa biyayya har ga Allah ba. Kungiyoyin addinai su fahimci junansu kuma su yi wa kawunansu uzurin fahimta. ‘Yan siyasa su hana mabiyansu zubar da jini saboda bukatunsu. Shugabannin addinai su koyar da zaman lafiya. Ilimi ya zama na neman cigaban dan-Adam a duniyarsa da lahirarsa. Ta haka ne kawai za mu iya attaruwa don samar da kasashe da al’ummomi masu soyayya da juna ba gaba da tada hankalin juna ba. Ta haka ne za mu daina kera nukiliya cikin ruwan sanyi ba tare da Majalisar Dinkin Duniya ko Amurka sun tsoratar da Iran ko Koriya ta Arewa ba. Ta hanyar soyayya za mu samu cigaba ba ta hanyar kashe juna da zubar da jini, ko rushe-rushe da sare-sare ba.